Hausa Novels and Stories

Idon Naira 33

Sponsored links

Cikin dan boye mamakinta tareda kokarin basar da tsananin fushi da bacin ranta akansa na tun jiya daya kasa ko daukan wayarta Sam yaqi lokacinta..,

Miqewa yayi daga zaman da yayi yabar gurin

Kai tsaye mai aikin gidan yakira ya bata umarnin hada breakfast lafiyayye a basket tukuna ya wuce bangarensa.

Tubewa yayi ya zari towel qarami ya rataya a wuyansa daga shi sai Qaramin boxers ya nufi toilet.

Wanka yayi yafito ya shirya Kansa na tsananin sarawa da alamarma idan ya kwanta zazzabi shigarsa zaiyi

Gaishi da komaima a gabansa yana neman rikice masa dan kuwa a yanzu da maminsa tayi irin wannan haihuwar bazai iya tafiya yabarta ba,

Ga rasuwar Mijinta,

Ga haihuwar bagatan,

Ga babyn na incubator

Tayaya zai tafi yabarta a wannan yanayin bayan yasan babu Wanda zai iya kular masa da ita.

Cikin black qananun kaya yafito yasa samira takai masa basket din mota ya fice daga gidan Kai tsaye batareda yaje gurin ummansaba tasan da fitar tasa dan zata iya kawo masa wani uzurin dazai hanasa fitar.

Koda yakoma asibiti Maminsa ta tashi tana zauna fes cikin wasu kayan da alama sun taimaka mata tayi wanka ta sake shiryawa

Fuskarta ya kalla yaga babu walwala ko farin ciki saima sake shiga damuwa da tsoron babynta kada itama ta rasata,

Tea ya hada mata dakansa ya zauna gefenta yana kallonta cikin tsananin kulawa da bata tabbaci yace,

“Mami kada ki taba yankewa kanki rahama dan rahamar ubangiji bata yankewa,

Ina nan,matuqar ina raye mami dake da babyn nan bazaku taba rasa gatanku ba insha Allah,

Wannan babyn zan zama gatanta,

Zan bata farin cikin da kowanne dan yake fatar samu wannan alqawarina ne idan Allah yabani tsawon rai da lafiya to tabbas nine babban yayanta kuma ubanta dazai tsaye mata a komai dan haka mami kada kisa damuwa kiyi mata adduar samun lafiya baba Malam kuma adduar samun rahamar ubangiji.

Da yake kukanta ya qafe qyam baya zuwa tun jiya dan haka bata iya cewa komaiba saima Jin nauyin zuciyarta daya qaru duk da alqawarin da Aqeel din yayi mata akan future din ‘yarta sai hakan ya sata shiga fargaba idan aqeel din ya tafi kafin yadawo waye sukedashi.

Daqyar ta iya cin abincin daya tilasta mata ci dan daga bakinta har maqoshinta zuwa cikinta abincima kamar yankar matasu yakeyi a halinda take ciki.l

Bayan tagama akace zaa kawo mata abubuwan da zata ja Nono zaa je abawa babyn.

Aqeel ne yakuma bada kudi aka siya komai aka kawo mata nurses biyu suka taimaka mata aka dan samu nono shima daqyar da wahala.

Neman alfarmar ganin babyn Aqeel yayi suka tafi tare harda Mamin wadda take tafiya a hankali sbd rashin karfi da damuwar data gama ci da mamaye kuzarinta.

Suna isa saida aka dauki mintina kafin nurse ta fito da babyn kointa a rufe dunqule cikin tattausan bargo mai tsada da kyau pink ta miqawa Aqeel din ita.

Nauyi yaji zuciyarsa tayi lokacinda aka miqo masa babyn saida ya sauke numfashi boyayye kafin ya miqa hannayensa ya Karbeta cikeda tsananin so da Kaunarta tun baiga fuskartaba.

Gefen mamin ya dawo ya zauna tareda dan bude musu babyn suna zubawa ‘yar qaramar fuskarta idanuwansu kowanne cikeda Kauna da tausayin tazo duniya a marainiya.

Wani numfashi mai zafi da qunci Zainab ta sake tareda Dagowa ta kalli Aqeel daya kasa dauke idonsa akan babyn Ahankali ta iya furta,

“Aqeel kai kadai takeda kayi mata huduba da suna..

Dama abinda yake shirin yi kenan saidai sunan dayake Ransa yana fatar idan ya saka hakan yasa kaunar babyn yashiga ran mai sunan..

Ahankali ya dagota sama yakawo daidai fusktarsa yayi mata huduba tareda kiranta da sunan MARYAMAH..

Kallon maminsa yayi alokacinda ya furta sunan daya sakawa babyn a fili…

Batace komaiba kamar yanda har cikin ranta bataji komaiba na damuwa ko rashin jin dadin sunan,

Har a ranta sunan yayi tunda shine ya zaba sunan,

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button