Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 64

Sponsored links

Kamar yanda su Malikat Haseena suka faɗa a yau aka tashi da gyaran sashen Iffah, sai dai abinda ya Bama kowa mamaki ba inda aka fara kaita bane. Ɗaya daga cikin sabbin sashen da babu wanda ya taɓa rayuwa a cikinsu ne a masarautar.

Hasalima an jima ana gutsiri tsomar dalilin gininsu da Tajwar Eshaan yasa ayi batare da ansan dalilinsa ba. Ba kayan ƙawata gida kawai aka zubama sashen ba, harda tarin sitturu da kayan ado na sakawar Iffah.

musamman ne suka duƙufa kanta a yinin wannan rana. Da dare ta samu hutawa. Washe gari aka cigaba da mata gyaran da ita kanta sai da zuciyarta ta fara shiga wasi-wasi. Koda yake dama a ciki take. Dan gaba ɗaya kwanakin nan aikinta kawai shine nazari da fasalta abubuwa masu yawa a rai da takasa gane bakin zarensu sam. Sai dai shawarar malam Fawzan ta waccan ranar ta ƙara mata ƙwarin gwiwa da maidota a hayyacinta da matsayin shigowarta daular ruman…..

 

 

 

Tsahon kwanaki uku ta gyaru ta ƙara ƙyau tamkar ba’ita tayi fama da jiyya na a kwanakin baya. Ƙamshin dake fita a jikinta ma kawai ya isa ai kiransa na musamman. Ita a karan kanta har gizago canjawar tata ke mata. Jikinta ya murje ta ƙara girma da cika ido tamkar ba autar Ummu da Babiy ba. Ga wani jin kai da takejin ta ƙara masu neman kere shekarunta. Babu shakka kuma hakan nada nasaba da girman da ake bata.

 

 

 

Masarauta da jama’ar cikinta zance ya yaɗu yau za’a maida Zawjata-almilk sabon sashenta tunda ta samu sauƙi. Shaidar haka kuma nada nasaba da walimar da Malikat Haseena suka shirya, acewarsu ta aure ce da ba’aiba sanadin abinda ya faru za’ayi yanzu. Shirya wannan walima ya kawo ƙananun magana matuƙa, dan kuɗi aka kashe tamkar za’a sake wani sabon auren. Abin mamaki sauran mata biyu kafin Iffah ga Tajwar Eshaan sai al’amarin ya sosa musu zuciya duk da har yanzu zaune suke batare da ko Tajwar ɗin sun san kalarsa ba.

 

 

Sam Iffah bata san da wani taron walima ba, sai da aka kammala mata shiri cikin wasu ƙawatattun kaya masu tsananin ɗaukar ido da tabbatar da ita amarya ta gaskiya mai amsa sunan Zawjata-almilk kanta ya fara ɗaurewa. A ganinta in har shigace ta iya rakata sashenta baici ace ta ƙawatu har haka ba kodan kasancewar dare ne ma. Kai mutanen nan fa sun fara caja mata ƙwaƙwalwa, ta faraji a ƙasan ranta akwai manufa. Amma dai koma minene zata jure har zuwa lokacin samun ƴancin kanta na komawa sashen nata dan ta shiryawa kowa talalarsa. A kwanakin baya ta kwantar da kai ne ga kowa domin fahimtar manufar wasu koda kalilanne a cikinsu. Alhamdullah kuma ta dace, dan koba komai ta gama samun yardar Daneen Ammarah da masu gayya da aiki Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Duk da dai tasan kada mage ba yankata bane. Amma koba komai raina allura yakan sa ta zama garma ga wanda yay sakaci ai.

 

Taji ba daɗi da barin ɗakin data rayu tsahon kwanaki cike da kewa. Koba komai bazata manta da rayuwar kusan sati uku da tayi a cikinsa ba. Ta koyi ilimi da yawa, harma da darasi data ɓoye matsayin sirrinta. Da wannan tunanin a ranta har aka iso babban ɗakin taro na cikin masarautar, wanda ya ƙunshi duk wani babba mai faɗa aji. Al’ajab ya kama Iffah, amma ta dake zuciyarta na sake tauri na nan dalilin ɓoye mata wannan zaman da akai. Amma a zahiri rashin ƙarfin cewa yasata yin luff kamar yanda ta kasance a kwanakin da suka gabata na samun lafiyarta. Daneen Ammarah data kasance mata ƴar jagora kasancewar fuskarta a sakaye take ta kaita har mazaunin da aka tanada dan ita a cikin ƙaton falon bisa tattausar dardumar da aka shirya walimar. Kamar yanda al’adar take, abinci aka fara ci yayinda Iffah ta gagara kai ko ruwan madara bakinta. Yanda tayi ɗin ya sake burge su Malikat Bushirat, suna ji a ransu sun dace da irin surukar da suke fata. Bayan anci ansha kowa ya nutsu. An fara buɗe taron da addu’a, tare da saƙon maraba ga sabuwar Zawjata-almilk, harma da fatan kasancewar ta abinda kowa ke fata. Kowa dai ya amsa da amin a zahiri, a baɗini kam sanin sirrin wasu sai ALLAH.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button