Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 67

Sponsored links

Wani irin mummunan bugun zuciya mai kaɗawa da tashin hankali da bai taɓa cin karo da shi ba a rayuwarsa yaji yana taso masa, amma yay jarumtar shanye komai ya zubamata idanunsa a dake. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, kamata yay ya zaunar a kujerar data taso, kafin shima ya kai zaune gefenta a hankali dan ji yake hajijiya na neman zubdashi ƙasa. Amma kasancewarsa gwanin kamewa ko’a fuska bazaka taɓa tantance komai da ga garesa ba.

 

 

 

……..Ruwan da ke ajiye kan table ɗin cikin jug ya ɗauka ya tsiyaya, cike da kulawa ya miƙa mata yana lumshe idanu da buɗewa. Kai ta girgiza masa zatai magana, shima ya girgiza masa nata alamar kartace komai. Ya ce, “please Ammie”.

 

Ruwan ta amsa, kurɓa biyu tai masa ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya, ta sake yunƙurowa zatai magana ya sake girgiza mata kai dai. “Please Ammie slow dawn ki faɗa min mike faruwa?”.

 

“So nake ka saketa kawai, ka janye garkuwar da ka bata, na sani dama Saiful-malik yarinyar nan bazata taɓa barinka ba. Amma Mammah da kai da Ammarah duk kuka gagara fahimtata, to gashi tun ba’aje ko’ina ba ta sake aikatawa. Yanzu badan ALLAH ya sa shi Sayeed Fayzul-haq ɗin ya lura ba wani zancen ake ba wannan ba, bazan iya jure rasaka ba a duniya wlhy Eshaan, dan haka ni kawai ka saketa na gaji haka bazan iya ba..”

 

“Wlhy Ammie ban aikata abinda kike zargina da shi ba”.

 

A tare duk suka dubi inda maganar ke fitowa, Iffah ce tsaye kanta a ƙasa, amma duk da haka ana iya hango yanda fuskarta tai jage-jage da hawaye. Abinka da fara tai jajir musamman ma kan hancinta. Wani irin mugun kallo Malikat Bushirat ke jifanta da shi, sai kuma ta miƙe cike da takun izza ta nufeta. Ji kake tauuuu!! Ta ɗauke fuskar Iffah da mari lafiyayyu haggu da dama. “K! Har kinyi isar da ina magana da ɗana ki kasance a wajen? Wacece k!? Ƴar uban waye k!?”.

Idanunsa ya rumtse da sauri jikinsa na wani irin yamutsawa, amma a zahiri zaune yake a dake yanda ta barsa ko kallonsu ma bayayi. Malikat Bushirat ta shaƙo Iffah da ko gezau batai a tsayen da take ba saboda taurin zuciya, duk da kuwa marin ya matuƙar ratsata dan zata iya rantsuwa ba’a taɓa mata mari mai azaba irin wannan ba. Yanda ta shaƙontanne yasa fuskarta ɗagowa, da wani irin gudu jini ya shiga fitowa a hancinta yana sauka har kan hannun Malikat Bushirat, hawayen fuskarta kuwa tsaf sun ɗauke, sai wani irin mugun jaa da idanun sukayi mai ban tsoro.

 

Malikat Bushirat da idanunta suka riga suka rufe ta ƙare matse wuyan Iffah duk da ganin jinin tana zazzaro manyan idanunta da itama suka kaɗa sukai ja.. “Yau zan kasheki na kashe banza wofi, sai naga ubanda ya tsaya miki da har kike tunanin idanunki sunyi tsaurin halakamin yaro…”

Wani irin kakarin azaba Iffah ta shigayi, ga idanunta sun fara juyewa, jinin hancinta ko sake gudu yake dan a tsinke yake (haɓo). Amma tsabar ƙarfin hali bakin bai mutu ba, jajayen idanunta da ke neman wulƙicewa ta zuba cikin na Malikat Bushirat tana sakin wani murmushin wahala. “A tunaninki kasheni ne zai canja komai? To kinyi kus…ku…ren fa… fahimtar hakan Ammie, dan masu san kashe ɗakin zagaye su…suke da ke. Idan kin kasheni ki ma… maciji kika kashe baki sare kanshi ba, ki rubuta ki ajiya ko gangar jikina ta daina numfashi sai ruhina ya dawo wannan masarautar ɗaukar fansar ruhin ƴan uwana……”

 

Wani irin yarfar da ita Malikat Bushirat da jikinta ke rawa yayi, dan wani irin guguwar bala’i ta hango a cikin idanun Iffah masu matuƙar gigitarwa tamkar ba ainahin idanun yarinyar ba. Akan jikinsa Iffah ta faɗa, dan yarfar da ita da Malikat Bushirat tayi dai-dai da mikewarsa dama, sai dai kalaman Ammien sa da shaƙar da tai mata kawai suka shiga kunensa da idanunsa, baiji komai na da ga abinda Iffah ta faɗa ba ita. Hankalinsa ne yay bala’in tashi da ganin jinin da ke fita a hancin Iffah, yay saurin tarota jikinsa ganin jiri na neman zubar da ita. Sake harzuƙowa Malikat Bushirat tayi. “Please Ammie, Please! Please” ya faɗa da wata irin raunananniyar murya mai sage duk wani kuzarin mutum.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button