Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 5

Sponsored links

..A wannan gaɓar haukane kawai ya rage wannan ahali suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raɗaɗi da zafin da yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun saka kowa ke ɗaukar tama zare kawai. Daga ƙarshe maganin barci aka ɗura mata. Bata tashi farkawa ba sai a ƙauyen da kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a ƙauyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun ɗaura ɗammarar ɗaukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman. Ba ƙaramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo hayyacinta. Sai dai ta daina fira’a da kowa, an daina ganin dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke’a ranta sai buri da ƙudirin ɗaukar fansa. Tama kanta alƙawarin ita da hannunta zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*. Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da azzalumin sarki mai mulki irin na fir’auna a ƙasarta a cikin al’ummarta….

*_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah😱? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa….? To mudaije zuwa wai mahaukaci ya sai kura😬🤧🚴🏼)_*

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” bakinta ke ambata cikin firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata luguden taɓaren daka a tsakkiyarsa, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin mutuwar ƴan uwanta da fara canjawar salon mafarkainta saɓanin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taɓa mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.

“Nina Arfa! Nina Fariha!”.

Ta ambata a zahiri zuciyata na ƙara ƙarfin gudu, yayinda hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani kuka masu ƙarfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin ƙofar ɗakin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiɗar barcin nata wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta ɗauka ta yanama jikinta, ta ƙarasa ga ƙofar ta buɗe…

“Kina lafiya kuwa ɗiyar nan?”.

 

Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi amsa.

 

“Ina lafiya Kaka”.

 

Jin shiru bai sake cewa komai ba ta ɗago ta dubesa a karon farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake maida idonta tai ƙasa, hawayen da take faman riƙewa suka ɓalle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta fara ta sata zubewa a gabansa kuka na ƙwace mata. Kusan minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaɗarta ya sata haɗiye kukan, ya ɗagota tsaye yana ɗan murmushi dake sake bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya ƙare, koba komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya ishemu farin ciki”.

Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani ɗan lokaci. “Kije kiyi addu’a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.

A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to dan ALLAH”.

 

Da sauri ya girgizamata kansa. “A’a bazai yuwu ba Iffah, iyayenki sun kawoki nan ne domin kuɓutar dake, taya kike tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina ƙanƙanin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saƙa kayan doki a garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na haifi ƙanin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa ɗan uwan mahaifiyarku a yaƙin kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da Fariha. Ke ɗaya da kika rage mana da yayanki wajen mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai yuwuba jeki kwanta…”

Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga ƙangin fargaba, da gaske tanajin matuƙar tsoro bayan rasa Fariha da Arfa da sukai watanni ƙalilan da suka shuɗe itama su rasata, tanaji zuciyar ahalinta bazata iya ɗauka ba idan itama suka rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu raɗaɗi da saka ƙuna a ƙirji……

Sautin ƙwala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira Iyyani ya sakata fitowa daga banɗaki data zagaya domin yin fitsari. Turus ta tsaya tare da haɗiye maganar da zatayi tana mai kallon ɗan-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a ƙarƙashin bishiyar ɗoruwa da take a tsakar gidan. Murmushin da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta ƙarasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai ɗan rungumesa ta gefe da faɗin, “Ina kewarku Akhi”.

Murmushinsa ya sake faɗaɗa yana mai kallon fuskarta. Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel. Gidan duk ya sake zama mana babu daɗi”.

Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci tana kaɗa kanta kawai.

“Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baƙo a garinku”.

Baki ta ɗan tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miƙe tana bata amsa cike da shagwaɓa. “Iyyani laifinkine fa, ban taɓa ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole Yayana ya miki kishiya”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button