Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 46

Sponsored links

“OMG!”.

Ya faɗa a hankali ƙasan maƙoshinsa jin tana kakarin amai. Bai motsa ba duk da yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, kusan mintuna biyu da wasu sakanni sai gata ta sake fitowa tana layi. Ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskar gwanin ban tausayi. Yanzu kam miƙewa yay da ƙyar ya nufeta, kamar jira dai-dai yana isowa gab da ita tai wani luuuu zatai baya ya tareta cikin zafin nama ta faɗo cikin hannunsa..

A hankali ta dinga jan ajiyar zuciya jin bata faɗin ba. Sai dai ta kasa buɗe idanunta da ke rufe ruf duk da tanajin alamun nasa kamar na binta da kallo. Kallon nata kuwa yake cike da kasala, sai kuma ya ɗan lumshe nasa idanun shima yana sake rungumota da ƙyau har yana jin saukar numfashinta a jikinsa. Yanda nunfashinta ke saukar masa a jiki sai yake jin tamkar shima hajijiyar na neman kwasarsa, gudun kar ai abin kunya ya ɗagata cak ya ajiye a saman gadon. Kafin ya zauna a kusa da ita yana mai tsura mata fararen idanunsa. Sun kai kusan mintuna biyu a haka, kafin ya katse shirun ɗakin ta hanyar motsa lips ɗinsa a hankali ya furta,

“What again?”.

Kanta ta nuna masa da gyar ta furta. “Kaina kamar zai fashe”. Sai ga hawaye sharr. Ita kanta bata san miyasa take jin karaya ba a gabansa ko ma shagwaɓa ne oho. Idanunsa ya zuba mata kawai yana bin hawayen da ke bin ƙyaƙyƙyawar fuskarta da gudu-gudu da kallo. Haka kawai sai yaji murmushi na suɓuce masa. Kansa ya kauda gefe yay murmushin sannan ya ɗan sake matsawa kusa da kan nata sosai. Numfashi ta ɗan ja a sanyaye jin saukar lallausan tafin hannunsa saman goshinta. Shi kansa yanda zafin kan ya ratsa hanun nasa sai da ya ɗan lumshe ido. Murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ta nan ne?”. Kanta ta ɗan jinjina masa, sai kuma ta ɗaura nata hannun saman nasa ta ɗan matsar zuwa gefen kunenta idanunta na sake kawo ƙwalla ta ce, “Harda nan da ma duka”. A yanda tai maganar cikin shagwaɓa kamar wata ƴar baby yaji tsigar jikinsa na wani yamutsawa. Amma jarumin naku sai yay ƙoƙarin basarwa har da yamutsa fuska kaɗan ya furta, “K raguwa ne ko? Just ciwon kai ki ke ma kuka?”. Kamar ya tunzurata ta sake turo masa baki da son ture hannunsa da ke kanta. Ko gezau, dan haka tai yunƙurin juyawa. Nan ma sai da ya nema sakin murmushi amma ya fuske. Cikin wata murya da mai lura zai iya fahimtar shauƙin da yanayin da suke cikin ke bashi ya ɗan matso da jikinsa gab-gab da nata yana faɗin, “Kin cika ragwantaka ne ai. Na miki addu’a?”. Kamar zata sakar masa kuka ta ɗaga kan dan da gaske kan na mata ciwo ne sosai.

 

Shiru bai sake magana ba ya kamota, kan nata ya ɗaura saman jikinsa. Sannan ya sake maida hanunsa saman goshin yana ɗan murza mata sannu a hankali yana mata addu’an. Idanun ta dinga lumshewa sannu-sannu itama, batare data farga ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bai daina addu’an da murza mata goshin ba, sai ma wani mayataccen kallo da yake mata idanunsa a shanye. Ya kwashe tsahon lokacin da bai fargaba a wajen zaune, dan tun kan da zafi har ya fara hucewa. Inda wani yace masa hakan zata faru tsakaninsa da wata ɗiya mace zai ƙaryata. Sai dai shi lissafin ƙaddara bai damu da wanda zai lissafa maka ba komai taka tsantsan ɗin ka akan nisanta kai ga abu…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button