Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 73

Sponsored links

Kai kawai khaleel ya daga masa batareda yace komai ba…….

 

Cikin tausayawa daddy ya kuma fadin;

 

“Don’t worry son, ina nan ina nemota, Insha Allah fatima zainab bata da wani miji sai kai, so ka kwantar da hankalinka kasamu lafiya sosai, ko kanaso tazo ta ganka duk a ramene?”……

 

Da sauri khaleel ya girgiza kai kamar wani karamin yaro abundai gwanin tausayi…..

 

Haka daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali yana basa assurance akan lallai sai fatima zainab ta zama matarsa har akazo aka mishi injection yayi bacci sannan daddy ya tafi………

 

Hira sukeyi isu isu yan dakin sunata shafta abunsu, eesha ce ta kalli spot din fatima zainab tace;

 

“Wannan unknown girl din anya lafiya take kuwa? Tun kafin a fara tests fa tabar hostel gashi har zaa fara exam next week, nidai na fara jin tsoro”……

 

Bilkisu ce ta karbeta da fadin;

 

“Gsky dai lamarin akwai question mark, kodai bata da lafiya ne bamu sani ba?”…..

 

“Zatayiwu wallahi, gashi bamusan ta ina zamu fara nemanta ba”…..

 

Cewar eesha fuska dauke da damuwa…..

 

Bata rai umaima da bata wani sa musu baki a hirar ba tayi tace;

 

“Toh ku ina ruwanku da wanda be damu da ku ba? Haka ta zabarma kanta sai kuyi minding business dinku mtssssssss”…….

 

Harararta eesha tayi taja tsaki itama tace;

 

“Muma bamu sako ki a hirar mu ba, ai ko makiyinka ne kaga baka ganshi ba ana shirin exam ai ka jajanta”…..

 

“Sai kuyi kuma, kila ma tanachan tana zuwa lectures abunta kunanan kuna damun kanku”……

Umaima na fadin haka tasa ear piece…..

Basu damuba suka cigaba da jajanta lamarin fatima zainab…..

Duk minti minti yake duba agogo yana expecting dawowan Deen anytime soon, tun yana a kishingide har bacci barawo ya kwashesa be sani ba…..

Wani mummunan mafarki ne ya tadasa daga baccin gajeran lokacin daya daukesa , wai Deen ya tafi da yarinyar gurin daurin auren, yana zuwa kuma yace a daura dashi, sai gashi ya dawo da yarinyar yana fadamasa yayi hakuri anriga andaura dashi…..

Wani mugun gumi ne yashiga keto masa, yana gogewa yana fadin ‘Allah ya kiyaye, Allah ya kiyaye’…. Shiyasa fa akace mafarki ba gaskiya bane, to in banda karyan mafarki ta ina Deen ze auri wacce ya fara gani a yau dinnan yanda yake babu soyayya a tsarin rayuwarsa, aiko auren zeyi sai wacce ta dage ta chusa kanta har Allah ya taimaketa ya sota sannan….Ballema yasan Deen baze iya stooping so low yaso yarinyar da shida khaleel suke fama akai ba……

Zaman gidan ne yaji ya ishesa kawai ya fita waje domin yasha iska ya kuma jira zuwan Deen dan yasan duk abinda ake yanzu yaci ace anshafa fatiha an tawo masa da amaryarsa…

Ko minti daya beyi ba a bakin gate wani kyakkyawan mutum yazo ya masa sallama yana mika masa hannu, gaisawa sukayi cikin mutunci, sannan sameer yace;

“Saidai bangane waye ba, kodai sabon makoci mukayi ne?”….

Dariya yayi yace;

“Eh kusan haka dai, dama wani abu nazo in fadamaka dukda bansani ba koshi kake nema”..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button