Hausa Novels and Stories

Idon Naira 28

Sponsored links

Cikin ikon Allah da rabo daga garesa wani babban al’amarin farin ciki ya samesu na samun rabon ciki daga Zainab.

Sunyi murna sun godewa Allah musamman malam Sanda sbd yariga ya tsufa baida ‘dan Kansa

Lamarin da kwata kwata bai saka raiba badan ya cire Rai daga rahamar ubangijinsa ba.

Zainab kuwa kunyar kanta ta ringa ji musamman da cikin yafara girma Aqeel ya gane.

Shi Kansa Aqeel din yaji nauyin Amma farin cikin daya shiga yafi na nauyin Dan haka sai ya zama shine yake kulawa da ita sosai.

Da Kansa yakaita asibiti akai Mata komai na ganin likita duk Bayan sati biyu.

Duk ranar zuwa ganin likita shine yake kaita ya dawo daita..

Babbar damuwarsa da rashin Jin dadinsa shine baya qasar Maminsa zata haifar Masa ‘dan uwansa ko ‘yar uwarsa Wanda ya tabbatarda kafin su hadu ya daukesu cikin hannuwansa ya rungumesu sai sun girma Tunda ba kusa zai dawoba,

Labarin cikin Zainab ya samu Haj maryamah da umma Amma har lokacin Babu Wanda ya iya daukar kirantaba.

Komai na alaqarta da Yar uwarta Haj maryamah da umma yagama lalacewa sbd sun tabbatar Mata da Basu ba ita din har abada kamar yanda suka Bata zabi.

Cikinta yakai wata bakwai ta zama wata yar lukuta da ita,

Babu kalar kulawa da tattalinda Bata samu daga malam Sanda da Aqeel Wanda kejin kamar ya Ciro babyn dake cikin ya ganta kafin ya tafi Amma ba Hali Dan haka saidai yake kulawa da Mamin tasa kadai.

Ba qananun kudi yake kashewa Mamin ba da Kuma kayan baby komai order yakeyi online yasiyo yakawowa Mamin wadda takejin kamar ma Aqeel din yafita zakwadin babyn.

Haj maryamah dakeda bayanin komai daga PA dinta akan yanda Aqeel ke kashewa babyn da Zainab zata Haifa kudi ranta ya sake baci takirasa tayi Masa tas karshe hadda umma saida taji zancen ita Kuma takira Zainab din da rabon dasuyi magana tun aurenta Amma yau da kanta takirata tayi Mata kaca kaca da fada har saida baiwar Allah tayita kuka karshe duka abinda Aqeel yabata tace ya maida inda ya siyo ya karbo kudadensa.

Bai karba ba Kuma ransa ya sosu matuqa da abinda itama Mamin tayi Masa Dan haka kwana biyu saiya dauke Kansa ga kowa ya maida hankali kan tafiyarsa da batafi sati biyu ba.

Kwana biyu da baya zuwa gidan sai itama Bata nemesa ba sbd malam Sanda dake fama da ciwon ciki Dana Kai a kwanakin sosai shiyasama koda akai rigimar harma da Kiran da umma tayi Mata tana fada duk bai iya saka bakiba sbd sosai ciwon cikin ke damunsa ko bacci baya samu sosai a kwanakin.

Aqeel baisan da halinda suke ciki ba Dan sbd shima tafiyarsa tazo ga Haj maryamah tadawo sbd tafiya tasa Dan haka ya maida hankali sosai gurin shiryawa da mahaifiyarsa,

Bayason ya tafi Tana Mai fushi dashi Dan haka ya tattara lokacinsa gabaki daya ya Bata gashi itama Tana fama da nata rashin isashiyar lafiyar hawan jini ya sakota gaba

Jikin malam Sanda ya Dan tsananta Dan sunkai a kwance yake yanzu

Taso Kiran Aqeel yazo sukai malam din asibiti saiga Kiran umma kamar tasani ta gargadeta akan kada ta sake Shiga tsakanin maryamah da ‘danta tabari su rabu lafiya cikin kauna da kulawa Tunda Aqeel din tafiya zaiyi yabarta.

Jin Yana tareda mahaifiyarsa sunata daidatawa da begen juna kafin ya wuce yasa ta fasa nemansa ta kame kanta Dan gudun sabuwar matsala Tunda ansamu sun daidata din.

Itada malam din sukaje asibiti yaga likita Amma Basu samu wani cikakkiyar bayani akan abinda yake damunsa ba andai rubuta musu test da hoto harma da wasu Yan magani tukuna kafin result din yafuto.

A hanya suka siyo maganin suka dawo gida daqyar yasha ruwan zafi da abinci kadan yasha maganin yayi sallah ya kwanta.

Sai data ga bacci ya daukesa tukuna ta fito tayi alwala jiki a mace tayi sallar la’asar Dan tun safe suna asibitin suna fama sai qarfe uku suka baro.

Itama abincin taci kadan sbd Jin duk batajin dadin jikinta da yayi sanyi da ciwon nasa Dan abune da Bata taba ganiba.

Da daddare jikinsa ya matsa sosai Allah yasa Basu kwantaba Dan haka ta rasa yanda zatai Dole takira Aqeel suna gaisawa cikin kewar juna taji Yana tareda mahaifiyarsa Dan haka saita fasa fada Masa kawai sukai sallama ta kashe ta ajiye wayar.

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button