Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 13

Sponsored links

A lokacin fatima zainab ta kara kulla aminta da codeine shiyasa duk abinda momma take baya damunta, kudin da daddy yasa ake bata kullum akan siyan codeine yake karewa kamar wacce aka yiwa baki, data siya abinci taci ta gwammace ta siya codeine tayita sha, tana sane da cewa smokers and drinkers are liable to die young amma she doesn’t care anymore dan tayi nisan da bata jin kira, abun nata har ya wuce addiction ya zama disorder…..

 

A gurin abdul kanin khaleel kadai take samun sauki saidai shi ba mazauni bane dan a boarding school yake shima, sosai yake shiga damuwa akan yanda take inactive koda yaushe, wani zubin yana mata magana batasan me yake cewa ba, haka zatayi ta bashi unrelated answers, tun yana karyata zuciyarsa harya fara zargin shayeshaye take saidai binciken duniya ya kasa gane abinda takesha cuz she knows how to play her game, gashi be isa ya kulata a gaban momma ba dan yanzu zata hau masa fada ta inda take shiga batanan take fita ba, momma ma nasane da shayeshaye takeyi tinda ko a ranar datazo gidan a bige tazo saidai ko a kasan slippers dinta, inma duniyar duka zata shanye bata damu ba……

 

Mama da aka ware gefe tana sane da muguntar da momma take ganawa yarinyar, sannan kuma ta mata daidai bakincikin ta daya yanda taga momma na wani faffadi akan lamarin yarinyar tana nunawa alhaji tana kula da ita, shikuma sai yayita jin dadi yana mata kyauta yana ji da ita….

Takaici ne ya isheta ta fara shirya yanda zata tonawa momma asiri har tasamu yarinyar ta dawo hannunta itama ta dandana mata kalan nata azabar batareda daddy da momma din sunsani ba…..

 

Yanke shawarar kiran alhaji tayi lokacin daya kusa dawowa kasar, da farko kin yarda da abinda ta fada yayi dukda tana kuka tana gayamasa yanda irin muguntar da ake yiwa yarinyar yake mata ciwo, harda cewa tasan ita tanada zafin kishi amma hakan bazesa tayiwa mutum mugunta haka ba, sannan tace mishi tasan baze yardaba tinda bajin maganarta yake ba amma yayi bincike akan lamarin….

 

Sosai jikinsa yayi sanyi dan yasan abinda zesa hafsah kuka ba karami bane, sai ya mata alkawarin zeyi bincike….

 

Koda ya dawo be nunawa momma komai ba dan tanata nan nan da yarinyar kamar yanda yasan tanayi da, sai ya fara dan bincike har Allah yasa ya kamata red handed, lokacin sun dawo daga masallaci shida abdul a ka’ida baya shiga part dinsu a irin wannan lokacin, ranar sai yabi abdul suka shiga, abun al’ajabi suka samu momma nata jibgar fatima zainab dake bacci a kitchen, dukan duniya kuma taki tashi saboda yanda tasha tayi makil bayan sallar asuba, tana dukanta tana zaginta harda fadin batace mata tadinga barin kitchen da sassafe ba, sai tayita bacci saboda alhaji yazo yaganta ya gane a kitchen take kwana……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button