Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 10

Sponsored links

Sauran ruwan zafin lipton da Ababa yasha shayi aka basu babu bread haka suka shanye zallar ruwan zafin da ko sugar baijiba sukai shirin makaranta suka fice.

Suna fita yauma tafiya kadan sukai motar Bilal daya kwana dasu a ransa baida sukuni ta tsaida mashin dinsu a kunyace suka sauko sbd overload dinsu ba kyan gani itace a tsakiya sun matsu iya matsuwa suda mai mashin dayake jin tudun kirjinta wanda kusan hakan suke zuwa makarantar kullum babu ranar da har akai makaranta ba cikin baqin ciki da quncin yanda jikinsu ke manne dana mai mashin din ba.

Shi kansa Bilal dake cikin motarsa qarewa yanayinsu dana mai mashin dain yayi yaji wani irin abu ya tokare kirjinsa musamman yanda kowaccensu dazata sauko kusan daida jikinta dana mai acaban ya hadu.

Rufe idanuwansa yayi ahankali tareda dauke kai daga kallon gurin glass ya aka sauke drivernsa ya miqawa mai mashin din 2k yace ya wuce kawai.

Drivern da kansa ya fito ya bude musu bayan motar suka shiga sbd Sir bilal din yana seat din gaba.

Suna shiga aka bar anguwar dasu babu wanda ya iya magana acikinsu bayan gaisuwar da sukai masa cikin girmamawa da nutsuwarsu dake sake samar musu da gurbi a zuciyarsa.

Hanyar asibiti suka nufa kai tsaye

Yau babu bata lokaci dubata akai aka canja dressing din qafar wanda suna kama hanyar gida suke ciresa su yar sbd kada a gani.

Ana gama dressing gurin aka bata magani tasha suka fito ya ajiyesu makaranta bayan yasa akawo musu abinci daga restaurant dinsu na Kaante hotel and suites.

Suna fitowa first lectures dinsu aka kawo musu abincin har kofar hall dinsu sumayyah din sbd Sir bilal ya sanar dashi hall din dazai sameta tinda ba waya ne dasu ba.

Sumayyah ganin mutane dakuma tsoron jawa kai attention yasa ta karba da sauri tabar gabansa ta nufi gurin Benazir da itama tsoron ganin abincin yasata jan sumayyah suka bar cikin mutane.

Nesa da mutane suka boye suka zauna tareda zubawa ledojin ido hankalinsu tashe sbd zuwa lokacin har ga Allah taimakon ya ishesu tinda sumayyah din tasamu sauki ba laifi

Har aka tashi basu ci abincin ba suka fito saiga driver yana jiransu a gate suka dauke kai suna shigewa mutane sbd kada ya gansu amma haka ya ringa binsu yana sanar dasu Sir bilal yace kada abari su hau mashin.

 

 

 

Benazir kaman zatai masa sujjada ta ringa rokonsa ya dena binsu shima kaman zai musu sujjadar ya ringa rokonsu akan umarnin mai gidansa ne.

Sumayyah datafi shiga tsoro tana kalle kalle tace su shiga kada wani yagani tinda ba tafiyar zaiyi ba.

Haka suka iso anguwarsu kaman zasuyi zawon kayan cikinsu sbd tsoro.

Yana ajiyesu suka fito qafafu na rawa suka nufi hanyar gidansu suna waiwaye sbd ledan dake cikin hijabansu.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button