Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 10

Sponsored links

Imran ya juyo a fusace zai magana likitan ya ɗaga masa hannu cikin zafin rai yace.

“To in kai jahili ne kaje kabi malamai akan Halaccin wannan cikin gare ka Yau inda baka taɓa kusantarta bane za’a ce ɗan na waje ne, amman Kai da bakinka ka bada shaidar ka kusanci matarka sau ɗaya, ka sani ko tun a daran Allah ya saka ƙwan haihuwar ka cikin mahaifarta,Wannan ɗa naka ne kuma koda baka saka hannu ba ni da kaina wallahi sai na saka sannan nai mata aikin bayan nan kuma na maka ka a kotun musulunci akan kana barazanar kashe matarka da ɗanka akwai CC camera a office ɗinnan duk maganar da mukai tana naɗe dakai wawa”

Jin Kotu yasa jikin Imran ya hau rawa don a wajan cike file har Hotonsa sai da ya saka yasan babu damar Guduwa sabida akwai cikakken bayanin shi da kwatancen sa a Files ɗin daya buɗe a cikin asibitin.

“Zan saka amman Ciki kamar na aljanu ba laulayi babu girma ni a iya zamana da ita babu ta yadda na gane Tana da ciki”

Likitan yace.

“Allah ne yaso ɗan ko ƴar su taka ƙasa shine yasa ya ɓoye sanin ka da jinka da ganinka akan cikin nata”

Daga haka Imran ya saka hannu ran shi a Matiƙar ɓace ya zama dole ya Ɓoye haihuwar nan sabida kada Uban gidan shi yaji wanda Ya nuna masa harkar da yake a yanzu wanda sai da sukai yarjejeniya akan babu batun kusantar Mace ta gabanta har abada sai ta bayanta…………

Yana fita daga Office Ɗin yaci karo da Ummah wadda Ko Kallon arziƙi bata samu wajan Imran ba sai ma wuce tan da yayi ya nufi motar shi ya zauna aciki yana saƙa wasiƙar Jaki na yadda zai salwantar da Amatullah da Ɗan da zata haifa sabida Gudun tonuwar asirinsa a wajan uban ɗakin sa wanda ya mayar dashi kamar matar shi( wa’iyazubillah )

Ummah kuwa Babu abin da take aranta sai zagin amatullah sabida zatonta maganar Ɗazu ce na bijire masan da Amatullah keyi ya saka yaƙi mata magana, Sam Ummah bata ta lafiyar ƴarta sai ta jimamin kada ran Imran ya ɓaci ya sako mata Amatullah suka samu suga rashi.

Cikin Aminci da Yardar Ubangiji akaiwa Amatullah aikin wanda aka samu nasarar Ciro mata Yarinyar ta mai kyau kamar su ɗaya sak da imran sai dai kawai farar fatar uwar ta data ɗauko amman kama kam kamar ka tsaga kara da Imran.

Bayan an gyara yarinyar wadda ko kayan haihuwa babu Sai Likitan ne yacewa Nurse su samo tawul a naɗeta bayan an naɗe ƴar an yanke mata cibi sai akaiwa Amatullah allura aka aje mata yarinyarta a gabanta Likitan yace a barta ta huta har allurar ta saketa.

Koda da nurse ta leƙa waje don sanar da Imran bata ganshi ba kuma bata san Ummah ba sabida haka ta koma ta kuma gyara wa yarinyar kwanciya sannan ta rufo musu ƙofar……..

*Wannan salon na da banne kuma ban taɓa zuwa da irin shi a rubutu na ba mai kike jira ki hanzarta biyan naki dan tuni masu biya sun yi nisa labarin ko rabi bamu shiga ba yanzu ma aka fara*

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button