Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 43

Sponsored links

Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan hanashi komawa yay saboda dare ya ɗauka Iyyani da Ummu suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman inda zasu samo Babiy da Hanash.

 

Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne ɗan gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”.

 

Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin ɗan jimm alamar tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al’amari nada wuya, saboda bamu da tabbacin waɗan nan jami’ai daga wane station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin kamar mu nema gidan shi marigayi ɗin, tunda matarsa ita ta kawo jami’an tasan daga ina suke”.

 

“Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda gizo ke saƙar kai koka san ina gidan Dawood ɗin yake? Dan ni dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare da Muhammad Zayyan”.

 

 

“Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take, amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma, sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan ɗin yake zaune tunda ba wani huɗɗa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu Hanash ɗinne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na anguwa ya haɗa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara mu tafi can ɗin kawai rana ma nayi”.

 

 

 

Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da jikinsu ya ɗanyi sanyi ganin ƙofar gidan babu alamar anyi wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau uku. Ana huɗun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haƙuri nasan baka sammu ba. Muma dai munzo nan ɗinne neman wani bawan ALLAH daya zauna anan shekara kusan huɗu haka baya. Sunansa Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”.

masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”.

“ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban wuce shekara biyu da tarewa anan ɗin ba. Na kuma sayi gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”.

Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka wuce.

“Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan tambayesa ne ko zai faɗa mana inda zamu samu shi Ibrahim Askari ɗinne”.

Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da kai kenan. Kasan shi al’amari irin wannan yana buƙatar kasan dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waɗanda suka haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naɗi akan al’amarin”.

“Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauƙi shi zai iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo cikin sauƙi tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari’a ko kuwa?”.

“Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”.

“In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”…

Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen Ammarah akan ɗakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan dashi ya iso gareta. Taji matuƙar sanyi a ranta da farin ciki. Hadimar data kawo na fita ta buɗe akwatin ta shiga dubawa. Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da malam Fawzan ya bata ɗinnan itama tana a inda ta ɓoye ta. Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai ta ɗauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe kaf yinin har zuwa dare tana abu ɗaya. Da daddare bayan kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun Alkur’ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja mata ƙofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daɗi.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button