Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 173

Sponsored links

Babu wanda bai zaro ido ba a falon. Cikin bacin rai Iffah ta ce, “Na fika sanin wannan”Jikin matar na rawa ta cigaba da zayyano mata sauran. Yayinda tuni Ummu dake rude Iftihal mamuke da ita ta yunkura da niyyar zuwa ta nemi Kaka a waya, dan dazun da sukazo sun kawo mata wayarta shima Babiy yana amfani da nashi. Kin sakinta Iftihal tayi, dole sai tare suka tafi. Iffah kam juyawa tai ta dubi hadimanta da ke dauke da abincin data bada umarnin a biyota da shi, ta nuna na hannun amintacciyarta. “Ajiye musu shi suci”

 

 

Da ga Banou har abokiyar aikin nata kuka suka sanya, dan su suka san abinda suka gani a abincin. Ko kallo basu ishi Iffar ba, tana tsaye a kansu fuskarta kawai abar firgitarwa ce. Haka suka fara cin suna kuka da rokon tayi hakuri, a haka su Malikat Haseenat da akeje aka sanarmawa suka shigo hankali tashe. Dan can sun samu Malikat Bushirat tayi barcin da kyar bayan an rufu kanta da addu’oi. Kallon Iffah da su Banou din kawai suka tsaya yi cirko-cirko. Daneen Waheeda kam tuni ta koma bayan Mammah ta makale, yayinda Daneen Ammarah itama nata kamanin suka fara canjawa dan idanunta sun kada sunyi jazur. Ture abincin Iffah tai da ga gabansu, ta wani irin hankada Banou gaban Malikat Haseenat. “Jeki sakar mata kafafu!!”. Cikin madaukakin mamaki Malikat Haseenat ke duban Banou da Iffah. Sai dai razananniyar tsawar da Iffahr taima Banou din ita kanta sai da zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa. Banou dake kuka cikin rawar jiki ta kama kafafun Malikat Haseenat, wani fushin kumburi da kafafun sukai tsahon shekaru an kasa gane kansa sai gashi yau yana bajewa, Kusan minti biyu tace mata ta mike, mikewar tai jikinta sai kakkarwa yake, du da girman jikin nan nata ga tsaho amma Iffah dake yar digila gabanta ta zame mata dodo. “Na baki minti hudu, ki dakko tukunyar da kika ajiye a cikin flowers”.

Banou din ta fada cikin sake gurfana. Suna tsaitsaye har yanzu babu wanda ya iya cewa komai sai ga Banou ta dawo da tukunyarta, A gaban Iffah ta zube, ta bude tukunyar ta shiga fiddo abubuwan da ke ciki. Abinne kamar tsokar nama, duk ta daure. Kwancewa ta shigayi tana sakinsu, firrrr suke tashi kamar tsuntsaye, wasu ko da kyar zakiga sun tashin saboda ta jima tana wahalar da su. Cikin

bada umarni ta dubi sauran hadiman ta ce, “Aje a duba duk wanda yake a halin ciwo ya mike a yanzu a kaimun shi tsakkiyar masarautar nan. Ina bukatar Ghazi guda biyu anan”.

Cikin kankanin lokaci Ghazin data bukata suka shigo, su tasa suka tasa mata keyar su Banou.

Tun fito da Hadimar da ta jibga a sashenta al’amarin ya fara zagaye masarautar. Abin mamaki sanda take fitowa su Malikat Haseenat biye da ita masarautar ta gama cika. Dan sashe-sashe an fito kamar busar kaho. Cikin kankanin lokaci duk wani mara lafiya dake gidan aka fito da shi, harma wanda ba Banou din ce ta tabasu ba. Tana kuka da faman rufe fuska ta tsatstsallakasu. Tana gamawa suma sawa tai aka daure mata su tare data farkon. Dai-dai nan su Baby suke isowa cikin masarautar. Hakama Tajwar Eshaan a rikice Malikat Haseenat tai kiransa ta sanar masa babufa lafiya a gidan da ya kamata ya

 

fito. Dama shirin fitowa yake, dan amintaccensa yazo masa a kidime babu dadewar nan, hakama Sayeed Fayzul-haq ya kirasa shima.

Lokaci daya wajen ya dauki shiru sakamakon fitowar tasa, dan abunne da babu wanda yay zato. Kowa a wajen sai da yay kasa da kansa har Iffah, dan a zahirinsa yake kyakykyawar fuskar nan a bayyane, sai dai fa cinkus take babu alamar wasa ko sassauci. Amintaccensa ya ajiye wata yar kujera mai kyau dake a ninke aka budeta. Sai kuma katuwar umbrella da aka bude masa duk da bawani ranar nada zafi bane dan ta la’asar ce ma dake neman faduwa. Sai dai kuma a mamakin kowa ma bai zauna ba. Sai duban Iffah da yay na kusan mintuna biyu. A hankali ya furta, “Mike faruwa”. Cike da irin girmamawar dake nuni da ba ita bace ba ta kai kasa gurfane gabansa. Gaisuwa ta fara mikawa,kafin dukkan abinda ke faruwa ta zayyane masa. Idanu ya dan lumshe da sake budewa. Kamar bazaice komai ba sai kuma yay mata nuni da ta tashi, tare da fadin,”Duk da ba itace a tare da gangar jikinta ba kuskurene kai Zawjata-almilk kuma * Malikat * kasa a kowane irin yanayi a gaban al’ummar kasar ta”

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button