Hausa Novels and Stories

Idon Naira 31

Sponsored links

Wurgi Zainab tayi da wayar da qarfi Tana sake fashewa da kuka sosai Mai bayyanarda tsananin qunci da radadin dake cikin zuciya da jininta ga wani ciwon Mara Mai qarfi daya soketa a take sbd tsananin tashin hankalin baqin ciki da qunci wani akan wani..

Irin kukan datakeyi yasa AQEEL daya kusa isowa gurinta ya qaraso da sauri hankalinsa na sake tashi sbd bai taba ganin Mamin tayi irin wannan kukanba.

Yana isowa gurinta taji nauyin zuciyarta ya qaru sbd itadai Allah ne ya saka Mata kaunarsa fiyeda komai Amma koyaushe baqin jininta da kukan da ake sakata akansa ne….

Wane tashin hankali yafi na rashin mijinta Wanda shi kadai ne gatanta,

Rufin asirinta,

Uban cikinta, tarasashi ayau Amma ko ayau din laifinta ake gani tareda gorin haihuwa da maganganu masu qunar Rai da qarin radadi akan Wanda tasamu kanta aciki yau.

Neman rikicewa Aqeel keyi da yanayinta Amma ta dakatar dashi ta hanyar dakatar da kukan nata aka Basu gawar a motar asibiti suka nufi gida.

Koda suka iso gida kusan duka dattijan anguwa wasu daga jama’arsa da dalibansa manya da yara kusan duk sun fara halarta Dan Jin labarin rasuwar tasa.

Babu Bata lokaci aka hau gyara gawar Dan janaizarsa,

Aqeel duk da matashi ne da shekarunsa Basu Gama zama na manya sosai ba dashi akai komai sbd shine tamkar Dan malam din Dan Haka kusan kowama shi yakewa gaisuwar rasuwar

Ahaka akai janaizar Malam Umar Sanda mijin Zainab aka kaisa gidansa na gaskia.

Dangin mahaifin Aqeel din wasu da yawansu sun halarci janaizar sbd Malam din dakuma Aqeel dayayi rashin wani uban a Karo na biyu.

Gashi rasuwar ta dakesa sosai shima kamar yanda tayiwa Zainab mugun duka.

Acan cikin gida kuwa Zainab Tunda suka dawo makotanta ne a tareda ita suna tayata zaman,.

Bayansu batada dangi batada kowa da zaizo Mata.

Haj maryamah sai bayan da aka kaisa makwancinsa aka dawo Aqeel ya iya samun damar kiranta ya sanar Mata abinda yafaru.

Addua tayiwa malam din tareda nema Masa rahamar Allah daga Hakan sukai sallama.

Umma Haj maryamah dince takirata ta sanar da ita sai alokacin ta fahimci abinda yasa Zainab ta kashe Mata waya dazu Dan kuwa harta dauka zafi da Hakan matuqa

Itama adduar samun rahama tayiwa malam Sanda din sukai sallama.

Kiran wayar Zainab din sukayi su dukan Dan Yi Mata taaziya Amma Bata shiga sbd Tunda tayi wurgi da ita a asibiti batasake bi kan neman wayarba Hankalinta baya kan wayar kwata kwata.

Da daddare gidan yakoma daga ita sai Aqeel Wanda daqyar ya iya sata taci abinci da maganin zazzabi sbd zazzabi Mai qarfin gaske ta wuni dashi dan har wani hucin zafi jikinta keyi na zazzabi…

A gidan ya kwana palon malam sbd bazai iya barinta takwana gidanba ita kadai sbd yanayinta.

Cikin tsakiyar dare ciwon Mara Mai qarfi dataketa daurewa tun safe ya taso Mata gadan gadan..

Tsoro da tashin hankalin rasa cikinta yasata kasa neman Aqeel ta zauna Tana hawaye da hada uban zufan azaba.

Cikinta wata bakwai ne tasan bai Isa haihuwaba Amma ayanda takejin wannan azabar da wuya idan ba barin cikin zatayiba.

Acan bangaren Aqeel Tunda ya shige yaketa sallolin darensa daya saba

Yana idarwa yayi adduoinsa ya zauna Yana Shiga tunanin daketa addabar ransa tun Bayan janaizar Baba malam wato jibi ne tafiyarsa Uk

Yaya zaiyi da Maminsa kenan yanzu??

Ga juna biyu ajikinta Dan Haka a yanzu dinne tafi buqatarsa itada babyn Dan kuwa sunzama amanarsa yanzu,

Sun zama ahalinsa da zai tsaya musu ya zama gatansu Dan kuwa Amanar Hakan ce malam yabar Masa alokacinda ya kafesa da ido gabanin rasuwar tasa.

Yanzu tayaya zai iya tafiya yabarsu anan tsawon shekaru?

Waye zai kula Masa dasu kafin yadawo din??

Bazaiso qaninsa ko qanwarsa su taso ba acikin gata da kulawarsaba…….

Nishin Maminsa Mai qara yasashi juyawa ya kalli kofar palon Yana Dan miqewa tsaye ahankali yanufi kofar Dan tabbatarda abinda yakeji.

Wani wahalallen nishin takuma saki cikin azaba

Ba shiri ya fito Yana Kiran sunanta cikin kulawa da damuwa daga bakin kofar dakinta yace”

Mami bakida lafiya ne?

Meyake faruwa??

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button