Hausa Novels and Stories

Dare Daya Hausa Novel Page 7-8

Sponsored links

yawon barbaɗa da ubanki yake yine shine kema kika fara to wlh ubanki zanci a gidan nan sai narka mata hannunuwanta take a gadon baya tana ihu tana dan Allah INNA kiyi hak’uri wlh banzan ƙaraba ki yafe min dan Allah da gudu HAFSAT tafito daga ɗaki tana cewa INNA kiyi hakuri bazata ƙaraba kama hannun Mariya tayi ta miƙar da ita tana karkaɗe mata jiki ta turata ɗaki, taliyar INNA ta dauka ta jefawa BINTA tana cewa ke kuma shegiya tashi ki dafa mana yawuna har tsinkewa suke hanjina na kuka sbd yunwa dauka tayi jikinta na rawa sbd kar itama a dake ta Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci BINTA ta kammala tahuwar taliya sai kamshin Manja ke tashi INNA sai hura hanci take yau za’aci taliyar kamfani ƙwalawa Mariya kira tayi jiki na rawa Mariya ta fito tana cewa gani INNA dauko min kwando jiki na rawa taje ta dauko kwando babu kwanon ƙwarai ciki, nan ta shiga fito da kwanoni tana jerawa kwano yakai ashirin nan tashiga raba taliya guda ɗaya 🤣🤣amma kwano yakai ashirin sai yaryaɗa taliyar tace kwano ɗaya naga anzubawa abun ƙwarai aka miƙawa Mariya akace ta kaiwa HAFSAT itada Takeda ƙashin arziki

Tana idar da sallah ta tashi tasa dan ƙaramin hijab saman rigar material dinta ta fito zuwa ɗakin MAHELET sanyin idaniyar ta abun ƙaunar ta hallita mafi soyuwa a gareta Sam batasan wane kalar so take yiwa yarinyar bah tanajin sonta a cikin jinin jikinta Tanaji a ranta duniya zata iya sadaukar da komi akanta, tura ƙofar tayi ta hangota zaune a can gefen gado ta shinfiɗa carpet ta barbaza littafan ta tana karatu wasu kuma duba su ne kawai take sallamarta da taji yasa ta ɗako kai ta tashi a Kuje ta faɗa jikin matar ta ƙanƙame ta tana cewa MOMMA MIA yaushe kika dawo inata tunanin ki shafa kanta tayi zuwa gadon bayanta ba tare da tace mata komi taja hannunta sukaje gefen gado ta zaunar da ita tasa hannu ta ɗago da haɓarta tana cewa MOMMA BABY me ya same ki kwana biyu duk kin rame ko bakya cin abinci ne tana magana tana ƙoƙarin zaunawa daga gefenta ƙara shigewa tayi jikinta tana cewa your my life momma, your are the best ever momma in the world, your are my philosopher, your are CCTV, you are my Alarm clock, you are my ATM, ƙara ƙannameta tayi ta tusa kanta akan kirjinta tana shaƙar kamshinta tana sauke ajiyar zuciya a hankali zuciyarta na bugawa da sauri sauri kamar wacce tayi wasan tsera hannu momma tasa zata ɗagona ta ƙara ƙanƙameta tana cewa dan Allah momma Mia ki bari naji duminki dan Allah karki cireni ajikinki fashewa tayi da wani kuka mai tsima zuciya still kanta na manne a kirjin momma, Sam bata hanata kukan ba kuma bata ɗago ta ɗaga jikinta ba saima shafa bayanta data shiga yi a hankali tanajin son MAHELET har cikin zuciyarta tanajin babu wanda ya isa ya raba su a duniyar nan sai Allah, jin tayi shiru sai ajiyar zuciya datake saukewa yasa ta dagota ta share mata hawayen da suka ɓata baby face dinta tana cewa shikenan is okay gobe tare zamu fita nasan shine kike yiwa kuka, girgiza mata kai tayi hannunta ta dauka akan haɓarta ta ɗaga kanta sama alamun tunani tana cewa uhmmm mm yauwa kinaso na canza miki waya ƙara girgiza mata kai tayi tana ƙoƙarin komawa jikinta da sauri ta tareta tana cewa to gayamin menene? Ƙafe fuskar momma din tata tayi da kallo kafin ta buɗa baki cike da shagwaɓa tana goge hawayen da ke sauko mata tace A’a momma Mia Dan Allah ki bari muringa kwana tare murmushi momma tayi tana cewa MAHELET you are no longer a child fah you are a big gal now, okay so tell me are you scare of this room?

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button