Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 6

Sponsored links

Kwance yake akan makeken royal bed d’inshi yayi matashi da hannayenshi ya tallafe keyarshi da su idonshi a rufe kaman me bacci amma ganin yadda yake kad’a kafanshi yasa na gane ba bacci yake ba tunanin marin da ta mishi yake lallai ta dibo ruwan dafa kanta ya riga ya tsara abunda ze mata daki daki don wlh tallahi bata mari banza ba tun randa ya bar companyn ya kira manyan companies da yake da share ya gargade su akan tallafawa fareed tower kuma sun hanu yanzu next step yake tunani……..

kyakyawar fuskanshi na kura ma ido, lallai gayen nan ya had’u iyakar had’uwa kyakyawa ne na ajin karshe……….

Dogo ne sossai yana da siffa irin na kauraran maza kirjinshi a bud’e yake sossai yayin da ya tsuke daga kwankwaso kanshi a cike yake da gashi baki wuluk se tsantsi an mishi gyara na ban mamaki, manyan brown oily eyes nashi kullum suna a lumshe kamar me bacci, hancinshi dogo ne kaman pencil amma daga qasa se ya d’an karye ya lankwashe kad’an se d’an madaidaicin lips d’inshi kyawawa red sossai kaman ya shafa man baki………..

Gashin giran shi a kwance kaman an zizara, ba fari bane kuma baza a kira shi baki ba sannan yafi wankan tarwad’a fatanshi me sheki ne sossai da taushi a gani d’aya zaka iya ce mishi fari ne sede ba farin bane, kirjinshi a cike yake da kwantattun gashi masu kyau da ban sha’awa wadda ya bi har shara’banshi na hannu da na kafa a kwance suke lufluf………

Sam fuskanshi ba fara’a a had’e yake tam kamar an aiko mai da sakon mutuwa, kai tun tashinshi ba takaiman man mutum da ze iya cewa ya ta’ba ganin dariyarshi abu ne wadda be yi ko da murmushi ne kuwa se wani kafurin murmushi da yakeyi in abu ya bashi dariya murmushin gefen baki wadda ko fuskanshi gabad’aya be zagaye wa shine murmushinshi kuma shine dariyarshi, Abokin shi d’aya S.A sagir Ahmad soja ne d’an jihar Adamawa……..

Iyayensu kafin su rasu aminaine sossai, shima S. A maraya ne be da uwa be da uba se de yana da ‘yan uwa ta ‘bangaren uwa da uba se yayyu manya mata shine karami kuma na miji sa’banin haisam da shi kad’ai se iyayenshi ya tashi ya samu kanshi da Allah ya musu rasuwa kuma se ya koma rayuwa shi kad’ai se in sun had’u da S. A suna yawan had’uwa kasancewar aikin haisam a sati se ya zagaye states d’in nigeria………

Agogo ne shi sarkin aiki gashi yana wuya kaga ya yarda da mutum, magana ma in bata business bane toh be magana da kowa se S. A…….

“Hello” shiru tayi tana jin bayanin da secretary d’inta ke mata “what kana nufin ya bamu appointment amma a yola?” Daga d’ayan bangaren aka ce “sorry ma’am haka secretary d’inshi yace and he said yanzu hk yana abuja amma yace in kina son ganinshi yhu should meet him at adamawa 10am prompt”……….

 

 

 

Dafe kai tayi cikin jin haushi tace “kayi min booking na available flight, now” yace “ohk” tare da kashe wayan tana ajiye wayan ta buga tagumi tana jin takaici na kamata a haka simra ta same ta tana tambayar ta me ya faru, bayani hamrah ta mata, hakuri simra ta bata tana cewa ta daure kar ta karaya ko don mahaifinta, da karfin gwiwa ta mike ta fara shirya abunda zata bukata a karamar trolley duk da tsoron dake ranta sam taki fadawa kowa abunda ta mishi har simra kuwa gashi bata san me yake shirya mata ba da ya kira ta adamawa………

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button