Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 28

Sponsored links

Wani mashahurin farin ciki ne ya lullube sameer,dama abinda yake jira kenan yaji,yasan kuma tinda Deen ya masa alkawari to tabbas ze cikamasa dan shi baya saba alkawari!!……

 

Parking motar yayi a parking space din gidan ya fito da sauri ya budemata kamar yadda ya saba,fitowa tayi a hankali ta nufi ciki,karo sukayi da mama da fitowarta kenan daga sashen alhaji….. Fatima zainab bata wani yi mamakin ganinta ba dan tasan dama bazata hakura da alhaji ba…..

 

Wani taku mama tayi ta karaso inda take tace “Yan mata yasan ranki?,kinganni nan,nida alhaji mutu ka raba wlh,ina miki albishir da cewa Alhaji ya mayar dani dakina”… Ta fada tana shekewa da dariya…

 

Bata kulata ba dan bata ita takeba yanzu,abunda yake damunta yafi karfin ta biyewa shashancin mama,part dinta ta nufa mama ta bita da kallo tana jin takaicin kin kulata da fatima zainab batayiba …….

 

Itako fatima zainab tana shiga ta rufe kofarta ta cigaba da harkar gabanta…….

 

Wani dariya mama ta saki tuno da sai yanda tayi da alhaji yanzu,abu kamar wasa mallamin chan yace ta kawo dubu dari biyar kan aikin da ze mata akan alhaji,hankalinta ne ya tashi ganin batada wani isassun kudi tinda tabar gidan alhaji,gashi ta tatike kanta tasiya wani dan karamin gida dan bazata iya komawa garinsu ba,hakuri ta dinga bawa mallamin akan dan Allah ya mata ragi,shiko ya rufe ido yace aikinsa kamar yankan wuka yake dan haka shi baya ragi….. Buga buga tashiga yi amma shiru ta kasa hada kudinnan,haka tayi shahada ta karbi loan a bank akan in an mata aikin ta koma tasan dubu dari biyar chicken change ne in tana gidan alhaji…… Haka kuwa akayi takai masa kudin,a take akayi aikin ya bata wani kwalli yace tasa ta kuma tabbatar ta hadu da alhaji dan baa so abun ya kwana gudun kada aikin ya lalace,daga gurin mallamin office din alhaji ta nufa straight da yake da rana ne bayan tasa kwallin,batareda neman izini daga gurin alhaji ba suka barta tashiga dan su sun dauka har a lokacin matar alhaji ce ita…. Tana shiga sukayi ido hudu da alhaji,atake alhaji yaji wata zazzafar soyyayar mama ta saukarsa,yaji duk duniya ba macen daya keso ya kalla yaji dadi kamar mama,wani mahaukacin soyayyar mama ce ta lullubesa har yakejin ba abinda baze iya sadaukarwa a kanta ba,yaji duniyar tadawo masa sabuwa gabadaya…… Daga nan komai ya chanjawa mama,take jin kamar duniyarma a tafin hannunta take tsabar yanda alhaji ya sakar mata komai take jansa kamar rakumi da akala…..

Karasawa parking space tayi tashiga motar data zabi fita da ita a ranar…..

 

Driving take amma ko in kular da fatima zainab tamata ya tsaya mata a rai,bata tabajin ta tsani mutum kamar yanda takejin tsanarta ba,ita bataki ta taka fatima zainab da mota ta mutu kota ji sanyi a ranta,wata zuciya ce tashiga zugata akan tayi wani abu yau,yanda ganin fatima zainab ya zama kamar ruwan dare gwara tayi using wannan opportunity din,gashi kuma sai yanda tayi da gidan a yanzu so ko tayi wani abu tasan babu wanda ze daga ido ya kalleta,petrol station din dake kusa dasu tanufa,shiga tayi ta siya petrol 25ltr,sukasa mata a boot ta nufi gida….. Me gadi na bude mata gate tace yazo inya rufe… Sashi tayi ya daukar mata petrol din ta nufi sashen fatima zainab yana biye da ita….. Sashi tayi ya ajye ya dauko mata ashana,dauko ashanar yayi yana mamakin mezatayi dashi…..

 

“”Dauki petrol dinnan ka watsa minshi a ko ina na building dinnan”….

 

“Ban fahimceki ba hajiya” Ya fada a diririce ganin fatima zainab na ciki dan yaga shigarta,yana zaune kuma bega ta fito ba

 

Wankeshi da mari mama tayi tace “Dauki ka zuba nace,ko a bakin aikinka wlh”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button