Hausa Novels and Stories

Idon Naira 42

Sponsored links

Daga bayansu zancen ke fitowa Dan haka dukkanin Maza da matan gurin tsoro da fargabansu yafara raguwa Dan kuwa LULU ce da kanta tafito take magana wato shahararren ‘dan daudun daya Gama riquwa a bariki tareda gogewa a harkar duniyanci

Fari ne tas dashi kyakkyawa Amma babu wani Abu daya nuna tsoro ko fargaban halinda suke ciki.

Kofar ya nufo Kai tsaye ya bude Yana cewa”

Kuzo ku fice qartin banza da wofi wlh sai antafi daku ai Dama na Hana kowace shegiya kawomun Maza a gida ku wuce.

Bude kofar yai gabaki daya ya fito batareda tsoro ba ko shakkar abinda yake faruwa a wajen.

Take kuwa yayiwa mazan cune aka shigo aka kamesu duka cikin tsautsayi aka hada harda zainab wadda kwata kwata takasa gane meke faruwa Dan hankalinta ya Jima da barin jikinta.

Har ansakata a mota ganinta da goyo Kuma kamar Bata hayyacinta yasa LULU cewa Banda ita.

Ba musu aka sauko da zainab Yan sandan suka wuce bayan sun cika mota uku da Yan ta’addar dasuka tada fadan Dama kwartayen dasuka kwana gidan karuwan LULU.

Bayan Kamen Yan sandan sun wuce anguwar ta lafa aka fara firfitowa kowa naci gaba da harkar gabansa..

Zainab kafafuwanta dake rawa takasa dagawa sbd tashiga babbar firgici na abinda yafaru din kamar kyaftawar ido.

Kasa magana zainab tayi sai tayi gaba tana fasa neman kayanta duk da taso Kayan Dan basuda wasu saina jikinsu daga ita har MARYAMAH.

Ganin yanda take a kamar Mata hankali tana kallon babban gidan da gadonta yake ciki yasa LULU biyota ya kirata zaiyi magana yaransa suka iso mota kusan biyu suna masa kirarin,

“sai hajiya LULU”

Washe Baki yahau Yi Yana kallonsu sbd sune abin Alfaharinsa

Dan kuwa sune masu cire Masa baqin cikin aike kowane irine.

Qin binta zainab tayi saidai Kuma ganin shine maqocin babban gidan yasata tunanin jiran ko zata Samu bayanin dazai isar da ita inda gidan mahaifinsu yayi.

Shikuwa Lulu ganin yanda take kallon babban gidan makocinsa Kuma maqiyinsa yasashi son tsayar da ita yaji

Babbar fatarsa ace MANDE DS ne yayiwa matar wani abun yayi amfani da hakan ya lalata Masa suna da komai ya nuna Masa iyakarsa.

LUKMAN AHMED Wanda ake duniya ta sani da Lulu Asalin Dan anguwar ne Wanda mahaifinsa shima rasuwa yayi tun Yana qanqani,

Shi kadaine agun mahaifiyarsa namiji sai qanwarsa mace wadda ta rasu sanadiyar fyade da akai Mata da qananun shekaru,

Rasuwar qanwarsa ita tayi sanadiyar ta mahaifiyarsa wadda ta rasu bayan sunyi yawon Sharia Har qarfinsu yaqare babu nasara sbd Dan manya ne yayi Mata fyaden bayan yayi shaye shaye.

Lulu yayi gwagwarmayar rayuwa bayan rasuwar mahaifiyarsa ya dauki fansar abinda akaiwa qanwarsa da hannayensa ta hanyar saka mugun itace yaron da yayi barnar dukan da yayi sanadin daya rasa idonsa daya da qafafunsa duka biyun tareda hakoransa na Hana guda shida.

Hakan yajawa Lulu masifa Mai tsanani aka aikasa gidan yari tsawon shekaru goma Sha daya

Yana fitowa yashiga harkar siyasa inda yasamu shahara amatsayinsa na ‘dan daudun daya Gama cire tsoro da shakkar kowa.

Lulu yasamu shiga da suna sosai duniyar Yan siyasa da Yan duniya,

Gidan abinci ya bude babba Mai kyau da tsada,.

Ana haka aka Kuma yiwa yarinyar datake Masa aikin abinci a restaurant dinsa fyade Wanda yaja aka rufe restaurant din nasa yayi hasarar duka Dan arzikinsa..

Lulu yasha gwagwarmaya da wahalar rayuwa matuqa kafin yasamu yadawo gidan ubansa ya gyara..

Tun bai Gama gyaranba alhaji MANDE DS mahaifin Yaron dayayiwa kanwarsa fyade ya siye gidajen layin kusan guda hudu a jere ya bugesu yayi babban gidansa agurin batarda ya dubi lalacewar da anguwar tayiba tareda ga Kuma qarin Shi din Dan siyasa ne take jamaarsa suka sake maida anguwar ta yan siyasa.

Alokacinda mande ds ya siye gidajen yasone ya siye harda gidan Lulu sbd abinda yayiwa dansa yaketa sakawawa Ana lalata komai na lulun,

Rikicin siyan gidan lulun dayaqi saidawa ne yasa yane mande ds ne ke lalata Masa komai na rayuwa Dan haka yaqi saidawa qarshe ya maida gidan nasa na karuwai Dan kuwa gidan babbane dakuna birjik.

Mugun zama sukeyi da junansu sbd babu Mai kaunar wani tsakanin Lulu da alhaji mande ds din,

Lulu siyasar dayasan baa kaunar mande ko kadan ita yakeyi bakin Rai Dan haka yasa anguwar kullum cikin fadan sare sare akeyi na siyasa ga Kuma qaramar kasuwa a gurin,

Ga gidan Lulu daya shahara na karuwai,

Ga babban gidan abinci daya Kuma budewa anan Dan haka dai anguwar ta lalace gabaki dayanta babu mutumin kirkin dake zuwa,

Lulu da qarfin iko da lalacewarsa da karuwansa yayi amfani ya lalata suna anguwar kwata kwata sbd kawai duk lokacinda aka ambaci anan gidan Alhaji mande ds yake mutuncinsa ya zube a idon mutane.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button