Hausa Novels and Stories

Furar Danko Page 2 Hausa Novel

Sponsored links

Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shine kasancewa da namiji. Ko kai ɗan uban waye a kuɗi ko nasabar zuri’a baka ishi Lulu ƙamshi kallo ba, dan ko turawan sun buga sun barta kam, hannunka ma yace zai yi gigin zuwa jikinta komai shigar rashin mutuncin da tai zata sauke maka kwando-kwandon masifarta. Ta dai yarda ta shiga club aci uban rawa ayi nishaɗi tai gaba. Sai sirrintaccen harkar da takeyi da har yanzu babu wanda ya sani a gidansu, dan tana aikatawa ne cikin taka tsantsan da kula, shiyyasa har yanzu babu wanda ya ganota duk da an ɗan taɓa samun akasi tsakaninta da Uncle Yousuf dai ya kusa harbota ta kuɓuta da ƙyar.

 

 

 

 

Wannan itace Mawaddat Isma’il Jiƙamshi (Lulu ƙamshi) a taƙaice.

 

 

 

Saurayin nan da suke tare tun daga cikin jirgin sauri yake na son cin mata, duk da yanda take takun nata cike da yauƙi da yanga. Wannan ita kaɗai ce damar data rage masa, gashi kuma tana neman kufce masa. Tunanin hakan babbar asarace a garesa ya sashi ɗaga murya wajen faɗin,

_“K! Sarauniyar mata. Son kowa ki dakata mana!!”._

Ɓuɗaɗɗiyar muryarsa da tsarin adon dake nuna shima ɗin wani shege ne ya saka mata da yawa tsayawa cak, sai kuma suka shiga juyawa suna kallonsa. Sai dai abin mamaki ita ko nuna lamar ma tasan yanai batai ba tafiyarta take. Ganin ya cigaba da ƙoƙarin cimmata ƴammatan da duk suka juya garesa suka shiga taɓe baki da yatsine fuska. Ko kallo basu ishesa ba sai ƙoƙarin cimmata da yake yi dai-dai tana ƙoƙarin isa ga inda motocin ɗaukar mutane keda hurumin tsayawa. Wani shegen kallo ta watsa masa fuskarta na sake tsukewa.

 

Fuska ya marairaice yana mai haɗe hannayensa waje guda alamar roƙo gareta, amma saita ja masa tsaki zata cigaba da tafiyarta. Sake shan gabanta yayi da faɗin, “Haba mana Babie ki saurareni koda akan abu ɗaya ne Please. Address ko phone number abeg you”.

 

Cike da yauƙi da yanga ta furta, “A matsayinka na wa?”.

 

Duk da yay mamakin jin hausa a bakinta sai ya shanye, cikin murmushi ya ce, “Neighbour naki a jirgi mana beauty!. Sunana MM Atik Kumo. Mahaifina M Atik Kumo sunane da duk wanda ya kwana ya tashi a Nigeria dama ƙasashen Africa ya sansh…..”

 

“Kai dalla can ka isheni da zance yannn-yannn!! kamar tsohuwar akorukura. Bani hanya kona wanke banzan face ɗin nan naka zubin alakoro da mari stupid”. Ta faɗa cikin katsesa da yarfi ta bi gefensa ta wuce. Tamkar gunkin da aka sassaƙa domin tarihi haka yay tsaye ƙiƙam yana kallonta, hakama duk wanda ke kusa da su sai da yay mutuwar tsaye akan abinda tayi. Dan kowa dai yasan wanene sunan MM Atik Kumo, amma yarinyar nan mai zubin yahudawa tai masa wannan yarfin. Kuma ko’a jikinta kamar yanda shima babu alamar zai ɗauki wani mataki…..

Laahhh *_Uncle Smart_* ga Aunty Lulu ɗin nan”.

 

Wani ɗan ƙyaƙyƙyawan yaro dake saman jibgegiyar mota baƙa siɗik ya faɗa yana nunata. Wanda ya kira Uncle Smart dake gefensa tsaye kansa a ƙasa da keypad waya ƙirar Nokia a hanunsa ya ɗago a hankali tamkar mai ciwon wuya.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button