Hausa Novels and Stories

Idon Naira 25

Sponsored links

Aqeel Tunda ta amince da auren hankalinsa ya kwanta Dan haka ko zama sosai ya rage Yi a gidan motarsa yake ja ya fice zuwa gidan kakarsa sai dare yake dawowa.

Haj maryamah da umma kuwa kyara sosai da fada Mai tsanani Koda yaushe suke rufe Zainab din dashi akan bazaayi aurenba Amma dai batacewa komai.

Har malam Sanda umma Haj maryamah sukai magana dashi akan ya janye Amma Kai tsaye ya sanar musu Tunda Zainab ta zabi aurensa bazai janyeba zai aureta insha Allah.

Ayanda yasan komai da komai na rayuwar Zainab tun haihuwa har girma zuwa yanzu bayajin zai iya kasa aurenta Koda kuwa zasuyi Mata Baki ne sbd maraicinta tallafi yake nema sosai…

Sun kashe rayuwar yarinya qarama tun daga quruciya harta girma ta wuce layin ya Mata sbd son Rai Dana zuciya da Wasa da haqqin maraya.

Tasani Tunda yace zai aura Zainab din bazai taba fasawaba matuqar ba Zainab din ce tace batasoba ta fasa.

Dan haka sai suka sake maida pressure din kan Zainab musamman umma wadda a fili take bayyanarda Dana sanin Rikon Zainab din dasukai har girmanta..

Ayanzu da Haj maryamah zatafi buqatarta shine ta nace da wannan auren na malaminda komaima baida sai Dan rufin asiri..

Idan Aqeel ya tafi Abuja taso komawa gurin mijinta tareda Zainab basai ta nema wasu masu aikinba sbd qyanqyaminta tafison Zainab din dai ta zama permanent Mai aikinta,

yanzu gashi ta yarda da wannan auren da Babu abinda zata samu agurin malam Sanda din Tunda dai ya manyanta har tsufa ma yafara.

Qarin takaici da kunya tasan kusan Aqeel dinne zai dauki dawainiyarsu.

Zainab dai zuciyarta tagama raunana da komaima na rayuwa Dan haka koyaushe sukai Mata fadan da zasuyi mata kuka takeyi ta hakura Bata iya cewa komai Dan ko bakinta Bata iya budewa tai magana sbd raunanar datai sosai da rayuwar.

Su Kuma wannan yanayin data shiga shine yake qara zurfafa bacin ransu sbd takasa fadar zata fasa auren ko bazata fasaba gashi a yanda Aqeel yasake fada saura kwana biyu auren..

Dan ma rigimar da akai tasa an daga auren ne da yanzu tayi sati kusan uku da auren.

Aqeel da Kansa yabada kudi a gurin qanwar Dadynsa tayowa Zainab dunkunan sabbin sitirar alfarma da Zainab din Bata taba sakawaba

Hatta takarma da hijabs harma da veils biyu da tirarika da Yan cosmetics duk an siya Mata kusan dai akwati uku aka cika matada duk kayan buqata shidai yabada kudin.

Malam Sanda ma ya Aiko Mata da atampa guda uku da hijabs manya guda biyu har qasa da takarmi daya sai tirare daya.

Umma dataga bazata iya kallar wannan lamarinba fushi tayi ta tafiyarta Koda Zainab din zata shiga damuwa ta fasa Amma harta Isa Babu wani labari.

Da Zainab din takira Dan yimata barka da Isa lafiya Tana dauka taji ba maganar fasa auren bace ko sauraron ya haryar datake Mata Bata gamaba ta kashe wayarta ta ajiye tana rasa yazataiwa Zainab din afasa wannan auren Dan baida wata doguwar alfanu gareta,

Me zatayi da tsoho tanada sauran kuruciyarta.

Haj maryamah ko fuskar Zainab din Bata buqatar gani Tunda dai tazama cikakkiyar butulu Dan haka karshema tattarawa tayi itama tayi tafiyarta Abuja bataredama Zainab din tasaniba Dan haka Koda aka daura auren ranar juma’a Zainab batada kowa sai Aqeel Wanda shine ya tsaya Mata aka daura auren.

Matar datake Mata kitso itace tashigo ta wanke Mata kan tayi Mata sabon kitso Mai kyau da lallen hausa

Dama ita ba qazama bace Dan Babu inda wani dogon gyara yake atareda ita Kuma Allah yasa dattijo ne Kuma malami zata aura Bata buqatar wani qyale qyale Dan batadama Mai Mata qyale qyalen.

Lallen da kitson ma Dan matar ta dage akan zatai matane shiyasa

Amma badan hakanba ko Mai matasu batashi.

Alokacinda aka daura aurenta Ita Zainab Adamu batada waliyyi dazai tsaya Mata ya bada aurenta sai ‘danta Aqeel Wanda aka Haifa agabanta..

Shine ya karbi sadakin aurenta daga malaminsa ya bada aurenta jamaa suka sheda aurenta da Malam Umar Sanda Wanda dagashi har ita Babu Mai dangi Amma shi Mai jamaa ne Dan haka aka Dan samu mutane sosai gurin taron daurin auren Wanda ko IV baa buga ba andaiyi sanarwa a masallacin anguwar.

Aqeel ne yasake ajiye Mata sadakinta gabanta tareda sanar da ita an daura auren.

Addua da fatar samun nasara da rayuwar farin ciki da kwanciyar hankali yayi Mata.

Wasu hawayen radadi da dacin zuciyane suka gangaro Mata Dan kuwa ayau ta sake tabbatarda batada kowa sai kanta,

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button