Hausa Novels and Stories

Idon Naira 34

Sponsored links

Kuma sunan yar uwarta ne Jininta da bata da kowa sai ita da yayanta da suka zama biyu yanzu wato AQEEL da MARYAMAH.

Hannu nurse ta miqa masa Akan ya bada babyn a maida ya maida kallonsa kan babyn yana kallon fuskarta cikeda kulawa da kauna

Hakanan yakejin kamar idan ya bada MARYAMAH din ya Rabu da ita kenan.

Miqata yayi bayan ya sake rufeta koina kamar yanda aka kawo musu ita.

Dakin da maminsa take suka koma ko zama baiyiba ya fito yaje ya biya kudin komai da komai harna sallama dan haka babu abinda zasu Nema har ayi sallamarsu insha Allah.

Daga can gida yakoma sbd kiranda ummansa ke masa.

Yana isa ta rufesa da fada amma dai bayan hakura baice mata komaiba saima maganar data daga hankalinta dan saura kiris ta some.

Bata buqatan yace mata yar Zainab yasawa sunanta dan haka Ta zuba masa idanuwanta tana jiran amsar dazai bata dan bacin ranta qaruwa yakeyi da komaima ayanzu idan har Aqeel yafasa tafiya Akan zainab wlh wannan karon ba qaramin fushi da bacin ranta zaa ganiba.

“Umma yar maminace da wannan sunan

Bakuma lafiyayya bace tayaya zan barsu natafi waye zai kula dasu?

Maganar tafiyata kuyi hakuri umma abarta sbd bazan iyaba…..

Kofa ta nuna masa da hannu Tana kokarin danne zuciyarta daga furta kalamanda basu daceba ga ‘danta.

Yana fitowa bangarensa ya nufa ko zama baiyiba kiran Haj kaka yashigo wayarsa dan haka ya juya ya fice zuwa gidan haj kakan,

Yana isa haj maryamah na isowa nan take sabon rikici ya tashi qannan babansa ma su uku maza duka sun saka bakinsu a maganar amma Aqeel din ya tsaya cak akan bazai bar zainab da MARYAMAH su tagayyara.

Duk yanda ake tunanin kusanci,shaquwa da girman kaunar dayakewa Zainab wannan karon sun tabbatarda abin ya wuce tinaninsu dan haka hankali ya tashi cikin kwana daya lamarin ya zama babba dan kuwa su dangin mahaifinsa duka tsananin laifin haj maryamah suke gani Dan itace tayi watsi da ‘dan ta Barwa zainab din har Aqeel din yazo gashinan idanba zainab da baya Jin kowa a ransa

Umma tayita kiran wayar Zainab din yafi so dari da dori amma bata samu dan haka takejin kamar ta zama tsuntsuwa tazo ta samu zainab tayi mata duka,

Sun rabu da ita kowa ya kama rayuwarsa amma takasa barin yar uwarta taji dadin rayuwarta da ‘danta

Yanzu gashinan itama ai ta Haifa tata yar tabarsa da tasa uwar taqi.

Hannuwansu su haj kaka suka cire sbd duk yanda sukeson tafiyarsa karatu sunfison farin cikinsa akan nasu dan haka suka hakura Akan yanda yakeso din kuma suka amince da yaci gaba da kulawa da zainab da MARYAMAH..

Jin hakan yasa zuciyar haj Maryamah bugawa qarshe dai saida aka hada da Kaita asibiti dan kuwa jininta yayi mugun hawan data kusa samun matsala.

Umma dataga zasuyi biyu babu sai gata ta iso ba shiri gashi da a ranar zai wuce Abuja Gobe su wuce UK din.

Hankalinsa sosai yatashi ganin Halinda mahaifiyarsa tashiga akan lamarin dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya zauna tareda ita yana nuna mata kulawa da kauna qarshe umma na ganin irin tsananin son dayakewa mahaifiyar tasa itama sai sukayi magana da maryamah sukai shawara.

Shawararsu suka sanarwa Aqeel din akan haj maryamah din zata karbi zainab da ‘yarta su zauna a gurinta insha Allah

Da farko hakan bai kwanta masaba dan kuwa hankalinsa yafi kwanciya da kulawar zainab din a hannun dangin mahaifinsa amma kuma duba da yanayin unman tasa data shiga damuwar tafiya sai kawai ya amince ahakan jikinsa duk yayi sanyii

Yanason zuwa gurin maminsa amma itama Ummansa duk takasa barinsa sbd yanayin jikin nata

Haka ya hakura.

Washe gari tunda safe ya shirya tsaf batareda lokacin wucewar yayiba ya tafi asibiti tareda umma gurin zainab.

Batayi wani mamaki ko damuwar rashin dawowarsa a jiyan ba sbd tariga tasan zuwan nasama Allah kawai yasan irin fitinar da akeyi a gidansu akan hakan.

Ganin umma ya sata jin sanyin jiki dan kuwa tasan dole sai wani abu yafaru umman ke zuwa dan haka tasan akwai wata rigimar

Umman ta amsa tareda Yimata gaisuwar mijinta da Barkan haihuwarta duk lokaci daya.

Aqeel ne da Kansa jiki a mace cikin kulawa yayi mata bayanin tafiyarsa a yau din tareda sanar da ita daga asibiti gidansu zata koma da zama komai ya wuce tsakanunta dasu ummansa sun karbeta ita da little MARYAMAH.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button