Hausa Novels and Stories

Idon Naira 11

Sponsored links

Sam bayan aikin wahalar hidimar gidan maryamah da hidmar maryamah din batada aboki Dan haka duk Takoma kaman wata nakasasshiya karatun ma yanzu sai ahankali Bata Wani ganewa zuwa kawai takeyi.

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._

_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._

_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_

_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _

 

 

 

_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_

_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._

_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _

Kasancewar maryamah nason kalolin abinci daban daban Kuma ta saba yiwa Alh Asad na Wanda ake fitarwa harabar gida da dare yasa ta Sanya zainab gurin koyan abinci Amma a online tareda siya Mata wata Yar tab wadda da ita take sake koyan komai.

Da farko zainab na Shan wuyar gane kan lamarin tab din gabaki daya kafin ma gane abinda take koya din

Amma sanin koyar Dole ce a gareta kaman yanda aikin tasani Dole ne itace wadda zata ringa yi har lokacinda Allah zai yanke Mata wahalar Dan haka ta ringa takura kanta tana dagewa gurin fahimta da koyon har Allah yasa ta Dan fara fahimta sosai.

 

Sbd yanda take tsananin kiyaye doka da shakkar keta kowace irin sharadi da iyakar da maryamah ta ajiye tareda dorata akai yasa yanda ta maida hankali da nutsuwa a gurin koyan girki da sauran ayyukan gidan ko karatunta bata bawa wanna kulawar da mahimmanciba.

Ahakan saida ta Dan dauki lokaci kafin ta iya gane kan tab din harma da abinda take koya din Wanda kullum da abinda take girkawa na abinda ta koya sai gashi tafara qwarewa musamman da Inna Karima Tana qara fahimtar da ita wasu abubuwan.

Ana hakan Maryamah ta Kuma samun wani ciki me laulayi sosai kala kala

hakan ya sanya Zainab sake zama busy da ayyuka sbd kusan yanzu idanba aikin zainab dinba daga Alh Asad har maryamah din basa son aikin kowa

Dan haka samun cikin yasa hidimar kulawa da buqatun maryamah suka ninkar Mata wata Rana ma ko makarantar Bata samun zuwa sbd tarin ayyuka.

Yanayin laulayin maryamah me wuya ne sbd yawan amai yake sata sosai Wanda yasa yanzu a wuni so uku ko so biyu take wanke toilet din dakin maryamah din bayan gyare gurarenda wani lokacin anan yake kufce Mata.

Samun cikin maryamah yasa zainab ta qarasa figewa kamar kamun yunwa sbd rashin Hutu.

Zainab bata ga amfanin Inna Karima ba a gidan don yanzu hutawa kawai takeyi girkinma an sakar Mata na Rana ne kawai ba ita keyiba sbd kafin tadawo makaranta tayi lokaci ya shige shi dinma Tana gamawa take komawar boys quarters ta shigewarta ita kuwa Sam hidimar Maryamah baya ƙarewa, bata da wani cikakken hutu sai idan dare yayi.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button