Hausa Novels and Stories

Idon Naira 32

Sponsored links

Da saurinsa ya shigo Yana kallonta zaune ta hada gumi da hawaye sosai

Kusan ma azabar taci qarfinta da Haka ba wani tsaiko Tunda baisan mezaiyiba ya kamata suka fito

Allah yasa motarsa na taredashi bai aka gida ba sbd Nan din ba gurin ajiye motar Dole sai kofar gida.

Dare ne sosai Amma baiji shakkar komaiba ya nufi asibiti da ita

Duk hankalinsa yagama tashi,

Tsoro yakeji yanzu na mutuwa,

Yana tsananin son Maminsa bazaizo mutuwa ta rabasu ba yanzu,

Idan itama ta tafi tabarsa a duniyarsa baida kowa kenan Dan kuwa Maminsa itace yakejinta a jininsa tamkar itace jininta yake yawo ajikinsa.

Kai tsaye labour room akai da ita sbd da Alama haihuwace tazo Mata gadan gadan Babu shiri lokaci baiyiba.

Kasa zama yayi Tunda aka Shiga da ita gashi yakira wayar ummansa yafi so ashirin Bata dagawa duk da yasan darene Amma yasan batada nauyin bacci Kuma takan tashi itama sallar dare wani lokacin Dan Haka zaiyi wuya a nemeta baa sametaba da dare.

Magani da duka abubuwan da ake buqata aka rubuta Masa yaje pharmacy din dake cikin asibitin ya siyosu Komai ishashe Mai yawa.

Bayani sukai Masa na cewan preterm labor ce maana haihuwa a wata bakwai din zata sbd matsalolin da cikin yasamu gashi bai kaiba.

Da sauri ya juya ya nufi gurin motarsa saikuma ya tsaya sbd yasan Babu inda zai samu shago a lokacin

Dawowa yayi Yana jiran afito sallar asuba dasuke kokarin Shiga shima yai alwala ya Shiga masallacin.

Ana idarwa sama sama yayi adhkar ya fito ya ja mota ya nufi gidan tsohon driver din Dadynsa da yanzu shagone dashi na siyarda Kaya.

Aminu na masallaci Aqeel yazo nemansa Dole ya dauko mukalullan shagonsa suka nufi shagon ya bude ya basa kayanda yake buqata

Shima Dole transfer yayi Masa Dan Babu cash a jikinsa,

Allah Kuma sai yasa shagon nasa baa sakuwa yakeba da Babu Wanda zai bude musu kasuwar alokacin.

Koda ya dawo asibiti da siyayyar kayan baby masu yawa sosai har Allah yasa Zainab din ta haihu lafiya ta samu baby girl wato ‘ya mace saidai babyn batada qwari ko kadan Dan Haka Yana kawo kayan aka Danyi Mata Shiri aka sakata cikin babys incubator da ake aje jarirai irinta.

Da farko tsoro yaji Jin babyn na cikin kwalba Amma Kuma sun Masa iya bayaninda zai gane yakuma ganar da mamarsa kamar yanda suke tunani.

Bacci Mamin tasamu bayan magani da allurai tareda tea Mai zafi datasha Dan Haka sai alokacin yasamu ya tafi gida guraren 9 na safe kenan.

Gidansu ya nufa direct sashen mahaifiyarsa ya nufa ya taddata zaune akan dining Tana breakfast a shirye cikin shigar dake nuni da fita zatayi.

Qarasowa yayi jiki a mace yana gaidata ya zauna kan dining din ya zuba ruwan zafi Yana hada tea.

Kallonsa tayi lokacinda yake Shan tea din ahankali cikin sanyi da nutsuwa tinaninsa nakan Maminsa.

Zatayi magana ya dago ya kalleta cikin nutsuwa yace”

Umma Mami ta haihu da asuba yau Amma babyn is not okay Tana incubator..

Kallonsa tayi cikeda mamakin Dama Zainab cikin da aka fada gaskia ne harya tsufa da haihuwa yanzu haka..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button