Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 1

Sponsored links

Wata tsohuwar Mata ce zaune a bakin bishiya, ta jingina bayanta a jikin bishiyar tana shafa sumar kan Yarinyar dake kwance saman cinyarta,

Yarinyar bazata wuce 20yrs ba, tana kwance kamar mai yin bacci taji uwar tana shesshekar kuka! A firgice ta tashi zaune tana fadin “Uma lafiya kuwa, meya faru dake?”

Cikin kuka Tsohuwar tace “Ayush inaso ki tayani neman gafarar ubangiji, na tafka babban kuskure a rayuwata, inaji ajiki na zan mutu, Ayush! Zan mutu ba tareda na nemi yafiyar Junaid ba”

Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai kashe zuciya

“Uma Dan Allah ki daina kukan nan banso, banso na rinka ganinki acikin wannan halin,

Shin wanene wannan JUNAID din? Sannan mai kika Aikata masa haka har kike fad’in munanan kalamai akanki saboda shi? Cikin zubda hawaye Ayush take fad’in “Uma idan baki furta mun abunda ke ranki ba taya Zan iya temaka miki da Addu’a bayan bansan laifin da kika Aikata ba”

Cikin takaici da cije la66e Umma take kallon Ayush wacce itama Ayush d’in kallon Umman take,

“Ayush! Na tsani kaina, kema idan kika ji labarina na tabbata zaki tsaneni ne, Zan gaya miki Amma kafin nan inaso ki yafe mun Dan Allah” tana kallon Ayush cikin tausayawa.

Da mamaki a fuskar Ayush cikin kasalalliyar murya tace “ni kuma Uma? Nasan bakiyi mun komai ba, duk abinda kikayi mun nasan aciki soyayya ne, bazaki iya cutar dani ba Mamana, saboda haka na yafe miki duniya da lahira”. Murmushin takaici Umma tayi murya a sha’ke tace “Ayush a yanzu rayuwata batada amfani, a shirye nake dana mutu, sai dai Ina mai tausaya miki idan na mutu bansan halin da zaki shiga ba, Ayushh banida en uwa banida kowa,mutane gudu na suke saboda ban aikata abu mai kyau ba, hakan yasa laifi na ya shafeki kowa kyamar mu yake,” kinga can👉 ta nuna wani ‘Dakin Kara sannan ta cigaba da cewa “nasan kinsan cewa nan ne ‘Dakin mu na kwana, tin kina jaririya muke wannan dajin! Kinsha tambayata cewa Ina BABANKI, SU WAYE EN UWANKI amma na kasa baki amsarki saboda kada ki gujeni, amma yanzu a shirye nake dana fuskanci duk wani ‘Kalubale”

Taja dogon numfashi murya Ciki-ciki tace “AYUSH

Cikin Sanyin murya ta amsa “Na’am Uma Ina sauraronki” fuskar nan duk ya jagalgale da hawaye ga yayi jawur abunka da farar mace.

Ta cigaba da cewa “Ina so naga kinyi Aure kin haihu, Ayush kina da kyakykyawar zuciya, kinada tausayi, Sam bana fatan ki d’auko kalar halina koda da qwayar zarrah, sannan banaso ki d’auko halin mahaifinki shima, tirrr da halayen mu” ta sake fashewa da wani sabon kukan mai cin rai!

Ayush itama kukan take ta rungumi Uma tana shafa bayanta rarrashinta take cikin kulawa, cikin sassanyar murya tace “Uma kibar mun wannan labarin indai zai Saki kuka, banson abunda zai sakaki kuka Umma nah Ina matukar kaunarki”

Umma ta raba jikinta dana Ayush tana sharar hawaye sannan tace ” a’a Ayush indai ban fitar da abunda ke raina ba, bazan samu nutsuwa ba,

Zan gaya miki ko ni wacece.

Da farko ni sunana *AGATHA* ni ba musulma bace, asalin er kasar Ghana ce ni, na rasa iyayena ta sanadiyar hatsarin motor, banida kowa bayan su saboda rashin zumuncin dake tsakaninsu da en uwansu hakan yasa basu ta6a gaya mun cewa inada en uwa ba, ni kuma ban damu da sanin hakan ba, ni dai nasan cewa mahaifina christal ne, mahaifiyata kuma musulma ce sai dai mahaifina ya rinjayeta zuwa chrital hakan yasa gava ta shiga tsakanin en uwan mahaifina da kuma mahaifiyata,

Sakamakon ba Wanda ya kula dani yasa na shiga harkar karuwanci ta hanyar nan nake ci da sha da kuma sutura a kaina,

Ina cikin wannan halin Allah ya had’ani da wani Attajirin Bawan Allah, ya fitar dani daga cikin wannan halin da nake ciki,

Ya taimake ni a rayuwa sannan ya kwad’aita mun musulunci, na musulunta ta sanadiyarsa, ya canza mun suna na koma *BARA’ATU* shi ‘Dan nan Nigeria ne kasuwanci ya kaishi kasar Ghana,

Nayi kusan shekara guda ina tare da shi amma ba wani abu daya ta6a shiga tsakanina dashi, nabi duk wasu hanyoyin dazan bi domin ya nemeni da lalata amma Sam yaki, ni kuma ina da munguwar sha’awa Gashi na kamu da matsanancin son sa,

Duk wani nauyi na akansa ya rataya shi yake mun komai hatta kudin da zan kashe shi yake ban,

Wata rana yana zaune yanata Lissafe-lissafensa na kudurta a raina cewa zan sanar masa cewa ina sonsa kuma zan Aure shi,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button