Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 48

Sponsored links

Suna gama wayar ya fara laluben flight da zaije china yanzu yanzu, be samu ba saina anjima haka ya hakura ya samu guri ya zauna a airport din…….

Yana zama wata iranian babe tazo ta mishi hi, ko kallonta beyi ba bare ya san tanayi, shafa fuskar shi tayi tace;

“Hello handsome!”…..

Dagowa yayi ya dauketa da wani wawan mari dama neman inda ze sauke fushinsa yake abu ya cika da ita, a take yaga securities sun yo kansa, zabgawa wanda ya fara zuwa kusa dashi mari yayi ya naushi na daya gefen, yarinyar ce tayi saurin dakatar da securities din dan ita bataji zafin mari ba sam, ta kalli Deen da yake wuci kamar ze tashi sama tace;

“I’m sorry handsome”….Saida asuba ya isa china saboda tafiyar kusan awa shida sukayi, hotel din dake kusa da airport ya shiga yayi wanka yayi sallah sannan ya fito ya hau nemansu kamar yanda ya saba, duk inda zashi yana rungume da hotonta a kirji amma ya kasa nunawa kowa, ya gwammace yayita nemansu akan ya nunawa wani hotonta…….

 

Haka yayita yawo har gari ya waye……

 

Kwanansu uku a asibiti sannan ta dan dawo normal amma har lokacin baa sallamesu ba…..

 

Tana zaune khaleel ya shigo bayan yaje sun gaisa da Abby, a lokacin ta dade da sanin Abby dan kullum sai ya shigo ya dubata saidai haka kawai taji mutumin be kwanta mata ba shiyasa ta kasa sakin jiki dashi, zama yayi a kusa da ita, ya kalleta cike da so da kauna da tausayi yace;

“Ya jiki my love?”…..

Ya fada yana fita daga dakin, straight hotel din da suka sauka ya tari cab ya kaishi, yana zuwa ya dauko two bottles kamar yanda yaga tana sha ya saka a cikin hand bag dinta da suka siya sanda suka zo…..

 

Tana kishingide ya dawo hannunsa dauke da jakarta, mika mata yayi ta karba ta zuge jakar, ciro kwalaben tayi ta ajyesu a gefe, har zata zuge jaka ta hango wani abu, fito dashi tayi taga wayar Umm ce data dauka, jujjuya wayar ta shigayi a hannunta tanajin wani guilty conscious na kamata na daukarwa mata waya datayi, sai kuma oga ya fado mata arai, ko ina yake yanzu? Murguda baki tayi tace ‘masifaffe’, kallonta khaleel yayi yace;

“Ke kuma dawa?”…..

Deen daya keta yawan nemansu har lokacin ya kasa giving up kawai yaji tracker dinshi ya fara alarming din din din, da sauri ya duba wayarsa inda yayi connecting yaga processing address, ko kafin ya gama tantance ko mafarki yake yaga address din ‘American Hospital Dubai’, hakan kuma yana nufin an kunna wayar a chan ne, zabura yayi ya sake gyara tsayuwarsa yana kallon wayar da har lokacin address din beyi disconnecting ba, nan yagane wayo khaleel yayiwa sameer yake cemasa baya dubai, toh kodai sungane yana nemansu ne? Koma menene Allah ya tonu asirinsu, a yau dinnan basai gobe ba zeje ya samesu, cije dan yatsa yayi tuno da distance din dake tsakanin china da dubai, amma be gaza ba haka ya siye ticket a take ya bar china da short short dan baze iya jiran direct flight ba…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button