Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 53

Sponsored links

A ɗan zabure Iffah ta ɗago ta dubeta. Itama da idanu tai mata nuni da abincin. Sam Iffah ba fahimtar Yaren nan nasu ta cika yi ba kai tsaye, dan haka tai ɗan tsamm tana kallon Daneen Ammarah ɗin har sai da ta furta mata da baki. Numfashi ta sauke a hankali bana samun nutsuwa ba, na sake shiga ɗimuwa da kaikawon bugun zuciya, a saɓule ta motsa ta miƙe dan tayi ɗan nisa da shi, ta bayan Malikat Haseena ta zagaya ta koma kusa da shi ta durƙusa. Ta gefen ido ta ɗan sake kallonsa cike da taraddadi, cikin sauri ta kauda idanun dan abinda ta gani ɗazun ne dai ta sake gani, ta jawo numfashin dake neman kufce ma ƙirjinta da ƙyar….

“Ki haɗa masa waɗan nan”.

Daneen Ammarah ta katseta ta hanyar nuna mata abinda ke cikin kwanikan gabansa.. Da ƙyar ta iya amsa mata da to, sannan ta kame jikinta dake rawa, ta ɗan duƙo zata ɗauka abu ƙamshin turaren da bazai taɓa ɓace mata ba ya daki hancinta, da alama wanda take shaƙar ne tun ɗazun ya dannesa saboda ba’ayi amfani da shi ba a yanzu ko kuma wani abu da ban. Da sauri ta ɗan ja jikinta baya jininta na tsinkewa, yanzu kam duk yanda taso dannewa sai da halin da take ciki yaso bayyana….

Malikat Haseena ta jeho mata tambayar da har shi kansa sai da ya ɗan kallesu ta gefen ido. Kanta ta girgiza mata tana ƙoƙarin danne abinda ke neman fin ƙarfinta na ruɗani.

“Ina cikin godiyar ALLAH Mamma”.

Murmushi Malikat ɗin tayi cikin cigaba da nazartar ta harta kammala. Sosai kanta ke juya mata, dan haka ta koma mazauninta da jan jiki tamkar ta tsala ihu ko hakan zai bayyanama kowa a wane hali take ne…

Ko sau ɗaya Iffah ta kasa kai abincin bakinta, sai faman juya spoon take da satar kallon yanda yake tsakurar nasa abincin shima cike da ƙasaita. Lura da bata ci yasa Daneen Ammarah mata magana. Sai kawai tai murmushi da ɗan ɗiba kaɗan takai bakinta, juyashi take a hankali kamar mai tauna magani, dai-dai shi kuma ya ajiye nasa cokalin zai ciri tissue suka haɗa ido a karo na biyu. Da ƙarfin zuciya taso janye nata amma yaƙi bata damar hakan, sai ma jan nashi da yay cike da salo kamar zai lumshe ya sake buɗe su a tsakkiyar ƙwayar nata. Ƙwarewa tai tsabar lamarin yazo mata a bazata..

Daneen Ammarah da Malikat Haseena suka zabura kanta baki ɗaya, da kyar ta iya buɗe baki ta amshi ruwan da Malikat ta saka mata a baki, yayinda Daneen Ammarah ke faman shafa bayanta tana jera mata sannu.. A dukkan bidirin da ake idan dutse ya motsa Tajwar Eshaan ya motsa. Har tarin ma ya lafama Iffah ta samu daidaiton numfashi. Koda ganganci bata sake yunƙurin duban sashen da yake ba har lokacin tafiyarsa yay, duk yanda taso zamewa a masa rakkiya da taga Daneen Ammarah da Malikat Haseena na shirin yi hakan bai yiwu ba, dole ta bisu har waje. Tana ta faman ɗauke kanta amma tamkar wani sihiri sai da suka haɗa ido dai-dai zai shiga motar da aka buɗe masa. Wani irin karsashi da ƙwarin gwiwarta ne a bazata suka dawo jikinta, ta yamutse fuska da tsuke baki ta fincike nata.. Yayinda shi kuma ya ɗan motsa bakinsa tamkar mai son yin murmushi ko magana….

Ruɗani, mamaki, al’ajabi sun taru sun hana Iffah runtsawa a wannan dare. Kanta ya gama kullewa dangane da abinda duk suka faru ɗazun. Shin mutumin nan aljanin ne da gaske? Kokuwa wani abu daban da bata sani ba. Babu abinda ke mata kaikawo a zuciya sai haɗuwarsu ta baya har sau uku, kenan idan lissafin ta yayi dai-dai shiɗin jikan gidan nan ne tunda Daneen Ammarah ta kirasa da ɗanta, kamar yanda Malikat Haseena ta kirasa da jikanta. Shiyyasa yake komai cike da ƙasaita da izzar da ko Shahan-shan ɗin da kansa iyakar wadda zaiyi kenan ai. Ita kam al’amarin wannan gida ya fara birkita mata lissafi. A lissafin ta dai Daneen Ammarah aka haifa a gidan nan, Hakan na nufin ta rabu da mahaifinsa ne? Kokuwa a cikin gidan itama take auren? Dan ita dai tunda tazo anan take ganinta babu alamar tana da wani miji ko gidan zama bayan nan ɗin..

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button