Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 37

Sponsored links

Tsaye khaleel da sameer suke a gaban burnt building din fatima zainab,idan akwai abinda yafi shock toh khaleel yashiga,he couldn’t believe what his eyes just saw,like how can someone be this wicked?… Anya wasu suna tinanin kiyama kuwa?, Yanzu akwai wanda ze iya kona mutum dama?,shi besan tsanar da mama take yiwa abun sansa ya kai hakaba,gsky baze kyale ba dan in aka cigaba da tafiya a haka tabbas wataran saidai a kirasa ace masa fatima zainab ta mutu,so dole ya dau mataki……

 

Sameer ko sakin baki yayi yana kallon ikon Allah tinda shi besan komai ba,kallon khaleel yayi yace

 

“Dude gobara akayi a part dinnan ne?”

 

“Yes,not quite long”…

 

“Innalillahi,I hope ba kowa a ciki?”……

 

Kamar ya fadamasa wa akaso konawa,sai kuma ya fasa yace

 

“Fortunately ba kowa a ciki!”….

 

“Toh Alhamdulillah,Allah ya kiyaye gaba”….

 

“Ameen,mu karasa part dina”…..

 

Saida khaleel yayiwa sameer providing duk wani abu daze bukata sannan ya sake fitowa,so yake yaje ya ganta koya samu nitsuwa dan yasan bazata wuce part din momma ba,plus he needs to do something about mama…… Hango daddy yayi da shigowarsa kenan ya nufi part din fatima zainab ganin kamar gurin a kone yake…… Karasawa inda daddy yake yayi yashiga kallon building din kamar be gani ba dazun,shidai haryanzu ya kasa dena mamakin wannan abu…..

Kurawa building din ido daddy yayi yana mamakin yanda abun ya faru,kuma a rasa wanda ze kirasa ya fadamasa,saidai kawai yazo ya gani?…. Kallon khaleel daya tsaya a gefensa yayi yana tinanin shikuma yaushe yazo?…..

“Son yaushe kazo?”…

“Not quite long!”…..

“Kaga abinda ya faru ko?,Amma daughter bata ciki ko?”…. Daddy ya fada kamar khaleel a gidan yake da ze san meya faru

 

“Yes abinda ya kawoni kenan,Abdul ne ya kirani yake fadamin,he overheard conversation din mama akan kona fatima zainab”…..

 

Saida kirjin daddy ya buga duk da be kamata yayi mamaki ba tinda yasan yanda mama ta tsani fatima zainab,a rikice yace

“I hope dai bata ciki?”….

“It was confirmed that tana ciki,tambayi me gadi kaji,koda fire extinguishers sukazo suka kashe wutar sun tabbatar da komai na ciki is completely burnt,so ko gawarta an kasa ganewa,ta mutu a ciki”…. Khaleel ya fada da gangan duk da yasan bata ciki amma so yake ya ruda daddy yanda dole ya dau mataki akan mama,sai daga baya kuma yace bata mutu ba…

Zubewa a kasa daddy yayi ya daura hannu aka ya shiga salati kamar wani zararre,a gigice yace

 

“Nashiga uku,kace ta mutu? Innalillahi wa ilaihi raji’un,nooooo!”…….

 

Gyada kai khaleel yayi alamun tabbatarwa dariya na cinsa a rai,in banda rudewa irin na daddy taya zaace fatima zainab ta rasu aganshi a tsaye kan kafafunsa?,ai kila ma da tini ya bita… Amma yaji dadi da daddy be kula da hakan ba,da alamu plan din shi will go well…..

 

Mikewa daddy yayi a zabure cikin ihu yace

 

“Ina hafsan take,nace ina take?,Wayyo Allah ta kashe yar mutane?”…..

 

Sai kuma ya nufi gurin megadi da sauri be ko jira yaji abinda khaleel zece ba…..

 

Da sauri khaleel ya nufi part din momma dan ya samu suyi magana da fatima zainab,ya kuma boyeta har sai plan dinshi ya tafi daidai,saidai me? Yana zuwa yaga be ganta ba,nan hankalinsa ya tashi yashiga duba ko ina….

 

Megadi daya dawo bayan komai ya lafa ya kwashe komai tass ya fadawa daddy,ya kuma tabbatar masa da tana cikin kuma ta kone(dan shi besan bata ciki ba)….

 

A hargitse daddy ya nufi part din mama,ko sallama beyi ba ya shiga bugun kofar ganinta a rufe kasancewar mama ta rufe dan gudun kar fatima zainab ta kara dawowa…. Da karfi ya cigaba da buga kofar yana fadin

 

“Hafsah zoki bude kofarnan kafin na ballata”… Dan ganin kofar a rufe ya kara tabbatar masa da batada gaskiya….

 

Jin muryar daddy yasa mama ta fito tana dingishi ta nufi kofa dan su husna har lokacin basu budeba…

 

Bude kofarta yayi daidai dajin saukar wani kykkyawan mari a kuncinta da yariga yayi jahur dalilin marin da tasha a gurin fatima zainab

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button