Hausa Novels and Stories

Kaunar Uwa Hausa Novel Complete

Sponsored links

Ka yi wa darajar Allah kada ka raba k’aunar dake tsakanin d’a da uwa.

 

ka tuna tausayi da shak’uwa da Allah ya sanya tsakanin mahaifiya da d’anta,

 

kada ka raba tsakaninmu kayi min alfarma kabarni na rayu da d’ana ina sonshi ahaka kada ka raba k’aunar uwa da ɗanta na yarda da dukkan hukuncin da za ka yanken amma kada haka ya sha fi lafiyar jaririn da ko cibi ba’a yanke mishiba.

Kuka ne yaci ƙarfina sakamakon ganin kwalin da mahaifina ya d’auka yana shirin sanya jaririn da ko wanka bai samu anyi mishi ba. ji nayi dukkan wani tsoro da fargaba ta fita azuciyata tsantsar k’auna da tausayin gudan jinina da ƙila shi kaɗai Allah ya mallaka min amma saboda rashin tawakkali ana shirin salwantar da ranshi saboda allah ya hukunta zuwanshi duniya to menene laifinshi da har mahaifina ya kasa karɓarshi menene laifinshi don ya zo A matsayin ɗan da aka samu cikinshi ta hanyar fyad’e meyasa duniya ta lalace mutanan kirki sun yi ƙaranci acikinta. na rasa tudun dafawa alokacin da mummunar ƙaddara ta faɗawa rayuwata alokacin dab anyi zato ba.

Amma mahaifina ya shafawa idonshi toka wayyo rayuwa ni sumayya ina zan saka raina naji daɗi jin fitar mahaifina daga ɗakin da nake ne ya farkar dani daga tunanin ƙaddarar da ta faɗa min,aguje na bishi tare da fisge kwalin da ya saka jaririn aciki na yi, ban taɓa tunanin tsanar da mahaifina yake min ta kai haka ba shin akaina aka fara haihuwar ɗa ba tare da aure ba.

Mene ribar kashe rai me abbana yake shirin aikatawa ina ji a yanzu ko duniya za ta tattaru akaina bazan iya bada gudan jinina asalwantar da ranshi ba.

 

Wallahi ina sonshi ahaka na shirya fuskantar dukkan ƙalubale na rayuwa na shirya dukkan abin da zan gani ko na ji dangane da ɗana Abbah!!! nakira shi cikin amon murya abba wallahi muddin ba za ka zauna da ni da ɗana ba a haka ba na zaɓi barin gidan ka”.

Na zaɓi na shiga duniya na zaɓi dukkan wani ƙunci da zan shiga ayanzu ko agaba amma kasani bazan iya bari akashe Muhammad Anwar ba.

 

Ina tantama akan so da ƙaunar da ka nuna min abaya Allah sarki Ammie Allah ya jiƙanki allah ya sa ka miki yabi miki haƙƙinki duk wanda ya yi sanadiyyar rasa ranki Allah kana ganin zalincin da aka yi wa bayinka Allah ka sa ka min kukane yaci ƙarfina tabbas anyi mana zalincin da bazamu manta ba.

Juyawa Abba ya yi idonshi yana zubar da hawaye nima rungume Anwar na yi zuwa ɗakina tare da ɗaukar sabuwar reza na yanke mishi cibiya ruwa na ɗaura akan wuta sai da ya tafasa sannan na ɗiba wanka na yiwa anwar duk da ban iya sosai ba.

Amma ina ganin yarda Ammie take yiwa ƙanina Muhammada Anwar ina gama yi mishi wanka na ɗebo kayan murgayi Anwar wanda kafin rasuwar Ammie ta danƙa min da hannunta.

Allah sarki uwa Allah ne kaɗai yasan ƙaunar da ya sanya tsakanin uwa da yaranta na yi kewarki Ammie ke kaɗai ce kika yarda da ƙaddarar da ta faɗawa tilon ƴarki Ammie allah ya jiƙanki ammie ganin na shiryashi kamar yarda naga ammie na yi sai na kwantar da shi na shiga banɗaki wanka nayi da ruwa me zafi haka na daure ina kuka ina komai na gyara kaina na fito na gyara wajan da ya ɓaci zama nayi ina tunanin rayuwa yunwar da ke ƙwaƙular cikina ce tasa na ɗauki kayan karin da ban iya ci ba ina turawa ba dan daɗi ba banjima ba wani masifaffen ciwon ciki ya murɗeni kuka nake ina juyi tare da kiran sunan Allah don na san babu me fitar da ni ahalin da nake ciki jin Anwar na kuka ne yasa na ɗan janyoshi kusa da ni tare da sanya mishi nono abaki jin zafi ya ziyarce nonona lokacin da ya kama yana zuƙa lokaci ɗaya naji tausayi da ƙaunar dukkan wata uwa tabbas iyaye sai dai addu’ar allah ya biyasu ahankali nake shafa kanshi ina ƙare mishi kallo farine tas sumarshi irinta fulanin usul gata baƙa ƙirin da ita yaron yana da hanci da manyan ido sam ba ya kama dani sai dai kama ta jini.

Abban Rufaida me nake gani a gidanka ɗan shege fa ɗan zina wallahi bazan zauna da ɗan shege ba sai dai kasan abin da za ka yi ko dai aje a yarda shegen yaron ko kuma uwar da ɗan zina subar gidan ko kuma ni inbar maka gidan sai ka zaɓa tsakanin ni da su jikin Abba na rawa ya miƙa hannu zai ɗauke Anwar saurin dakatar da shi na yi na miƙe tare da janyo akwatina na haɗa dukkan abin da nake buƙata na goya Anwar na juya na kama hannun Abbana da yake zubar da hawaye nima hawayen nake na ce”Abba kayi haƙuri na san duk abin da kake ba yin kanka bane Abbana me ƙaunata ba zai taɓa wulaƙanta ni ba Abba a duk inda nake a faɗin duniya addu’arka nake buƙata bazan taɓa mantawa da Abbana ba zan kasance me roƙon Allah ya fitar da kai daga sarƙaƙiyar duhun da ka shiga Allah ya fitar da kai ke kuma ki jira ranar da asirinki zai tonu ki jira ranar sakamako tun a duniya ki sani wannan yaron insha Allahu shi ne mabuɗin tonon asirinki jan trolly ɗina na yi tare da sa mukulli na kulle ɗakin mahaifiyata.

Ban san ina zan shiga ba bansan ina za ni ba tafiya nake ba tare da nasan ina na nufa ba ga duhun magriba ya kawo kai yanke shawarar barin garin gombe na yi ban san ina dangin Ammie suke ba bare na nufe su dangin Abbana kuwa ko giyar wake nasha bazan doshi inda suke ba ko da na je bazan sa mu masauki ba ƙarshe cin mutunci da tozarci ne zai biyu baya atsakaninmu tabbas maraici mugun ciwo ne nayi imani da Ammie tana duniya bazan tozarta ba.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button