Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 170

Sponsored links

Wani irin mahaukaciyar dariya ta shiga babbagawa da fadin, “Sai na ga bayansu, sai na haukata rayuwarsu, saina gigitasu. Yanda suka hanamu zama cikin alkaryar kasarmu suma basu isa su rayuwuba. Sai na mulki ruman, sai na mulki duniya, zan zama mafi girma a karfin iko. Matsiyacin tsoho (Kaka) gani nan gareka, nice da kaina zan tsireka a tsakkiyar kasar ruman. Hahahahaha!

Gaba daya na wajen suma suka dauki dariya. Dandanan dajin ya dauki amsa kuwwa. Tako ina dariyarsu amsawa take a cikin dajin..

“Akia, an taba ciwo babu cin abinci, ki daure ko kadan kisha madarar nan sai kisha magani”. Jasrah da dawowarta kenan da ga gidansu tun bayan tashi a kotu data tafi sai yanzu take dawowa, ta sanar ma babban yayansu komai yay mata alkawarin zuwa kuma duk da dama Shahan-shan ya tura masa sako, dan yana daya daga cikin mashawartansa ma akan yankema su Miran Jasim hukunci, kasancewarsa babban malami masani. Kai tsaye dakin Malikat Bushirat ta nufi, shine ta iske ta farka. Ganin jikin nata duk babu karfi tai zaman fara bata madara mai dumi akan tasha kafin ta watsa ruwa sai tai sallolin azhar da la’asar da suka wuceta. Amma Malikat Bushirat din taki amsa sam, gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Lallashinta Jasrah ta cigaba da yi har ta samu ta dan sha madarar kadan. Magungunan ma da kyar tasha. Mikewa tai zuwa bayi ta hada mata ruwan wanka sannan tazo ta kamata ta kaita. Fitowa tai ta barta da rokon tayi wanka koda ruwanne kawai ta zubama jikinta kozai danyi karfi.

 

 

 

 

 

Kamar jira ake Jasrah ta fita aka fara kyalkyala dariya. A firgice ta fara waige-waige sai dai bataga komai ba. Kuka aka fashe dashi kuma. Nama duk ta kidime tuni ta mike zumbur kamar ba itace aka kawo bayin da kyar ba. Sake kwashewa akai da dariya. Sosai jikinta ke wani irin rawar mazari kamar zata amayo zuciyarta ta baki. Tako ina waigawa take amma babu komai sai ita kadai a bayin. Da mugun sassarfa ta nufi kofa da nufin ficewa. Amma ina kofar ta rufe gam-gam babu alamar zata bude, Tanata kiciniyar budewa akai mata wani irin harrrrr!!! Daga jikin kofar sal ga mummunar suffa ta bayyana, baya taja a razane ta kwalla wata irin kara mai tsananin firgitarwa data saka Jasrah dake gyara mata gadon kafin ta fito zabura itama tayo bathroom din a razan

..A guje Jasrah ta fado toilet din da tunanin ko faduwa tayine tunda taga jikinta babu kwari. Wanwar ta sameta a tsakkiyar bayi sume harta farke hannu da wani dan karfe da

 

akaima bayin ado da shi. Ai batama san ta fasa razananninayar kara ba tai kanta itama a kidime. Jijjigata ta shigayi amma babu alamar rai tare da ita. Sai kawai ta sake fashewa da kuka, dan a rayuwa tana matukar kaunar yar uwar tata, itace ta zame mata uwa a lokacin da suka rasa mahaifiya. Ta mata gata irin na Va da uwa bata taba banbantata da dan data haifa ba. Zama ta iya cewa ta fishi samun gata dan shi an dauke sa a gabanta.Itako tunda tasan kanta a gabanta take,duk abinda tace tana so shi take yimata.Idan tashin hankali yay tashin hankali baka tuna-mai ma ya dace kayi, kuka kawai take faman rusawa tama manta a bayi suke.

 

Diwa da ke tsaye a bakin kofar dauke da kayan lunch da ta kawo ma Malikat Bushirat din ce ALLAH ya jiyar kukan Jasrahn. Dama kuma itace tace ta hado abinci mara nauyi ta biyota da shi. Bata da hurumin shiga dakin sai da izini, ga kuma kukan tashin hankalin da takeji Jasrah nayi. Tray din ta ajiye cikin dan rawar jiki ta fice zuwa sashen Malikat Haseenat. Suna zaune a falo Daneen Ammarah na faman lallaba Ummu ta sake kwana itako ta ce yau sai gida zataje suyi shirin tarbar amarya gobe insha ALLAHU sai ga Diwa ta shigo a firgice. Kallon mamaki gaba daya suka bita dashi, Daneen Waheeda Sarkin masifa ta daka mata tsawa dan abinda Diwar tayi babban tsaurin ido ne. Malikat Haseenat ce ta katseta da fadin, “‘a Waheeda wannan ba dai lafiya ba bita a hankali. K! Miya faru ne?”. Kuka Diwa ta fashe da shi tana nuna bayanta bayan ta zube a kasa. “Ku gafarceni ranki ya dade, babu lafiya ne gaskiya. Ga Aunty Jasrah can nata kuka a dakin Malikat, da alama akwai matsala ne why, tabbas akwai matsala, dan dama likita nata zaryar dubata tsakanin jiya da yau”

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button