Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 13-14

Sponsored links

Yan Mata Kuwa Subhannallahi ana ta shiga dasu da manyan Alhazawa wasu ana sauke su a napep,wasu sunyi gayu suna zaga wajen masu so suna samu suna Shiga dasu ciki,sai zare Ido nakeyi Ina kallo.

Ina nan tsaye wani kamshi ya daki hancina Wanda ban taba Jin irinsa a duniya ba,kafin nayi motsi wani azababben matashi ya wuce ta gefena,Nawwar kenan hannunsa dauke da ledojin take away,wayarsa ce tayi Kara ya Fara lalubota ya zaro Wayar ya daga tare da shigewa cikin Hotel din, Wallet dinsa ce ta Fadi bai kula ba sabo da ga waya ga ledoji a hannunsa har ta Fadi bai sani ba,Ina kallo da sauri na karasa kanta na dauka tare da budewa ATM card ne kala sun Kai biyar a ciki sai wasu kudin Amurka dollars amma dake ni Yar Kauye ce ban San Mene ba sai na tabe baki nace aikin banza babu abin arziki a ciki ma bari na jira ko zai fito ya amshi abarsa,waje na samu nesa da wurin na zauna a jikin wata bishiya,shi Kam bai San ma ya jefar da wallet dinsa ba wanka yayi ya kwanta bacci abinsa,Ni Kam a jikin bishiyar bacci ya kwashe ni sai farkawa nayi Naga rana a kaina,tashi nayi da sauri na koma makarantar da masaukina yake Alwala nayi nayi Sallah wallet din tana wajena,itacen bishiya na balla na zauna na goge bakina tas na kuskure da ruwa,Fitowa nayi Ina dubawa har naje wajen da mutane suke sosai da manyan shaguna ga me kosai a wajen na siyo cikin kudin barata na jiya,na siyo bredi da shayina ba Madara aka zuba min a Leda na dawo makarantar na zauna naci na koshi, na sake shafa bakina a Fuska duk nayi Mata dabbara dabbara da bakin gawayi na saka yagaggun kayana na bara na fito rike da wallet a hannunta.

Ina tafiya Ina kalle kalle Ina zare idanuwa wani ne ya tare ni a hanya ganin Kamar ko zararriya ce ni,yace ke…a gabansa na tsaya Ina kalle kalle,gashina na sosa na kasa tsayawa kyam,kana ganinsa kaga kamili yace Ina Zaki je? nace ai Almajira ce ni,kai ya jinjina yace kina zuwa makaranta Kuwa? Murmushi na saki nace tab ai ni Jahila ce bani da ilimin komai yanzu ma littafi da karatu bazai Shiga kaina ba,galala ya kalleni yace kina so ki iya? da sauri nace ae,yace Okay da zaki iya zuwa dakina da na koya Miki dole sai karatu ya shigeki da yatsansa ya nuna kirjina yace idan bai shiga ta kanki ba dole zai shiga ta nan idan bai shiga ta nan ba to Dole zai shiga ta nan ya nuna gabana da yatsa,nace har ta nan karatu Yana shiga kaji karya,to Malam Iskanci aka ce ana yi da wajen,Kai baka sani ba Iskanci fa akeyi da wajen ba ruwana wajen Iskanci ne,na ja tsaki na juya nayi tafiya ta abina Ina masifa ya dauka bani da wayo zai taba min wajen Iskanci na Allah ya kiyaye.

Direct hotel din nan na koma ko zanga mutumin jiya gashi bazan ma ganeshi a Fuska ba sai dai ko idan naji kamshinsa na dade Banga alamar shi ba na bar wajen na tafi barata yau ma iya kudin abinci na tara, Wasa Wasa kullum Ina zuwa Hotel har da dare ban sake Jin me irin kamshinsa ba har na kwashe kwana biyar,shi Kuma Nawwar bai ma duba wallet dinsa bata nan ba,yau da dare na sake komawa nace wallahi daga yau Matukar ban ji me kamshinsa ba bani sake zuwa, ranar Kuma Nawwar ya nemi wallet dinsa ya rasa musamman atm card dinsa sune Suka dame shi, Fitowa yayi ko zai iya gani a cikin motarsa Nan ma ya gama dubawa babu, Fitowa yayi dake da duhu a wajen ko fuskarsa ban gane ba nidai naga hadadde ya wuce,Yana wucewa wani kamshi ya dakeni naji Kamar irin kamshin Wanda ya jefar da wallet dinsa jiya,Ina juyawa Naga ya Dan min nisa da karfi nace Malam….tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba da gudu na fyalla naci wawan birki a gabansa Ina haki na zaro wallet din tare da Mika Masa nace t…taka..ce? Yau sati guda kenan ka jefar da ita na ganta kullum sai nazo ko zan ganka,kasan irin hatsarin da na Shiga a hanya sabo da zan kawo maka abarka ai Saura kadan wani ya taba min wajen Iskancina,wai dan Allah karatu ai baya Shiga ta wajen,Nawwar bai gane me nake nufi ba ko saurarar zancen nawa baiyi ba, farin ciki ya Kama Nawwar cikin muryarsa me dadin saurare yace ta ya Kika ganeni? Nace kamshinka yasa kawai danni ko yanzu in za a kasheni bazan ce ga fuskarka ba sabo da duhu,karbar wallet din yayi Ina kallo ya duba komai nasa Yana ciki inda suke ya fito da dalolin masu yawa ya irga ko wacce dala dari dari ce a ciki ya zaro guda Uku yace gashi na gode

Baki na turo nace Hmmm uhm jam ni me zanci da wannan takardar ai gwara ka bani dari biyar,dariya ta kamashi yace kudine fa idan Kika canja sunfi dubu dari nace wallahi bana so kaji mutum dama can baka yi Niyyar kyautata min ba in hakane ka bani dubu daya mana,Nawwar ya buga buga nace wlh bana so,yace to jirani a nan Ina tsaye a wajen ya koma cikin hotel din sai gashi da kudi Yan dubu dubu ya Mika min Yace gashi dubu talatin Kika samu ba cash a hannuna da yawa,da sauri na karba nace Allah ya shi Albarka za kaga daidai a rayuwarka bukatunka sai sun biya da iznin Allah na juya na take da gudu,yace jita Kamar yarinya da bakar Fuska kamar bayan tukunya Kai wannan da baki take,ni kuwa ko gane fuskarsa banyi ba nasan dai fari ne sosai dan dogo haka ,baki ya tabe ya juya ya koma ciki Yana cewa Kai amma tana da Amana a Zamanin nan.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button