Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 132

Sponsored links

Ta dan kyalkyale da dariya da sakin hannun, yako tafi yaraf alamar duk wata mahada mai motsi a jikin Malikat Bushirat din ba aiki take ba a yanzu. A hankali ta koma kasa kusa da kafafunta ta zauna, tare da hannu ta dago afar ta fara matsa mata. Zabura Malikat Bushirat tai kamar wadda aka kodama mari ko ta suma aka zubawa ruwan sanyi drum guda, sai hakan kuma yay dai-dai da shigowar Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed. Yar dariya Iffah tai kamar bata san da shigowarsa ba ta cubi Malikat Bushirat din. “Ammie irin wannan zabura haka na sake tabo wajen da yay dayin kenan?”.

Idanun Malikat Bushirat ne suka sauka akan Tajwar Eshaan din dake takowa a nutse idonsa a kansu fuskarsa da dan sakewa. Sai dai kafin ta iya cewa komai da ga daurin goro ko makircin Iffah zatace mane oho Tajwar Eshaan din ya karaso yana dan gyaran murya. Dagowa Iffah tai ta kallesa har yanzu fuskarta da murmushi. Cikin yar shagwaba ta ce, “Yauwa ai garama da kazo, Ammie na nan zata kasheni da dariya, tace fa na matsa mata kafarta ya mata dan nauyi saboda zaman waje daya amma da nayi- nayi sai ta fara fadin ya isa a bari ta huta”.

Wani dan moso yayi iya lips yana dauke idanunsa da ga kallon da yakema Iffah’r na kasa-kasa ya maida kam Malikat Bushirat da mamakin duniya a makircin matsiyaciyar yarinyar ke neman dauke numfashinta. A hankali

cikin dan sanyin nan nasa da kamewa ya ce,

Ammie shiyyasa nace ki dinga motsa jiki tun last year, wannan zaman waje dayan da kuke ai ba gata bane, gashi nan shi ya kashema Jaddah kafafu anata fama”.

Da kyar ta iya dannewa ta dan saki murmushin karfin hali da yafi kuka ciwo ta ce.

“To ya za’ayi Saiful-malik, mizamuyi da wani motsa jiki a wannan shekarun namu?”.

Kafin ya bada amsa Iffah ta amshe da fadin, “Ai Ammie kike da motsa jiki kuwa, dan motsa jikin nada amfani sosai, kuma ya kamata ko dan cikin badda kama kuna fita kwamaga yanda talakawan kasa ke yan sabgoginsu, sannan koba komai ai hakama karin imani ne da lafiyar jikin harma da ta zuciya”.

Wani irin ji Malikat Bushirat tai kamar ta shako wuyan Iffah, dan ta fahimci maganace cikin ta jefa mata. Itakam ta farama tunanin anya yarinyar nan mutumce kuwa ba aljanaba a sufar mutane? Ya kamata a bincika mata kam dan al’amarin ya fara girman tunaninta. Amma a zahiri sai ta cije tai dan yake. Tajwar Eshaan da ke dan jinjina kai batare da ya fahimci komai ba shi kam a zancen idanunsa dake akan Iffah ya lumshe kadam da budewa lokaci guda. “Ammie shawaran nan nata mai kyau ne, ni kaina naso na miki tayin hakan tuni sabgogina basu barni na zauna ba. Amma Alhamdullah tunda gata yanzu bayan ni da Aunt kin sake samun diya daga ALLAH nasan zata kula mana da ke kamar mu din. Sannan kusantar al’ummar mu yanda ya kamata a zahirance zai kara saka mana son su da kaunar su a zukata kamar yanda ta fada. Zakiji dadin hakan, ki samu lokaci ki fara gwadawa koda tare da itane ni mai yarje muku ne”.

 

 

 

“Uhm kai dai. To ALLAH ya shige mana gaba kawai”.

 

 

 

Amin suka fada a tare shi da Iffah, sai dai a ransa yasan bata amshi lamarin ba. Dan haka ya basar da zance ya dakko mata na tafiyarsu.Cikin mamaki take kallonsa sai dai batace komai ba. A ranta kam wani irin zafi takeji mai kuna. Har itace sai yau Saiful-malik ke sanarma zaije Umrah, Umrah din ma na azumi baki daya. Kai anya bata fara rasa danta ba kuwa? Bata fara rasa danta daga jikinta ba kuwa? Jifa maganganun da yarinyar nan ta fada mata a yanzu, irin wanda ko mahaifiyarta sanda tana a raye bata jin ta taba fada mata su, amma shi ya hau ya zauna Kamar ma bai fahimci manufarsu ba. Tabbas akwai matsala, matsala babba da uwa sam bata lissafo ba a lissafinta. Yanda fa rawar take neman canjawa dole ne shima kidan ya canja inba hakaba zata kona Masarautar nan ne baki daya why, dan bazata dauki faduwa a saman nasararta ba. Never for ever……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button