Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 9

Sponsored links

Karap wannan magana a kunnen daddy da ya zama very shocked tinda suka fara jiyo maganganun momma……

 

Abdul ne ya ankarar da momma da tsayuwar daddy, ta jiyo sukayi ido hudu da daddy daya dafe kansa yana jinsa highly betrayed!….

Zatayi magana kenan ya daga mata hannu sannan yace ta tafi gida sai ya nemeta dan yasan inta cigaba da zama a gidan yana ganinta komai ze iya faruwa…

Har kasa ta tsuguna tana basa hakuri daya bata second chance zata rike yarinyar da gaskiya dan denying be taso ba tinda ya riga ya kamata red handed……

Dago fatima zainab yayi data riga ta farka ya rike hannunta yayi hanyar fita da ita……

“Kullum saina tambayeki a waya babu abinda ake miki sai kice min babu, meyasa baki taba fadamin abinda take miki ba daughter? Meyasa?”…..

“Tace zata kasheni idan na fadamaka”….

“Karki damu babu abinda ze sameki da yardar Allah, daga yanzu duk wanda ya miki wani abu a gidannan ki fadamin kinji daughter?”…..

“Toh daddy”…..

Part dinsa ya tafi da ita yana kiran mama a waya…. Shigowa mama tayi da sallama hankalinta na kan fatima zainab, guri daddy ya nuna mata ta zauna, yayi gyaran murya ya fara magana;

 

“Hakika hafsah kinmin abinda ban taba tinanin zuciyarki zata bari kiyi ba, kin ankarar dani muguntar da akeyiwa marainiyar Allah da bataji ba bata gani ba, a yanzu bazan iya bari ta kara zama a gurinta ba, bansani ba ko ke zaki iya rikemin ita amana?”…..

 

“Nasan kanamin kallon wacce bata da kirki saboda yanda nake nuna kishina akan ka a fili, inaso ka sani son da nake maka ne yasa nake behaving haka, amma wallahi Alhaji bazan iya cutar da kowa akan hakan ba, ka jarrabani zan rike maka ita fiyeda yanda kake tinani”…….

“Kinyi alkawarin zaki riketa tsakani da Allah? In kinsan bazaki iyaba kema gwara ki sanar dani in nemi inda zan kaita”…

Daddy ya sake tambaya dukda ya gamsu da maganganunta, ya kuma yarda tana son shi sosai kamar yanda ta fada, kuma ko ba komai gwara ita tinda tana nuna abinta a fili akan momma me munafurci……..

“Nayi wallahi, tawo daughter kinci abinci kuwa, taso muje naga kamar ma bakya jin daddy”…..

Murmushi daddy yayi yacewa fatima zainab ta tashi ta bita…….

Daganan wani sabon phase na rayuwarta ya sake budewa, inda ta gwammaci zamanta a gurin momma so dari akan mama, a takaice dai lamarin rayuwarta sai ya kara hargitsewa, da farko mama ta dan fara sata aiki saidai ganin yanda take kwabamata yasata gane bata iya komai ba, nan tace bazata zama me koya mata ba wallahi gwara ta saura a haka yanda duk inda taje bazata moru ba, ada da take kwana a kitchen sai mama ta maida gurin kwananta store, batasan store din ya fiye mata kitchen ba dan koba komai yafi dimi dukda ba fanka ba fitila ga beraye, nan fa shayeshaye yaci uban na da dan wani zubin sai tayi kwana biyu a kulle a ciki, gane hakan ne yasata take siyo codeine in excess tazo ta boyeshi tayita sha tana mayenta ita kadai, gashi mama ta iya takunta dan daddy ko momma basu taba gane halin da take ciki ba, daddy har dena tambayarta yayi ko akwai abinda ke damunta ganin kamar mama na iya bakin kokarinta akanta, a lokacin duka yayan mama boarding sukeyi amma in suka dawo hutu suyita mata rashin mutunci iri iri, momma da take hanata abinci na kwana daya sai gashi tagamu da mama da sai tayi sati biyu abinci, abu daya ke taimakonta kusan kullum sai daddy ya kirata sunsha fruits a part dinsa hakan yasa ta saba da rashin cin abinci, sai ya zamana ko an bata abincin batasan ci dan bata saba ci ba, shiyasa gatanan kullum sai a hankali ba auki sai shegen kyau, taimakonta daya tanada diri sosai kuma duk raman da zatayi iya fuska ne da wuya amma mazaunanta da hips dinta basu san anayi ba, kadama boobs dinta suji labari…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button