Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 23

Sponsored links

Fitowa sukayi tana jin yanda wani bacci yake fuzgartarta ta daure, har sunkusa gate yace mata yayi mantuwa ta rakashi part din mami su dauko, batace komai ba suka juya suka tafi…..

Kamar gaske yace ta zauna bari ya dauko abu, gurin dining ya tafi ya gama zagayen shi ya dawo, kallonta yayi yaga ta fara gyangyadi daga zaune……

Yana tsaye a gurin harta shige dakin mami, ajiyar zuciya ya sauke me karfi yana fadin ‘nasha da kyar’…. Sannan ya kwanta a parlourn kamar yanda yayi last time data kwana a gidan…..

“Yanzu abinda yarannan yayi ya kyauta kenan? Ya mayar dani kamar wani sa’ansa? Ince karya kara barin garinman sai yayi tafiyarsa? I’ll make sure ya gane shayi ruwa ne this time around”….

“Allah ya wuci zuciyarka alhajina, nima Deen ya bani mamaki, tiryan tiryan fa mukayi magana dashi akan yarinyarnan har cemin yayi zeje ya ganta sai gashi yayi tafiyarsa, amma gsky Deen ba haka yake ba kila akwai me zugasa”….

“Waye ze zigasa banda uwarsa? I’m very sure abuja ya sake komawa tinda yanzu maganarta kawai yakeji”…..

“Gsky be kyauta ba, amma ga shawara alhaji”….

Umm da mami suka hada baki wajan fada suna dagawa fatima zainab dake gaban mota hannu….

 

Jan motar Deen yayi har lokacin fuskarta a hade yake, haushin shi takeji dan tinda safe yasata a gaba wai sai tayi karatu batasan ya akayi yayi finding out tanada exam 11 na safe ba, haka ya isheta da tambayoyi akan course din tayi banza dashi, karshe ya fara mata masifa wai she’s not serious sai taje ta kwaso carry over, ce masa tayi ko tazama serious saita kwaso course din daya yaga mata paper besan tanajin haushin abun ba haryanzu, dariya abun ya bashi sosai yace mata indai zatana jin maganarsa toh batada case da course din ko A takeso ze bata, amma kememe taki yarda suyi karatun, sai hakura yayi ya kyaleta, haka da sukazo tafiya ya dinga bata wahala dan yafi so hudu yana cewa taje a sake mata kaya, a na biyar dinne mami ta biyota tace be isa ba, tuburewa yayi wai saidai tasa hijabi har kasa, haka mami tace tayi hakuri tasa su tafi kartayi latti dan tasan Deen da kafiya, hakan be ishe shi ba wai sai tasa nikab, wai ai tasaba sawa, Umm ce ta raba wannan fadan tace toh ta saka nose mask su tafi kar lokaci ya kure…….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button