Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 3

Sponsored links

Jin maganan Manager yasa Sumayya jin faɗuwar gaba , tana mai tambayar kanta da cewa ” To ina ita ɗayar sakatariyar? Amsa ta bai ma kanta da faɗin ” ina ruwanki…kedai baki ganki a wurin kuɗi ba,to Amma ai nan wurin magatakadda kenan”. Shikenan zaki iya tafiya aiki na jirar ki…ta tsinkayi Muryar Manager Mubarak Al-mustapha..Ɗan murmushin saman laɓɓa tayi ba tare da ta nuna wani damuwa ba tace ” Thank you”. Tana raɓashi haɗi da wucewa baki sake yabita da kallo har ta shige ,yana mamakin ganin rashin damuwa a tare da ita ,ance mata sakatariya bata damu ba , Bama tayi tambaya ita ina Mrs Hauwa ɓaidu ba…tabbas da jarfa zaman ta a wajen nan!

Kaman yanda manager yayi mata bayani position ɗin sectary ta zauna ,inda ta cidda komai tsaf cleaners ɗin Company n sun gyara komai na wurin ,sai dai takardun da ta gani ne cike saman table yasa ta zama tana kai hannun ta a hankali tana fara duban su…Kallon wurin tayi tana hango wani fridge ɗan ƙarami , murmushi tayi tana cewa ” banza ya samu”. Mrs Sumayya right?

A hankali ta ɗago da kanta tana bin baƙuwar fuskar da batasani ba da kallo ,kamin ta jinjina mata kai tana cewa ” Yeah”. Kece sabuwar sakatariyar sir Khamal?. Ta kuma tambayar Sumayya a wulaƙance “. Eh nice ya akayi?’.

Wani irin dariya Najwa tayi ma Sumayya na ƙasƙantarwa kamin tace” ashe kuma ana kan hanya kenan?”. Ɗauke kai Sumayya tayi a hankali kamin tace ” Wani abu ki buƙata?. Ina son ganin shi ne. Wait for him there”.

Sumayya ta bata amsa ba tare da ta kalleta ba idon ta na akan takardun gaban ta da take so ta fahimta inda aikin wurin ya nufa.

Shiru Najwa tayi tana gyara tsayuwar ta takaici ya ishe ta ,don ta lura itama Sumayya ba kanwan lasa bace ,ƴar rainin hankali ce…wannan yasa najwa ja baya tana zama can gyefe kusa da inda Sumayya ta nuna mata tana zama….

Sai da Sumayya ta ɗauki kusan minti goma a haka , kana ta miƙe tana nufa office din Sir Khamal don ta sanar masa da Najwa… nocking tayi wanda bata ji maganan sa ba wannan yasa ta kai tsaye murɗan handle ɗin tana shigewa abun ta…Good morning ther….. wait for me out side”. Yayi maganan yana katseta tare da ɗaga mata hannu …wani abu ne ya bugi ƙirjin ta da ƙarfi, tsoro ne kome? Yanda taji Muryar sa ba wasa yasa Sumayya natsuwa duk da wani abu dayazo wuyan ta ya tsaya , don abun da yayi mata wannan wulaƙanci sunan shi ba wani abu ba…yarfa ta yayi sosai…a hankali ta juya tana shirin ficewa daga office ɗin , kaman ance ta juyo ta kalleshi taga yayi mata ƙurrrrr yana kallon ta ta cikin tabarau ɗin dake idon shi…

Kallon ƙasa ƙasa tayi masa taana hararar sa haɗi da saurin ficewa daga office ɗin…Sauke eye glss ɗin yayi yana kai hannun shi haɗi da shafa sajen fuskar shi , kaman ya ɓaci da Daddy ,sai dai yarinyar bata da kunya sam , dagani bata samu tarbiyya ba Ni take harara ,wannan shine karon farko da wata mace ta kalleni ta hararen WHO is she? Wacece ita ɗin? Shiru yayi kamin a zuciyar shi yace ” meye shafeka da rayuwar ta?.

Zama Sumayya tayi haushi ya isheta ita abu ɗaya ta tsana a rayuwar ta shine wulaƙanci…gashi ta fahimci Sir Khamal yayi sabo dashi. Wannan yasata zaunar da Najwa tana cewa ta jira shi…ana haka wani babban mutum yazo shima zaunar dashi tayi tana cewa su jira shi … Ba tare da ta sanar mawa Khamal ba awa da awanni tayi ta tara masa manyan mutane masu muhimmanci anan wurin ,a cewan ta baxata koma ya wulaƙanta ta ba , wuraren 12pm ne ta miƙe tana nufar ƙasa inda sauran ma’aikata suke , don yau ko gaisawa basu yi ba… Da kuma yunwan da ta fara ji yasata nufar inda suke . Tun da take sakkowa taga fuskokin ma’aikatan ya sauya sai washe mata baki akeyi wanda jiya basuyi mata.

Ɗan tsam Sumayya tayi kamin a zuciya tace ” Kai wannan fara’a badon Allah bane da dai dalili..wldone taji kowa nace mata ,wanda jin haka yasa Sumayya kanta ƙara girma cikin izzar ta da mulki a gadarance take faɗin ” Thanks”.

Sannu Hjy”. Taji Muryar Wata mata da ashekaru zata yi talatin da biyar tana katseta , kallon ta summy tayi don ta ganta da shigar ma’aikata na wurin…ɗan murmusawa Sumayya tayi tana nufan inda take….gaisawa sukayi a mutunce duk da Sumayya na mmkin wannan mutunci , a zuciyar ta sai cewa take ” Da gadar zare A wannan tafiyar…Tambayar madam Bukhari Asma’u Sumayya tayi ina zata samu abun sha?”.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button