Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 18

Sponsored links

Deen ko yana gefe yana kallonsu, zirgi zirga ya shigayi ya kasa zaune ya kasa tsaye, chan kuma sai ya zube a kasa yayi tagumi yana kallonsu with blank expression, a haka bazaka taba gane yanayin da yake ciki ba saidai shi kadai yasan me yakeji aransa, ashe dama abin tausayin ce ita shiyasa yakejin tausayinta sosai? And he has a lot of questions to ask her right now, sannan a labarinta tace daddy mutumin kirki ne amma bega alamun hakan ba, the fact is that koma menene zeyi finding out, wuyarta kawai ya fara bincike yasan da sannu ze gano komai……Sai ya sake daga kai yaga kuka suke har lokacin sai abun ya basa mamaki ya kuma rena karfin zuciyar mata, abu kadan sai su zauna suyita kuka?….

“Haba Umm ke baki dena kukan ba taya zata dena ita?”……

Cewar mami da har lokacin itama hawayenta be tsaya ba amma bata sani ba………

Dagowa Umm tayi tana share hawayenta tace;

“You’re also crying sis and I understand, I just can’t believe she went through a lot at this very young age?”…..

“Gaskiya kam, I am even speechless with lots of questions!”……..

Gyada kai Umm tayi ta dago Fatima zainab tashiga share mata hawaye, saida taga hawayen tsaya ya tsaye sannan tace;

“Sweetheart stop crying pls, komai tsanani maganinsa Allah, ki dauki hakan a matsayin jarabawar rayuwa kuma Allah be manta dake ba yana sane, you have a brighter future Insha Allah, worry not okay?”……

“Permit me to adopt you, I really want you to have a good life?”…….

Umm ta tambayi fatima zainab amma hankalinta na kan Deen da taga ya mike tsaye yana kallonta…

Shiru tayi bata bata amsa ba meanwhile bataso tayi adopting dinta dan daga gani takurawa rayuwarta zasuyi suyita mata kulle, ita kuma ta riga ta saba da freedom, tasan tsap zasu iya hanata shayeshaye musamman yanda Deen ke yawan ci mata mutunci akan hakan, kuma tasan ko sama da kasa zasu hade bazata iya dainawa ba……

“I mean yanzu a gurin Alhaji Ibrahim take, adopting her won’t be easy, dole sai komai yayi settling”……

 

“The last time I checked kai ka binciko Alhaji Ibrahim has bad intention towards her, toh akanme zata koma gidansa?”……

 

“Ba gidansa zata koma ba, aure zan mata very soon saboda shi kadai ze nitsar da ita!”…..,,,

 

Yana fadin haka ya sa kai ya fita daga parlourn da sauri dan yasan bazasu kare ta dadi ba…….

 

“Umm kinji shashasha ko? Tun yaushe ake binsa yayi aure yaki yayi amma yana da bakin cewa aure ne ze nitsar da ita kamar wani ubanta, toh sai ya mata auren mugani”……..

“Rabu dashi mami he’s not serious, in banda rashin hankali irin na saif antaba cewa zaayiwa mutum aure without someone on ground?”…..

“Inaga siyo mata mijin zeyi, ni yazo ma inji a wani stand yake, nace yaje gidansu eesha banajin yaje”…..

“Kai, Allah dai ya shirya, nidai yaya sai inga kamar gwara a barshi ya kawo wacce yakeso da kansa, kina gani wacce ya damu da lamarinta ma ba kyaleta yayi ba inaga wacce kwata kwata baya bi takanta, tsoro nake kar ayi aure ya dinga cutar musu da yarinya da wannan zafin zuciyar tasa”…..

“Kinfi kowa sanin halinsa Umm, I’m sure ko zaa bashi nan da ten years baze kawo wacce yakeso ba, toh haka zamuyi ta zuba masa ido ba aure?”……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button