Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai Book 2 15

Sponsored links

Jamcy dariya take wato Sabreen ce me kwankwason Lion Zaki kullum sai Santana ya Mata gorin shaye shaye,Yana gama girkin ya kalleta yace to Yar kwaya a tayani kwashe abincin,Jamcy tace ni bana son sunan nan gaskiya yar kwaya fa,idan kinyi zuciya ki daina,ai na daina ka bini a hankali yace better dakko muje muci kizo ki goyani,kana namijin Ina Zan iya,yace yau wlh sai kin daukeni gaki nan katuwa ni Ina Naga nauyi,Jamcy tace hmmm Kawai a ranta tace Ina ganin kaddara a nan.

Suna gama cin abincin ta mike tace to Zo na daukeka,Santana yaje ya dane Jamcy dama gata katuwa sai data iya daukan Santana sabo da rashin kibarsa,dalaf ta dauki Santana harda juyi da shi,yace Amma kin taba aiki a gona ko? Jamcy tace Kai karfi ne dani,yace harda karfin kwaya ma gaskiya,dariya tayi tare da ajiye Santana,sake daukan Santana tayi tana nishi,Sabreen ce ta shigo dauke da sallama,Baki ta saki me Zan gani haka? Santana ya karasa Mata Namiji da suna Hajara ko,soyayya ake ke tunda kin kasa,ke Yar nan rufawa kanki asiri ki samu Wanda zaiwa local government dinki aiki,Kinga ki kiyayi kwayar nan baza kizo ki maida matata ruwa ba gashi na samo kanta har goyani take karki zo ki dinga dagula min iyali ato,Sabreen dariya ma ya bata Zama tayi ta ajiye Jakarta a gefe Santana yace gata nan kuyi Hira Amanatun Amana wallahi idan Kika bata kayan maye yau sai kinci dan banzan duka a gidan Nan,Sabreen tana kallon ikon Allah ta saki baki.

Suna gama cin abincin ta mike tace to Zo na daukeka,Santana yaje ya dane Jamcy dama gata katuwa sai data iya daukan Santana sabo da rashin kibarsa,dalaf ta dauki Santana harda juyi da shi,yace Amma kin taba aiki a gona ko? Jamcy tace Kai karfi ne dani,yace harda karfin kwaya ma gaskiya,dariya tayi tare da ajiye Santana,sake daukan Santana tayi tana nishi,Sabreen ce ta shigo dauke da sallama,Baki ta saki me Zan gani haka? Santana ya karasa Mata Namiji da suna Hajara ko,soyayya ake ke tunda kin kasa,ke Yar nan rufawa kanki asiri ki samu Wanda zaiwa local government dinki aiki,Kinga ki kiyayi kwayar nan baza kizo ki maida matata ruwa ba gashi na samo kanta har goyani take karki zo ki dinga dagula min iyali ato,Sabreen dariya ma ya bata Zama tayi ta ajiye Jakarta a gefe Santana yace gata nan kuyi Hira Amanatun Amana wallahi idan Kika bata kayan maye yau sai kinci dan banzan duka a gidan Nan,Sabreen tana kallon ikon Allah ta saki baki

Wise ce taje da sassafe part din Iyamami zata gaisheta sabo da ta hanata zaman lafiya duk da tana zuwa gaisheta gwara ta sake dagewa ko zata samu ta kyaleta ta zauna lafiya,ta sameta a Palo Baffa Yana gefenta shima Papa Yana zaune,Wise ta durkusa tace Ina Kwana Iyamami,kallonta Kawai tsohuwar tayi tana tabe baki tace yau Kuma kinibibi ne ya tashi wato sai da Kika ga Ina tare da yarana Kika Zo gaisheni sabo da suce kina da biyayya ke ta gari ce,Baffa yaji ba dadi Iyamami taki shiryuwa yanzu abin ya koma Kan Wise,tashi yayi ya bar part din ma Sabo da takaici,Shima Papa yaji haushin irin wulakancin da Iyamami ke wa matarsa tashi yayi kawai ya bar palon,Wise tana tsugune tace Dan Allah Iyamami idan wani Abu na Miki ki yafe min mu zauna lafiya…da wa Zaki zauna lafiyar? Karuwa ballagaza,na taba ganin marar tarbiyya irinki kinzo kin makale Mana a gida sabo da Kinga arziki ko? to abinda Kika Zo samu baza ki samu ba Karuwar banza Karuwar wofi,fasika,Wise ranta ya baci tace Ina ganin girmanki amma ki gyara kalamanki ni ba karuwa bace yanzu ba Kuma fasika bace aure nakeyi nan Kuma gidan mijina ne karki ga nazo Ina Baki mutunci kice Zaki takani wallahi bazai yuwu ba never ai ba aurenki nake ba Kuma ba zamanki nake Yi ba,sabo da kin samu ma na gaida ki sabo da fa mahaifiyar Mijina ce ke kema idan da Kara ai Mahaifiyata ce ….wani ihu Iyamami tayi ta dafe kirji tace ni na Zama uwarki Allah ya kiyaye ban haifi karuwa ba Kuma ki sani bana sonki tare da dana sannan bari kiji tunda Baki San muhimmancin uwa ba,Baki San zafin haihuwa ba dole ki fada min abinda kika ga dama sannan mu zuba ni dake Zan fito Miki da asalin ya nake kin daina Jin dadin aurenki,Wise tayi Murmushi tace to shike nan Naga yanda za ayi ni Kuma na kasa Jin dadin mijina tunda Yana so na Ina sonsa Ina jiranki ta juya tayi tafiyarta.

Iyamami mikewa tayi ta bita har part dinta Wise bata sani ba ma tana shiga Papa yazo ya rungumeta ta kankame shi suna dariya tace murna nake Zan haihu,ai na fuki murna Zan sake samun yara Alhmdllh yayi kissing dinta suka sake rungume juna sai ga Iyamami ta shugo tana zuwa tsakiyarsu ta Shige tare da Jan hannun Papa tace muje Dana Ina son magana da Kai tana zuba Murmushi Kamar wata kishiyar Wise,Papa juyowa yayi hannunsa Yana cikin na Iyamami tana jansa Yana yiwa Wise signa akan tayi hakuri karta damu,ta bangaren Iyamami idan suka hada Ido sai ya washe Mata baki irin ba matsalar nan, sai da ta kaishi har bedroom sannan tace yaushe zaka kaini gidan Nawwar ne papa bai San me Iyamami zata Yi ba yace yaushe kike so? tace gobe,Allah ya kaimu ya furta sannan taci gaba da takalo hira, Wai dan Kar ya kula Wise,Wise tana tsaye sororo a palo tace hmm mu a gaya Mana bariki mu da Muka fito daga can tunda baza ki ja girmanki ba Zaki gani wlh na gaji, Papa ne ya fito Iyamami tana gefensa ya zauna a kujera itama Iyamami ta zauna,Wise Dining ta koma ta zauna tare da juya musu baya ranta in yayi dubu to ya baci,Papa ya juya ya kalli Wise data juya baya ransa ya sake baci da halin mahaifiyarsa, Wise tashi tayi ta ebo shinkafa sai ta zuba mai da yaji tana ci abinta,Papa yace Ya Naga kin San mai da yaji? Wise tace kasan cikin nan da kayi min ne yanzu abinci sai da yaji Iyamami hankali tashe tace ciki? Papa hankalinsa ya tafi Kan matarsa, Suka rabu da Iyamami suna hirarsu,Wise tace ya fara motsi ma,farin ciki ya ishi Papa ya manta ma Iyamami na nan yana washe baki yace ke ki bari dan Allah? Sosai fa hmm baka ji ba da alama Dan kwallon kafa zamu haifa akwai Chinese, Iyamami ji take Kamar bakin ciki ya kasheta ta mike tsaye da Niyyar tafiya tace dama ka haukace ta juyar maka da kwakwalwa, Papa yace Dan Allah kiyi hakuri Iyamami ba yanda na iya halittar Allah ce so,Kauna abin ne ba a iya Masa komai dagiya ,Digiyar ubanka haka na baka tarbiyya mutumin banza,ke Kam kinyi asara karuwa tirrr ta juya ta fice,Wise tace bana son sunan nan da take kirana da shi Karuwa,Amma ai ba ita bace ni na San ba karuwa bace ke cewar Papa Yana lallashin Wise yace karki tashi hankalinki akan wannan kina da ciki Kar a samu matsala please,shike nan ya wuce ta furta sannan ta mike Suka koma bedroom Suka tsunduma cikin rayuwar aure.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button