Hausa Novels and Stories

Idon Naira 22

Sponsored links

Duk da Maminsa ce bayajin zai tsaya boyon zancen dake ransa gameda shawarar tasa,

Qari Kuma Daman zuciyarsa Bata kwanta da barinta gidanba sai ga wannan lamarin daya faru harya sakata cikin damuwa,

Sosai ta canja a kwanakin kwata kwata ta sake kame kanta sosai ta maida kanta a matsayinta na ‘yar Aiki Mara gata ko mutuncin dayafi na Hakan,

Ta yarda cewan ‘dan wani Baya taba zama ‘danka duk da tanajin radadin raba kanta da tayi da Aqeel Amma Hakan shine kwanciyar hankali da mutuncin kowa duk da tasan bawa mutuncin take dashiba a gidan..

Tsakaninta dashi share Masa sashensa ta gyara takai Masa abincin ta jere saita komawarta cikin masu aikin gidan Yan uwanta.

Hakan Yana tsananin cizon ransa Dan hakama yake sake Jin nutsuwar shawartarta akan auren idan har zata aminta sbd rayuwarta ta inganta dan kuwa Allah bazai barsuba dagashi har mahaifiyarsa harma da umma Idan har suka Bari rayuwarta ta qare ahakan batareda sun Bata damar aure ta samu daidai iya nata farin cikinba.

Bai tuntubi Mamin da zancenba saida safe guraren 10 zuwa 11 haka Bayan tagama gyare koina na bangarensa zata fice ya fito daga bedroom dinsa sanye cikin casual wears qafafunsa sanyeda black footwears marasa nauyi na yawo cikin Palo da daki.

“Mami” Kai tsaye yakira sunanta Yana qarasowa tsakiyar palon inda ta tsaya tareda waiwayowa ahankali ta kellesa cikin yanayi na alamar akwai wani aikin ne?

Qarasowa yayi gabanta Yana kallon kyakkyawar fuskarta da sai yanzu yake ganin diban kamanninta da ummansa

Ahankali ya Kai hannunwan duka biyu ya kamo nata hannuwan Yana sake kallonta cikin kulawa da kauna irin ta uwa da ‘da yace”

Mami Ni meye nawa da laifin maganar umma zai shafeni?

Tafiya fa zanyi zuwa farkon nxt year

Idan kina shareni haka bazan iya tafiyar nanba gaskia.

Kallonsa tayi Jin yanda Yar shagwaba take cikin sautin muryarsa

Duk saiya tuna Mata lokacinda yake yaronsa…

Sanyi jikinta yayi duk da tanajinsa cikin ranta fiyeda kowa Amma kuma kusancin nasu Yana neman zama damuwa ga kowa Dan haka har cikin ranta ta dangana zata danne zuciyarta akansa bawai Dan Bata son ‘dan nata ba sai Dan mahaifiyarsa dake ganin kamar ta rabata da danta data Haifa abinda.

Janta yayi ahankali ya zaunar kan kujera cikin kulawa tareda zaunawa gefenta hannunta daya yasake riqewa ya Dan sauke numfashi tareda nutsuwa ya kalleta.

Take tagane maganar dazaiyi Mai mahimmanci ce Dan haka ta dauke kallonta daga Kansa Tana sauraron abinda zai fada

Duk da tasan Hakan ba lallai Abu Mai yiyuwa bane saidai kuma yanda Aqeel din ya tattara nutsuwarsa akan maganar yasata kasa cewa komai.

Tabbas da tanada ikon kanta a gidan dakuma gurin tafiya da tafiyarta zatayi sbd tasan fitinar da zaayi idan wannan zancen na Aqeel ya bayyana,..

Haj maryamah ba qaramin bacin rai zata shigaba Amma Kuma a yanzu da Aqeel din yake maganar tareda magiya sosai yasa takasa cewa komai bare ta musa masa,

Zamewa tayi ta tafi tabar Aqeel din Yana sake binta da magiya qarshe dai dakinta Takoma ta zauna tareda rafka taguma Tana tunanin abubuwa da Dama.

Shi Kansa malam Sanda din dayakeson aura Mata kamar yafi qarfinta sbd yanada rufin asirinsa,

Tsaftataccen malami kyakkyawan bafulatani Mai haiba shine zai bige da aurenta ita data Gama rasa kanta a mace,

Wahala da aikin wuta duk yagama dafar da fatarta ta rasa kyanta na mace,

Duk wani adon da mace ke buqata Babu daya data samu Bayan kitso wadda shima matar Maigadin gidan Dan majalisar dake kusa dasu itace take Mata wanda shima sbd tsaftar abincinsu yasa Haj maryamah ta lamunce Mata zuwa

Da gaggawa ta kori tunanin zancen Auren dayake neman shigarta sbd kaucewa fada da gorin da zatasha dagasu umma da Haj maryamah sbd zaa ce itace ta kitsawa Aqeel din zancen.

Tattara zuciyarta tayi guri daya ta dangana ta dauki qaddarar da Allah yariga ya qaddaro Mata Dan haka kwana biyu tayita kaucewa Aqeel kadaicewarsu sbd kada yasake tayar Mata da zancen Amma kamar a banza sbd Hakanan yanzu daya riga ya furta tareda qudurta zancen sai yakejin idan ba auren sukaiba hankalinsa bazai kwantaba….

Ganin Mamin tasa batada niyar amincewa hankalinsa ya tashi sosai ya dage tareda hanata sukuni da magiyarsa Wanda yasata shiga mamaki da tsoron ganin yanda ya qwallafawa ransa maganar auren Dan harkomawa yayi kamar zai zauna yayi Mata kuka Dan kuwa har cikin tsakiyar ransa yakejin so da buqatan auren nata da Malam Sanda.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button