Hausa Novels and Stories

Idon Naira 27

Sponsored links

Rayuwar auren tasu farko yanayin yazo musu a Dan takure sbd nauyin juna da rashin sabo da rashin sanin juna ko kadan tun farko,

Ga kunya da nauyinsa dake tsananin dawainiya da Zainab sbd zamansa babba sosai gareta ya Isa haihuwarta sosai gashi kwata kwata basu San komai na raayi ko halayen juna ba.

Abu daya ne yafara sakawa zaman nasu dadi da kwanciyar hankali shine nutsuwa da biyayyar Zainab tareda taka tsantsan dan kaucewa laifi da Bata Masa Rai.

Da farko shi Kansa malam Sanda din ya dauka biyayyartace sai daga baya ya fahimci harda rashin sakewa da sabon datai da aikin bauta da biyayya batada raayin kanta kwata kwata sai Wanda akace tayi shiyasa anan din ma sai yazama kamar zaman bautar takeyi bana yanci da kwanciyar hankali ba, Dan haka yafara kokarin janta ajiki sosai tareda nuna Mata ba wannan zaman zasuyiba,

Zaman nutsuwa da kwanciyar hankali yakeso harma da kaunar juna.

Duk da Hakan dai Bata wani sakeba ta Sabu dashi saida sukai kusan wata uku zuwa na hudu tukuna tafara sakewa har Tana dariya da farin ciki a tareda mijin nata Wanda shikam har cikin tsakiyar zuciyarsa tuni ya kamu da so da kaunar matarsa sosai.

Zainab tasamu kyakkyawar rayuwa a hannun mijinta yanzu,

Batada abinda ta rasa face Yar uwarta da umma Wanda takewa kallon mahaifiya agareta

Har tsawon wannan lokacin su umman fushi sukeyi da ita Mai tsanani musamman Antynta Haj maryamah da kusan har lokacin Bata dawoba Tana gidan mijinta Abuja.

Kusan Babu ranarda Zainab Bata kiransu Amma basa daga wayarta

Amma takasa gajiya kullum sake Kira takeyi.

Aqeel yakoma gidan kakarsa Haj Kaka mahaifiyar Dadynsa Dan Sam baida raayin komawa Abuja gidan ummansa ya zauna acan

Dan haka ya zauna a gidan kakarsa kafin lokacin tafiyarsa dayake qaratowa.

Aqeel kusan Babu ranar da baya zuwa gidan Mamin tasa sbd anan suke karatu da baba malam din nasa yanzu Dan haka kusan abincin darensa a gidan yakeci kwata kwata

Har na Rana ma wataran duk anan yakeci sbd sabo da abincin Mamin.

Babban abinda yake taqaita damuwar Zainab akan Yar uwarta da umma shine Aqeel daya cike Mata gurbinsu ya hanata Shiga damuwarsu sosai duk da abin na cikin ranta takasa cirewa sbd fushinsu akanta Tana ganin illarsa Tunda dukkaninsu iyayenta ne.

Shi Kansa Aqeel yasan fushi sun umman sukeyi dashi sosai musamman ummansa Dan haka yake kwantarwa da Maminsa hankali akan komai zai wuce.

*****Lokaci ya Dan ja tun daga kwanaki har satittika da watanni,

Zainab ta sauya sosai kamar ba itaba,

Tayi kyan gani matuka tareda samun kwanciyar hankali da nutsuwa harma da Jin dadi daidai gwargwado duk da kusan komai na malam din yadan tsaya sbd manyan dayakewa karatu acan gidajensu basa iya zuwa gidansa sai kawai da yawansu suka sauya malamai da Wainda zasu ringa zuwa gida suyi musu karatun shikuma daga Hakan kusan duk jamaarsa suka tafi sai yakoma yanzu Bayan Aqeel da wasu Yan tsirarraku Babu masu daukan karatu agurinsa.

Zainab tayi jiki sosai tayi fresh abinta Dan yanzu duk sati take kitso

Lalle ma duk bayan sati uku ko hudu takeyi sai Takoma kamar wata Yar budurwa sabon tashe gashi Daman kyakkyawan ce nutsuwa da gyara ne Bata samuba da kwanciyar hankali.

Bata taba saka ran zuciyarta zata San wani so da soyayyaba sai yanzu data samu abokin rayuwarta mijinta abin alfaharinta malam Umar sanda.,

Soyayyarsu suke Mai dadi da kwanciyar hankali tareda tattali Dan kuwa tattalin dayake Mata yasa aduk lokacinda ta kallesa mahaifinta take tunawa Dan kuwa su biyun Hadi da ‘danta Aqeel sune kadai masu tsananin so da kaunarta da kulawa da ita,

Ta rasa mahaifinta Amma tanada su biyun a yanzu

Tana Kuma fatar su dore a Hakan har lokacinda mutuwa zata rabasu.

A yanzu datake cikin wannan rayuwar ta yanci burinta daya ne taga tafiyar Aqeel karatu sbd kusan ayanzu tafi haj Maryamah son tafiyar tasa Dan haka kullum cikin tambayarsa tafiyar tasa take.

Shi Kansa yanzu tafiyar yafiso fiyeda komai sbd yasamu Maminsa yanzu Tana hannu na gari Dan haka yasan koda ya tafi hankalinsa a kwance yake da inda yasan yabarta zai dawo ya sameta.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button