Hausa Novels and Stories

Fulani Page 9 Hausa Novel

Sponsored links

Ta amsa masa ita ma tana turo baki gaba kamar za tai kuka sannan ta mike tsaye rike wayarta ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta.

Zainab ta daga kai tana masa wani shegen kallo.

“Look at you Sirleem sai ka rika yin abu kamar wani fool ya zaka shigo a gaban mutane kana tambayarta miye take a waje? Kamar wani ubanta

Runtse ido yai ya bude cikin bacin rai ya c

“Hajiya Karama babu ruwanki a cikin wannan maganar, idan ina magana da Nana ki daina saka min baki

“Oh really? To ko dukana zaka yi?”

Ta fada tana mikewa tsaye, daman can ita da shi ba sa shan inuwa daya.

Sai a lokacin ne Shattima ya daga ido ya kalleshi ya kalli Zainab.

“Please Hajiya Karama tafi dakinki”

“Amman….”

Bata karasa ba maganar ta makale sakamakon kallon umarni da Shattima yai mata sai ta duka ta dauki wayarta ta fice daga falon. Shattima ya kalli Muhseen yana murmushi kamar ba shi ba yace.

“Muje sashena ka huta na san yanzu za a fara jera maka abinci dan gidan Mai Martaba”

A tare suka fice da Muhseen din aka bar Salim tsaye a falon kamar wani wawa.

FADIME POV.

Busar sarewar nan da take yawan ji a mafarki ta soma jiyowa tana tashi a hankali.

Kwantar da kanta tai jikin kafafuwanta tana sauraren yadda busar ke ratsa kunnuwanta tana saukar da nishadi a zuciyarta busa ce mai ban tausayi mai saka shauki da dadin saurare, a iya lissafinta tana tuna mafarkinta ne shiyasa take jiyo busar, hakan yasa ta rufe idonta tana ta ganin mutumen nan mai busar sarewa na mafarkinta, a kullum idan tai mafarkinsa baya yake bata bata taba ganin fuskarsa ba, yana daure da walki jikinsa babu riga.

Jin kamar a zahiri ake busar yasa ta bude idonta ta mike tsaye ta saki sandar korar shannun da ke hannunta, sai ta ji karar busar sarewar yana karuwa kamar ana kusantota, waige waige ta fara yi sai kuma ta juya da sauri ta nufi gurin itatuwan masara ta kusa kai ciki domin a ciki take jin kamar busar na fitowa, tana tafiya tana juyawo tana ratsa shukar masara ta ko’ina, can kuma ta juyo sautin kamar a inda ta baro ta juyo a guje ta dawo gaba daya hankalinta ya tashi domin bata taba jin busar a zahiri ba sai a yau, saman katon dutsen dake gaban shanunta ta haye tana hawaye tana waige waige ko zata hango mai busar ko kuma tabbatar da inda sautin busar ke fitowa amman sai ta ji abun ya karade ilahirin dajin gaba daya, faduwa tai a gurin ta dafe kanta tana kuka domin a yanzu ta fara tunanin ba azahiri take jin busar ba a cikin kwakwalwarta ne.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”

Ta furta tana kara runtse ido tana girgiza kai domin har lokacin bata daina jin busar sarewar ba, ta dade a gurin tsugune, sai da ta daina jin busar sannan ta mike tsaye tana kallon shanunta da ke kasa, a take saniya daya ta yanke jiki ta fadi a gurin tana shure shuren mutuwa, Fadime na ganin haka ta sauko da mugun gudu ta nufi hanyar gida tana wani irin kuka na tashin hankali, @250 ta isa gida kamar wata mahaukaciya ta fada cikin gidan tana kururuwa.

“Inna Inna yau ma nagge guda ta fwadi, gata can tana shure shure Inna mutuwa za tai”

Ta fada da yaren Fulatanci tana haki kukan kuma ya ki ya tsaya mata. Da sauri mahaifiyarta ta aje tasar nonon da take ta nufo inda take ta rikata.

“Yau ko mun shiga uku da wannan lamari haka kullum za yi tai zama? Tafi ki fada ma Malam yana gonarsa”

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button