Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 104

Sponsored links

……….A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da takejin sun mata matukar nauyi, sai kuma ta yunƙura ta tashi da ƙyar tana mai bin ɗakin da kallo. Dishi-dishi take ganin amintacciyar hadimar tata dake rukuɓe gefe ta zabga tagumi, _(An wayi gari da rashin

Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar.)_ kalaman hadimar na ɗazun suka shiga dawo mata tiryan-tiryan a zuciya. Da karfi ta rumtse idanun nata da sukai jajur, ga kanta dake matuƙar sara mata kamar zai rabe biyu. Amma haka ta yunƙura ta sauka a gadon cikin ƙarfin hali da jarumta, dan idan batai amfani da wannan lokacin ba tabbas damarta ta kuɓuce mata kenan, batajin kuma zata sake samun wata cikin sauƙi. Zumbur hadimar ta miƙe itama tana mata sannu, bata iya amsa ta ba, sai nuni da tai mata ta je. Jiki a sanyaye ta fice, ita kuma ta jawo mayafi ya naɗama jikinta.

Hadimanta dake falon farko duk suka miƙe, hannu ta ɗaga musu alamar bata buƙatar rakkiyar ta fice ita kaɗai dan babu yanda zasuyi. Da gaske masarautar a hargitse take matuƙa, duk da ba wannan ne karo na farko da aka rasa Zawjata-almilk ba, sai dai haɗi da mutuwar Sayyid Khairul-Bashar ta sake girmama ta Zawjata-almilk ɗin itama a wannan karon, da kuma tsallakewar Iffah da aka fara kaiwa babu abinda ya sameta. Cikin dabara da amfani da harmutsewar gidan tai amfani wajen kutsa kai sashen Shahan-shan. Zuwa yanzu fuskarta ba ɓoyayyar fuska bace ga masu tsaron sashen, dan haka babu wanda ya dakatar da ita sai ma gaisuwar girmamawa da suke miƙa mata duk da ganin nata ya basu mamaki. Su kansu hadimai masu girka abincin Tajwar Eshaan ɗin data samu a falo na uku saɓanin na karshe da ta san suna zama ganinta ya girgizasu, musamman daya kasance har yanzu ba’a fita da gawar Zawjata-almilk ɗin ba. Hasalima babu wanda yaga Shahan-shan har yanzu balle jin motsinsa. Kamar yanda tun a ƙasa bata tanka gaisuwar kowa ba anan ɗin ma bata kulasu ba dan ganinsu ya tabbatar mata anan abun ya faru kenan, ita wannan Zawjata-almilk ɗin a ɗakunan barcin falo na uku aka ajiyeta. Duk da bata san ya suke ba babu ko ɗar tattare da ita ta shige abinta inda take kyautata zaton ɗakunan barcin nan ɗin suke.

 

Ido rufe take bin ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, sai dai har kusan uku duk a rufe suke, bata gajiya ba ta cigaba sai a na biyar ta samu a buɗe. Cikin rawar jiki ta afka ɗakin, yayi kaca-kaca tamkar anyi dambe a cikinsa, dan wasu abubuwan ma duk gasu anan a fashe ƙasa, sai ɗigo-ɗigon jini ta wasu wajajen da dama. Idanunta suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar budurwar da a shekaru zata iya zama sa’ar Arfa shimfiɗe a ƙasa ta jikin gado. Yanda gashinta da jikinta ke a birkice zai tabbatar maka da ta jigata matuƙa kafin ta rasa ranta, dan hanunta na dama dake kaca-kaca da jini riƙe yake da wata kwalbar filawar doco… Alamar ta riƙe domin kare kanta, amma duk da haka sai da akaci galaba a kanta. Iffah da jikinta ke karkarwa ta durƙushe hawaye na rige-rigen sakko mata, dan ji take kamar Fariha da Arfa ne take kallo kwance. Ta jima tana kuka akan gawar kafin ta zabura sakamakon maganganu da takejin suna tunkaro ɗakin, zumbur ta muƙe ta fara daukar video recording ɗin ɗakin har gawar, sai kuma ta ɗauka hoton gawar ta kowacce kusurwa. Jin shigowar za’ai da gaske tai saurin fara neman wajen ɓuya.

Miran Jasim, tare da Miran Arshaan, shugaban jami’an tsaron masarauta, Daneen Ammarah sai Malikat Bushirat da a wannan karon ta kasa haƙuri itama suka shigo. Sai da suka gama bin ɗakin kaf da kallo kafin su ƙarasa kan gawar. Shiru babu wanda ya iya magana a cikinsu har tsahon wasu mintuna kafin shugaban jami’an ya nisa.

 

 

“Exactly kisan irin na baya ne dai babu wani banbanci gaskiya, da alama kuma tayi ƙoƙarin kare kanta itama shine dalilin kasancewar ɗakin a haka harma da wannan jinin”.

 

“Wannan lamari daban mamaki yake, taya za’ai kisa amma babu wani alamar yanda akayisan, a wannan karon kodai za’a canja likita ne? Dan dole dole akwai abinda yake a ɓoye. Yarinyar nan itace ta goma sha biyar da aka rasa, kisan kuma iri ɗaya babu wani bambanci sai kace abun tsafi”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button