Hausa Novels and Stories

Idon Naira 23

Sponsored links

Batada zabi ko qwarin gwiwar hanawa Aqeel dinta abinda yakeso Dan haka ta amince Bayan tashiga tsoro da fargaban abinda zai biyo baya sosai.

Kafin ta amince sharadin sai idan mahaifiyarsa ta amince tukuna zatai auren idan Haj maryamah Bata amince bazataiba.

Baibi takan shawartar Haj maryamah ba Kai tsaye yayiwa malam Sanda tayin auren Mamin tasa tareda rokonsa akan amincewarsa bawai Dan komaiba sai Dan kamar Yana rokonsa ne ya zama gatan Maminsa alokacinda baya Nan.

Malam Sanda yasa Aqeel matashi ne Mai nutsuwa da hangen nesa tareda tunani na masu ilimi Dan haka baiyi wani dogon Jan lokaciba yace idan Zainab din ta Aminta da aurensa shikenan Allah yabasu hakuri da zaman lafiya.

Take ya sanar masa ta Aminta Dan haka a washe gari ya karbi sadakin Maminsa a hannun baba Malam Sanda ya shigo dasu sai alokacin ya tunkari Haj maryamah da zancen sbd kamar aikin Gama ya riga ya Gama

Dan Idan ba Hakan yayiba tun farko ya tunkareta bazata aminceba da wuri zatai watsi da zancen.

Malam Sanda kuwa da baisan cewar Zainab din qanwar Haj maryamah bace baiyi tunanin Zainab nada dangiba Dan kuwa Dama kusan kowa sanin marainiya Mai Aiki ake Mata wadda aka dauko tun Tana yarinya har girman yanzu shiyasa ma ya amince da auren Dan shima ya bada tasa gudunmawar gurin inganta rayuwarta.

Kudin sadakin Zainab da Aqeel din yake nuna Mata take kallon agabanta zuciyarta na neman toshewa da rashin iska na zallan mamaki da firgici.

Maida kallonta tayi kan Aqeel ahankali Tana nazarin yanda yariga yayi nisa aduk wani lamarin daya shafi Zainab baya shakkar kowa bare tsoron bacin ranta

To meye amfanin samuna da zancen yanzu Bayan kun riga kunyi shawara har Kai ubanta ka karba sadakinta.

Dan rintse idanuwa yayi ahankali Yana sauke Kai daga kallonta Dan a kala manta Yana iya jiyo tsananin fushinta da bacin ranta.

Kasa cewa komai tayi ta miqe ta shige bedroom dinta tabarsa a palon sbd wani tiriri da zafi zuciyarta ta dauka.

Sbd yanda ranta yayi tsananin baci daga shi har Zainab Babu Wanda takuma magana dashi ta dauki fushi Sosai.

Zainab kuwa batasan meyake faruwa ba Dan batamasan cewa harya karba sadakinba.

A bangaren Aqeel kuwa ganin yanda Haj maryamah tadauki zafi matuqa akan zancen yasashi sanarda Baba malam Sanda a daura auren zuwa jumaa Tunda saura kwana biyar juma’ar tayi.

Sai alokacin ya sanarda Mamin tasa yakuma Bata sadakinta a hannunta.

Shiru tayi tsawon mintuna tareda shiga tunani kafin ta tambayasa Haj maryamah Bata kirata tayi Mata maganar ba Bayan Dole saida izininsu da saka hannunsu zaayi duk wani lamarin.

Haka ya share zancenta Dan yasan Maminsa bazata amincewa aurenba kamar yanda yasan bazata taba aurar da ita dinba

Shikuwa bazai iya barin rayuwarta ta qare a Hakan ba tinda ba baiwarsu bace itama uwarsa ce,

Idan a baya batada gata ayanzu daya San Kansa shine zai zama gatanta daga Nan har lokacinda zai bar duniya inshallah.

Hankalin Haj maryamah bai Gama tashina da tsananin bacin rai saida Malam Sanda da Kansa yayi magana da ita ya sanar Mata yanda sukai da Aqeel tareda Bata tabbacin jumaa zaa daura auren.

Kudi ya fidda ya ajiye Mata daidai qarfinsa akan asiyawa Zainab din sitira.

Haj maryamah harsuka Gama magana ya tafi batasan haqiqanin me take cewaba Dan kuwa Aqeel yagama kasheta da mamaki wato har dangin mahaifinsa yasa malam Sanda yayi magana dasu akan auren Zainab din acan akai neman aure na manya aka sake bawa Aqeel qwarin gwiwar wannan aikin alkhairin daya hada tareda saka Masa albarka.

Kasa danne tsananin bacin ranta tai Dan bazata iyaba,

Duk wani rashin mahimmancinta ga danta ya nunawa duniya Tunda ya yanke wanan hukuncin shi kadai ya zartar.

Umma takira Tana hawayen qunci ta sanar Mata komai Tana jaddada laifin akan Zainab da zata iya yarda da buqatar Aqeel ta aure batareda saninsu ba.

Kenan duk kokarin dasukeyi akanta Bata ganiba shine ta zabi ‘dan da aka Haifa a gabanta ya aurar da ita ga tafaffen malaminsa da baa San asalinsaba,baasan danginsaba baida kowa.

Wannan karon ummar da kanta ta Kira Zainab tayi Mata fadanda Bata taba yimata irinsaba…

Sai alokacin Zainab tasan da basusan da zancenba ashe

Hankalinta tashi yayi da fadan umma Dan kuwa maganganu marasa dadi da raunana zuciya ta fada Mata Wanda yasata kuka sosai.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button