Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 171

Sponsored links

akwai matsala ne why, tabbas akwai matsala, dan dama likita nata zaryar dubata tsakanin jiya da yau”

 

 

 

Babu wanda gabansa bai fadiba

 

a cikinsu, dan dama basu jima dayin maganar rashin ganinta a kotu ba. Daneen Waheeda ce make cewa kila bata da ra’ayin zuwan ne yau tunda sun san halinta. Gudun kar maganar tai tsaho ga Ummu da take bakuwa a tare da su yasa Daneen Ammarah kauda zancen ta dako wani.

 

 

 

 

 

 

 

Gaba dayansu suka kunduma sashen Malikat Bushirat, Ummu kawai aka bari. A gaban idon Banou da ke tsaye da wata bakuwar fuska a jikin fulawoyi suka wuce.Da wani mummunan kallo suka bisu, sai dai babu wanda yace komai. Su Malikat Haseenat da basu san sunayi ba ko mota suka shiga zuwa sashen Malikat Bushirat din. Sun sami Hadiman sashen Jigum-jigum, dan zuwa yanzu kusan duk sunji irin kukan da Jasrahn keyi. Babu wanda ya saurari gaisuwar hadiman sukai ciki da hanzari, dan suma dai suna shigowa da kukan Jasrahn suka fara cin karo. A bathroom din suka sameta har yanzu, da kyar Daneen Ammarah ta dagata, rungumeta tai cikin jikinta dan ta sami nutsuwa, Malikat Haseenat kuwa inda Malikat Bushirat ke kwance wanwar ta nufa, tattabata ta shigayi. Daneen Waheeda dai na tsaye babu alamar damuwa tattare da ita. Sai ma bin toilet din take da kallo baki a labe. Da kyar Daneen Ammarah ta lallashi Jasrah har ta dan musu bayani a takaice. Dole aka kara kiran Doctor sannan aka saka hadimai shigowa suka kakkamata aka fiddota aka kwantar saman gado.

Zuwan doctor ya tabbatar musu ba mutuwa tai ba, ta dai suma ne. Ajiyar zuciya suka dinga saukewa, shi kuma ya shiga kokarin ganin ta farfado, yayinda Malikat Haseenat ke faman tofa mata addu’oi. Wani irin numfashi ta kawo tare da zabura mai karfi, wadda har doctor dole ya kai hannu a kanta domin maidata amma ya gagara shi kadai. Dole Jasrah da Daneen Ammarah suka matso domin taimaka masa. Amma fa sun kasa dan wani karfi na masifa ta musu, ga fisge-fisge tanayi na tashin hankali.

(Tofa al’amarin fa babbane) cewar Daneen Waheeda a cikin zuciya tana dan tabe baki. Suko da basu san tanayi ba sunata kici-kicin son gain ta lafa, Malikat Haseenat kuma na tofa mata addu’a. Da kyar suka iya tankwarata, har sun hada zufa sharban kamar yanda itama tayi.Numfashi suka shiga saukewa na jigata. Doctor kuma ya shiga aikinsa. ya sake maidata barci sai dai fa barcin yaki yiwuwa. Dan da ya dan figeta sai ta zabura sai sun sake dannata ta

koma kwance. Al’amari fa tun anayi da marmari harya fara gundurar kowa aka karo doctors da was alluran masu karfi sosai da sukafi na farko da akai mata..

Cikin kankanin lokaci zancen rashin lafiyar ya zagaye masarautar. Masu tausaya mata nayi masu farin ciki nayi. Masu kuma fassara al’amarin da wani abu daban nayi. Dan danan labarin ciwon nata ya zama latest topic à cikin masarautar. Dama ga nã hukuncin su Miran Jasim da bai gama disashewa ba.

Duk wanna al’amarin Iffah nacan kwance tana shan barcinta bata san bikin da ake ba. Dan sai la’asar ta tashi. Wanka tai tayi salla. Bayan ta kammala kimtsawa ta fito neman abinci dan yunwa takeji. Hadimanta da ke dan kus-kus din su suma akan al’amurin Malikat Bushirat din sukai saurin mikewa. Kallo daya ta musu ta dauke kanta, dan har yanzu zuciyarta babu dadi. Zama tai tare da bada umarnin a kawo mata abinci anan. Cikin ko kankanin lokaci amintacciyarta ta jere komai. Ta bude zata zuba mata ta dakatar da ita idanunta kur akan abincin. “Waya dafa wannan abincin?”Ta fada tana kallonsu. Cikin rawar jiki amintacciyar tata ta sanar mata itace da mai girki. Ta nuna mai abincin. Shiru Iffah tana duban wadda aka nuna matan sai faman sinkuy da kai take. Ai bama tasan ta daka mata tsawa ba tace ta dago. Ba ita da taima tsawar ba hatta sauran hadiman sun matukar razana. Dan abu ne da bata taba musu ba. Wani irin kallo Iffah take ma matar rai bace. Jikinta har tsuma yake ga idanunta sunyi jazur na tashin hankali. Duk wanda ya dubeta sai ya razana, idan ma irin su Bily ne fitsari zamu saki a zani😝Dan gaba daya ta juye tabbacin ba Iffah bace.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button