Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 8 Hausa Novel

Sponsored links

Throughout the day’s lecture mood din Nihad was so dull, gaba daya she wasn’t her self, Husnah tace “Nihad mu je mu ci abinci ni dai na fara jin yunwa” A takaice tace “I am not hungry” Husnah tace “C’mon babe, wai me ke faruwa ne? Gaba daya you look dull today, don Allah ki gaya min me ke faruwa” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Wai har ni mutumin nan xai ma walakanci ya ajiye ma makulli ya wuce Husnah?” Husnah ta ja wani dogon tsaki tace “Ohh this? Wai wannan ne ya canxa maki mood throughout? Lallai ma, To wai meye abun damuwa, kika sani ko barin aikin ma yayi?

Ni na fi tunani ya ajiye aikin ne, ba gashi da kika tambayesa wa ya bar ma motar yace maki masu shi ba, probably yayi quitting ne” Nihad dake ta kallonta tace “Sai ya rasa wanda xai ajiye ma aiki sai ni, me yasa bai kai ma Abba makullin ba, salon ayi xaton ni ce na koresa? dama babu wanda ke considering dina a gidan banda Umma, kawai so yake ya kara ja min bakin jini wajen Mumy” Husnah ta ja tsaki tace “Soo what? Idan ma ajiye aikin yayi ai hakan ke kika fi so, abinda kike ta so ne ya faru fa, karkari su gama surutunsu na kwana biyu su yi shiru, sannan a samo wani driver din wanda xa ki juya yanda kike so, ba shikenan ba?” Nihad ta taɓe baki ta mike tana harhada material din karatunta tace “Xan tafi gida” Husnah tace “Gida kuma? Da wuri haka? Ke da nace maki xa mu je guest inn din su Bill yanxu, Kai Nihad yau da kike da full control din mota an bar maki kiyi yanda kika ga dama shine xa ki wuce gida da wuri, haba yan mata, ki bari wajajen six ki koma gidan mana” Nihad tace “Ni kawai gida xan tafi duk raina a bace yake” Husnah ta juya ido tace “Toh ai shkkn, bari in raka ki gun motar” Tare suka isa inda motar yake, Nihad ta ajiye jakanta da kayan karatunta a bayan motar, sannan ta zaga ta shiga driver seat, Husnah na tsaye har ta tada motar ta fara tafiya….

 

Nihad na isa gate din gidansu tayi horn, mai gadi ya fito da sauri ya bude gate din, ta shiga gidan tayi parking, sannan ta kashe motar ta sauka, kallon inda mai gadin yake tayi, ta ga shi kadai ne a wajen, ta nufi cikin gida ba tare da ta dau material din makarantar ta dake bayan mota ba, Mumy na xaune parlor da Nihal, sai Umma dake parlon ita ma duk suna kallo, ta gaida su xata wuce, Mumy tace “Bani makullin da kika amsa wajen driver daxu” Tsayawa tayi cike da mamaki tana kallon Mumy tace “Mumy wa yace ni na amsa makullin?” Umma tace “Atoh, nima dai nace baxa kiyi haka ba, amma shi algungumin yace kin amshi makulli, kuma sun yarda” Nihad tayi narai narai da ido tace “A yaushe na amshi makulli wajensa? Wllh Umma sharri yayi min” Mumy tace “Ban tambayeki ba’asi ba, makulli nace kawai ki bani, xa kuma mu hade a daki” Nihad ta fashe da kuka tace “Ni wllh Allah ya isa wannan sharrin da yayi min, Allah ya isa tsakanina da shi munafuki kawai, ajiye min makullin fa kawai….”

Throw pillow Mumy ta dauke ta jefa mata tace “Tafi ki bani waje, ga ki nan munafuka, wllh tunda haka kika xaba xa mu sa kafar wando daya dake a gidan nan, kuma daga yau kika sake driving da kanki sai dai ki canza wata uwar bani ba” Umma tace “Wai ya kike haka ne Maryam? Shikenan kai da ɗan ka baxa ka ja sa jiki ba komai ya fada maka sai ka karyatasa baxa ka goyi bayansa ba, me yasa kike fiffita bare akan naki? Wannan wace irin rayuwa ce? Ki bar ta tayi bayani ma kin ki sbda rashin adalci” A fusace Mumy tace “Bana son bayaninta, wani bayani xata min sai kace bani na haifeta ba, ko kuma ban san halinta ba, wllh daga ni har ubanki babu me irin wannan mugun hali naki don ma kiji, in har kince ke sai dai ki tuka kanki to wllh ki nemi wata uwar, kuma ai kin saba cewa a baki makullin ba wnn ne karo na farko ba, don haka babu abinda xa ki gaya min in yarda” Kuka kawai Nihad take xuciyarta na suya, ta ajiye makullin motar nan saman kujera tace “Allah ya isa karyan da ya laka min, Allah ya isa tsakanina da shi…”

 

Tashi Mumy tayi, Nihad na ganin haka ta wuce sama da gudu, Mumy tace “Tsaya dai ki min rashin kunya” Mikewa Umma tayi ta fita daga parlon, tana fita compound ta kwalo ma Aminu kira ya taho da sauri, tace “Ina dreban nan yake?” Mai gadi yace “Ya fita ya ɗan amso abu” Tace “Toh xai dawo ya sameni” Daga haka ta juya fuu ta koma ciki. Nihad na shiga dakinta ta sa makulli ta dinga rusa kuka ta dau wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing ya daga yace “Hello Dear, ina meeting i will get back to you” Ta fashe da kuka tace “Abba ni dai kawai a canza driver din nan, bana son ganinsa kuma, i can’t withstand the sight of him any longer, kawai ni dai Abba ka sallamesa” Abba ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Why did u ask him to hand over the key to you da ya kai ki makaranta?” Nihad ta xaro ido tace “Abba wllh sharri ya min, ta yaya xan ce ya bani makulli, wllh karya yake min ni ban ce masa haka ba” Abba yace “Idan na dawo gida xa mu yi magana yanxu muna meeting ne” Daga haka ya katse wayar, kuka ta dinga yi, nobody is getting her banda Umma, wato dawowa gida yayi ya laka mata wannan uban sharrin gashi kowa ya yarda, number Farooq tayi dialing, yana dagawa shi ma ta rushe masa da kuka yace “Lafiya??” Cikin kuka tace “Yaya dama Abba ne ya dau wani sabon driver, yaya tun da ya fara aiki yake laka min sharri iri iri, yana sa Mumy na kara tsanata, wai daxu ya kai ni schl shine ya ajiye min makulli yayi wucewarsa, da ya dawo gida shine ya je yace ma su Abba da Mumy ni nace ya ajiye min makullin” Farooq yace “To ai halinki ne wannan, amsan makulli a wajen drivers kiyi driving da kanki, ke ko wani driver sai kin samu matsala da shi, haka Habibu farkon da ya fara aiki a gidan nan, why are u always having issues with everybody? Me yasa ita Nihal bata ce an mata ba” Lkci daya ta hade rai, yace “Shi wannan din yaushe ya fara aiki har kika fara samun matsala da shi Nihad?” Kin cewa komai tayi, yace “Ki min magana ko in kashe wayata” Murya can ciki ciki tace “Sallah xan yi” Katse wayar yayi, ta jefar da nata wayar, wato nobody is even supporting her, then xata dau action da kanta. Tana kwance bayan tayi wanka tayi sallah wayarta ya fara ring, ta jawo wayar ganin number da ke kiranta ta mike zaune ta daga tana wara ido tace “Shine baka ce min xaka dawo ba bayan ko jiya mun yi magana” Yace “How are you?” Ta lumshe ido tace “I am fine, ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, yaushe za mu hadu? I will be leaving for Abuja next tomorrow” Tace “Wai yau kake nufi xa mu hadu?” Yace “Toh shikenan tunda ba yau ba” Da sauri tace “Noo ba haka nake nufi ba, i only asked, okay yanxu xan shirya in fito in sha Allah” Yace “Where are we meeting?”

 

 

Nihad na shesshekan kuka tace “Wllh shi inna, kawai an bar sa yana ta abinda ya ga dama a gidan kamar gidan ubansa, duk ya gama rena ni, ko gaisuwa bata hadani da shi” Inna tace “Duk ba wannan ba, yanxu kin kira Aliyun??” Nihad ta daura kanta gefen gadon inna hawaye na sauka idonta tace “Bayan ya ki dagawa” Inna ta dauko wayarta ta mika mata tace “Kirasa da nawa” Nihad tace “Ae idan ba shi da numberka baxa ka iya samunsa ba, ya sa layinsa a Private” Inna tace “Wai ko ba dai Aliyu ɗ’an wajen janaral Habubakar jikamshi ba?” A hankali Nihad tace “Shi…” Inna tace “To wannan dreba duk yanda aka yi tsinanne ne, ko don nace masa ya saki jikinsa yasa ya sake kamar gidan ubansa? to ai ni na xata yaron arxiki ne” Salati inna ta saki tayi tagumi tace “Yau naga dreban jaraba, ashe duk ni na ja komai da nace ya saki jikinsa, to a kira min Ibrahim din tun yamma bai yi ba ya sallamesa” Nihad ta dau wayar inna da sauri ta fara neman number Abba tayi dialing, Inna ta bude baki ta rike ha6a tace “To shi kuma Aliyun banda abunsa garin yaya xai ce sai yayi ma dreba magana mutumin da ba ajinsa ba, ai abinda bai sani ba talakawan nan haka suke da dacin rai kamar mutum ne ya doro masu talaucin, ina shi ina wani basamuden buzun dreba can?

To ko a almajiri dai baxa su yarda su ajiye wannan mutumi a gidansu ba balle dreba, su da tun daga titin da ya yanka unguwarsu xaka fara ganin dirka dirkan sojoji har da motocinsu….” Nihad ta turo baki tace “Abba bai daga ba” Inna tace “Ina xai daga, ya tashi ya kawo wani kato gansameme kamar mutanen farko ya dau mota ya basa, ni wllh ranan da na fara ganinsa sai da na tsure, sai fa ya daga mutum ya nanasa da kasa sau biyar bai gaji ba, irinsu ai gadin dogon banki ya kamata a basu ba wai motar mutane ba” Nihad dai tayi tagumi don abinda ya dameta daban, ita yanxu ta ya xata fara shawo kan Aliyu, da yaya ma suka dawo soyayyar, Inna tace “To ko kin san inda ya sauka ki rakani mu je in basa hakuri” Nihad ta kalleta tace “Ji ki kuma, kawai don ki ja min raini?” Inna tace “Wani raini mutumi na nema ya kubuce, wa ke ta wani raini Nihad, idan ma baxa ki shiga ba ni ki rakani ki nuna min hanya in je in samesa” Nihad tace “Aa ke dai kawai duk yanda xa kiyi kiyi Abba ya kori driver din nan kawai” Inna tace “Yo sai ma kin fada, abu har ya kai yana korar ma jikokina samari”

Hamid ne ya bude kofar dakin ya shiga yana kallon Nihad yace “Ke don uwarki ni sa’anki ne xaki wuce ni da abokina baki gaishemu ba” Nihad ta turo baki ta koma gefen Inna, Inna dai bata ce komai ba, Yace “Mahaukaciya kawai, uban wa xaki dinga daga ma kai?” A fusace Nihad tace “Kina dai gani babu abinda na masa ya xo ya fara xagina ko inna, ni fa shi yasa bana son xuwa gidan nan wllh, kowa yaje yaji da mugun halinsa” Cikin xafin nama ya nufeta, Inna ta mike ta wangale hannu tana tare Nihad tace “Dokeni to, Hamidu nace ka dokeni” Huci yake yana kallonta, Inna tace “Ai dama ka saba dukan nawa yanxun ma ka duka, ranan da ka biyo Bilkisu ai ni ka jibga ba ita ba” Nihad ko kallonsa bata yarda ta sake yi ba, Yayi wani kwafa ya fice daga dakin, Inna ta kulle dakinta tace “Kinsan korosa aka yi daga can kasar wajen wai wa’adinsa ya kare a can, to kuma sai kayi ta hucewa kan ya yan mutane” Nihad bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba, Inna tace “Allah haka uban yace min, duk a booth din jirgi aka kwaso su aka dawo” Nihad dai bata ce komai ba, Inna tace “Yanxu ko kin boye number ki baxai daga wayar ba?” Nihad ta mike tace “Ni dai xan tafi inna dama anjima da daddare kice Hamid din ya kawoki nan gidanmu ki samu Abba da kanki” Inna tace “Toh shkkn ma, kawai bari inje in riskesa a gidan ba sai mun yi waya ba, idan ma ya kama ko shi sai ya kira Aliyun ya basa hakuri” Bude baki Nihad tayi, can ta kyabe bakin tace “Ni dai sai kin zo” Daga haka ta fita daga dakin, A bakin gate abokin Hamid ya tare ta da ya faki idon Hamid ya biyota, yana fara magana ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana yatsine fuska tace “Ina wasa da kai ne malam?” Daga haka ta ja tsaki tayi ficewarta daga gate din, ya bi ta da kallo baki bude, dama Hamid ya gaya masa ya ki ji. Nihad na komawa anguwansu ta yi ido hudu da Khalil dake xaune kan dakali a kofar gida wayarsa na kare kunnensa, yana ganinta bai sake cewa komai ba a wayar da yake kuma bai cire wayar a kunnensa ba, har ta isa dai dai inda yake, tayi masa wani harara ta ja tsaki ta shige cikin gida tayi banging gate din. Abba na tsaye balcony bayan magrib Khalil ya karaso da ladabi yana kallonsa yace “Gani Alhaji” Abba yace “Yauwa pharmacy xan aikeka ka siyo min magani yanxu” Khalil yace “Toh, ya sunan maganin?”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button