Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 14

Sponsored links

_Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi…ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne👌haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw…..masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar🫶_

_*Free page zai ƙare a page 10…ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku na cigaba da karanta wannan labari , kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance… Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000…zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank…ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932…Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya…*_

“Girgiza kai kurum Sumayya tayi a zuciyar ta tana cewa ” To Sumayya ya kika iya? Dole kiyi haƙuri ki jure mawa duk wani tijara da cin mutunci , idan bakiyi haƙuri ba ya zakiyi ? Zaki bar Umman ki da yunwa ne ,kece kaɗai gare ta kece mai nemo mata dole . Yarinya wa kike nema ? Nan inda kike nufa ba hanyar Part ɗin Hajiya bane , Part ɗin Boss ne”. Juyowa Sumayya tayi tana kallon wacce take mata maganan Muryar na ba cikakkiyar bahaushiya ba. Ohk to Don Allah zaki iya kaini Sasan Hajiyan gidan?”. Eh ba damuwa taho muje! A sanyaya Sumayya ke bin Oruma tana tafe tana kallon ikon Allah komai na gidan abun burgewa ne , ga kyau da tsari , wata ƙofa ne ta buɗe tana ɗaga labulen mai laushin gaske , dark Blue Oruma tana kutsa kanta ciki tare da Sallama ,nan Sumayya itama ta shigo tana bin ta a baya… Kaman yanda Ta zube Gaban Hajiya Juwairiyya tana yin ƙasa da kanta kaman baiwa a gaban gjiyar ta yasa Sumayya cewa ” Barka da Rana Hajiya?’.

Ɗagowa tayi tana kallon Sumayya , wanda taji gaban ta ya faɗi daranmmm , sai ta kauda kanta tana kallon Oruma kana ta motsa bakin ta da kyar cike da izza tana cewa ” Oruma ina aikin dana saki? Kin ɗebo jiki kin dawo, kin san Gobe ne dawowar Su Fahad da Nurƙalby na ko?”. Cikin rawar murya Jidda Oruma tace ” Eh Hajiya na sani, na rakota ne na nuna mata nan Part ɗin ki. Shiru Hajiya Juwairiyya tayi kana tace ” Ok you are free to Go”

Miƙewa Oruma tayi tana fichewa cikin sauri tare da nufar inda hjy Juwairiyya ta umarci taje. Kusan mintuna biyu da fitar Jidda Oruma Hajiya Juwairiyya ta ɗari da idanun ta ,tana kallon Sumayya wanda anan ma Ita take kallo haɗa ido sukayi nan take taji wani Abu yayi circulating blood ɗin ta game da Sumayya ,fara magana tayi cikin Muryar mai ɗauke kamala tana cewa ” Ammm kaman na san ki?”.

Kallon ta Sumayya tayi kana ta ɗan girgiza kanta alamun a’a …ɗan caɓa baki Hjy Juwairiyya tayi kana ta miƙa hannun zuwa glasscup ɗin dake gaban ta tana kaiwa bakin ta …bayan tasha ruwan ne ta aje tana cewa ” Lyk i know this face in somewhere else”. So mah lady any thing you want from me?”. Aƙwai abun da kike buƙata?”.

A hankali Sumayya ta fara cewa ” Eh Hajiya nazo ne ki taimaka ki ɗauke Ni aiki gidan ki”. Aiki?? Kaman yaya kenan? No no it’s too late ,yanxu na daina ɗaukar ma’aikata Cox basu da amana , saboda ba ko wacce ma’akaciya ce Son ke buƙata ba , may b yace baki masa ba, Kuma ina da ma’aikata da yawa wanda bana buƙatar ko wacce ƴar aiki yanxu.

Wani irin ƙwalla ne ya ciko idon Sumayya cikin sauri tace ” ki taimekeni Hajiya , kona sati biyu ne ko ɗaya nayi maki aiki ki biyani ,Ni baƙuwa ce ban san kowa anan ba , kima Allah ki taimaka idan ya dawo yace baya buƙata na sai na tafi…..ta ƙare maganan hawaye na sauko mata sharrrr….. Ganin haka yasa Hajiya Juwairiyya cewa ” Ina ne gidan mahaifin ki?”.

Wani irin bugawa ƙirjin Sumayya yayi ,a hankali tace ‘ Abba na y rasu, daga Lagos muke ,bamu da kowa anan , dagani sai Umma na , kwatanta mata gidan da suke haya Sumayya tayi ,wanda nan Take Hajiya Juwairiyya ta gane gidan Hayan mlm sabo ne.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button