Hausa Novels and Stories

Idon Naira 40

Sponsored links

Babban tashin hankalin farko data fara fuskanta akan tafiyar tasu Abuja shine Haj Maryamah data Kira umma akan zata Aika Mata da MARYAMAH Qarama acan Cameroon bazasu da ita Abujan ba.

Bugawar da zuciyar zainab tayi yasata dafa bango tana Dan bude idanuwanta dake Mata dishi dishi.

A gabanta umma da aka Kira Kai tsaye itama tace bazata iya riqon MARYAMAH dinba sbd tsufa yazo Mata Kuma dasuka riqe uwarta tun tana jinjira me ta saka musu dashi Banda butulci Dan haka ita ma wanna halin uwarta zatayi itakam bazata iyaba.

Haj Maryamah ma Kai tsaye ta nuna zainab bazataje da MARYAMAH dinba idan har umma bazata karbetaba to gwara zainab din ta nema dangin mahaifinta ta miqa musu ita.

Tunda zainab take Bata taba Jin daci da radadin zuciyaba akansu sai wannan karon,

yarta ake ture turen inda zaa Kai kowa nacewa baya son saikace wani mugun abun,

Me tayi musu da tsanar dasuke Mata zata shafa ‘yarta hakan wadda batasan komaiba.

Tafiyar na matsowa umma ta Dage akan bazata karbi maryamah dinba,

Kukan da zainab tayi Saida takai idanuwanta ma basa gani sosai,

Tayaya zata iya bada qanqanuwar marainiyar ‘yarta har Cameroon itama taje ta taso Acikin qangi da wahala.

Kukan Rashi iyaye Dana Mijinta tayi tareda na Aqeel Wanda tuni ta cire Rai daga Kansa itada yarta.

Hada dukkanin tsumman kayanta tayi guri daya Dan tasan rigimarda zaayi idan tafada raayinta na bazata taba rabuwa da ‘yartaba,

Idan har Haj Maryamah zataje Abuja da ita to zataje da yarta,

Tasan hakan zai kawo rigima tunda ansaba takuma san ran kowa zai baci Amma bazata iya barin arabata da yartaba.

Rigimar kuwa akayi sosai tareda bacin rayika alokacinda ta sanarda Haj Maryamah bazata tafi bada MARYAMAH dintaba.

Umma ranta kusan yafi na Haj Maryamah din baci sbd mamaki da takaicin zainab take tafara jero Mata gorin irin rokon da Aqeel yayi musu akan su amsheta ta zauna gurinsa shine yanzu an zabar Mata rayuwar sauki da Jin Dadi zatace bazata rabu da yartaba,

Ashe ‘da yanada dadi shine ita ta raba haj Maryamah da nata Dan kullum cikin fada yake da mahaifiyarsa akanta.

Haj Maryamah kuwa tsabar takaicin da baqin ciki Kai tsaye ta Bata zabin Idan bazataba Saida yarta to tayi zamanta Amma tasan Wana gidan an saidashi gabaki daya har masu gadi tafiyarsu zasuyi.

Irin cin zarafi da tozarcinda umma tayi Mata dakuma maganganun Haj Maryamah din yasa ta sake hada kayanta guri daya.

Haj Maryamah ganin Bata bar gidanba yasa tayi tunanin ta aminta da tafiyar MARYAMAH din Cameroon Dan haka tasa babah ta shirya Dan itace zatakai MARYAMAH din har Cameroon.

Sai ranar tafiyar tun kafin asuba babah ta shirya sbd sammako zasuyi a tafiyar.

Ayau zainab ta fito tayi magana Kai tsaye cewan bazata bada ‘yartaba,

Tsananin fushin da haj Maryamah da umma suka dauka yasa akai hayaniya mai girman gaske da har tasa Haj Maryamah sakarwa zainab Marin daya bawa kowa tsoro.

Kasa hawaye zainab tayi sbd zuciyarta datakai qololuwar ‘daci da qunci,

Ayau ta tabbatarda har abada bazasu taba kaunartaba sbd qiyayyar dasuke Mata a jininsu take…

Maganganun Haj Maryamah suka rufe ganinta saidai batajin zata iya barin ko gari ya waye tunda umma tabata umarnin barin gidan daga ita har yarta dasuke neman aibatawa sbd rufewar zuciya.

Daurin kayanta ta dauka ta fito daga gidan tana Jin zuciyarta na tiririn zafi da azaba.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button