Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 7

Sponsored links

Cikin natsuwa ya mike da takun shi na qasaita ya fara cire kayan jikinshi se da ya saura daga shi se boxers tukun ya zaro towel d’inshi fari Kal ya shige toilet dake manne da d’akin se da ya shafe wajen mintuna 40 kafin ya fito ya nufi closet d’inshi kaya ne kala kala ko wanne da bangaren da aka ajiye shi a goge tsab, half jumpa ya d’auka ya saka black gezner me sheki ya sa black Zanna me adon fari a kanshi da half cover black……..

Black Gucci wrist watch yasa a hannunshi ya fito tsab da shi se fitinnannen kamshi ke tashi a jikinshi me sanyi, a natse cikin takun isa da kasaita wayanshi kawai ya d’auka yayi gaba abunshi yana fita daga d’akin ya nufi dining area, abinci d’an kad’an ya zuba kaman wadda ze bawa baby ya hau ci a yangance a hakan ma be karasa ba ya mike, fitowa yayi da sauri me mishi hidima da kuma shugaban securities/escorts d’inshi…….

Yaqoob ya taso ya karaso kanshi a kasa cikin husky masculine voice d’inshi yace “ka fad’awa pilot d’in nan yayi arranging jirgin nan zamu wuce yola yanzu” cikin isa da bada umarni yayi maganan a natse Yaqoob yace “ohk sir” da sauri ya juya yana waya, komawa haisam yayi ya samu cushion ya zauna yana danna waya kusan 20 mins kafin yaqoob ya dawo ya fad’a mishi an gama se da ya Kara 5mins tukun ya mike ya fice a mota aka d’auke shi aka nufi filin tashi da saukan jirgin duk a cikin gidan……..

Suna isa aka bud’e mishi kofa ya fita ya nufi jirgin da an riga ma an kunna shi kawai suke jira basu Kara 2mins ba suka tashi daga shi se yaqoob se pilot d’in jirgin cikin 40mins suka isa yola straight gidan shi na malamre suka wuce dake jimeta se da yayi wanka ya ci abinci ya huta tukun around 2 ya nufi gidansu S. A………..

Washegari karfe 8 daidai jirgin hamrah ya sauka a modibbo Adama international airport dake jimeta direct textile company d’inshi dake jimeta ta nufa a taxi ko breakfast batayi ba tana isa aka mata iso har gurin da ya kamata ta jirashi…………..

Zaman good two hours tayi ko me Kama dashi bata gani ba se workers d’in companyn ke kai kawonsu, wayanta ta fitar ta fara wasa da shi ta kai wani hourn zaune tana online da ta gaji ta fita ta shiga best game d’inta candy crush ta fara bugawa ta kai hour again tana bugawa nan ma gajiya tayi ranta ya sosu sossai kwanciya tayi ta jingina kanta da kujeran dake zaune ta lumshe ido……….

Chan hawaye ya gangaro mata mikewa tayi ta kalli time a kalla ta kai 5h zaune a gurin mikewa tayi tare da neman ganin secretary d’inshi aka ce mata be zo ba tare suke, kiran nata secretary d’in tayi yana d’auka murya na rawa tace “please Arham call haisam’s secretary wai ya manta sun bani appointment ne, am here for at least 5hours amma har yanzu basu appearing ba”………….

Daga chan secretary d’in yace “subhanallah sorry ma’am let me contact him” bata amsa ba ta kashe wayan ta ci gaba da share hawaye a boye……

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button