Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 50

Sponsored links

Turus Jasrah tayi ganin babu Abu Harith a inda ta barsa. Sai kuma ta nufi ɗakin barcinsa da tunanin koya shige. Nan ɗin ma dai babu alamarsa har cikin bathroom. Batare data kawo komai a ranta ba ta ɗan ɗage kafaɗa ta fito.

★Shi kuwa da tun bayan ficewarta ta ɗazun da kamar mintuna uku ya fice cikin ɓadda kama ya nufi sashen Miran Jasim. (Miran Jasim ɗane a wajen Ameera Banafsha, matar Tajwar Abdul-majeed ta biyu, shine ɗa na huɗu a wajensa, a maza kuma na biyu. Miran Arshaan ke bi masa. Sam babu jituwa tsakanin Ameera Banafsha da Malikat Haseena, ko mutuwar Miran Nayyar an dangantata da Ameera Banafsha a wancan lokacin. Sai dai da yake yaƙin sunkuru ne tsakanin matan biyu duniya bata san da haka ba. Burin Miran Jasim shine mulkar kujerar Shahan-shan tun yana ƙarami kamar yanda mahaifiyarsa ta horesa a kai, dan haka tayi matuƙar gwabza ɓoyayyen yaƙi akan marigayi Tajwar Haysam akan haihuwa har ALLAH ya bashi Tajwar Eshaan. Haihuwar Tajwar Eshaan wata ɗimuwace a nasararsu, saboda haka sun aikata abubuwa da yawan gaske na ganin bai kai ga matsayin da yake a yanzu ba ciki harda karkato da hankalin Miran Arshaan babban ɗa ga Ameera Aasfah amintacciya a wajen Malikat Haseena miji kuma ga Jasrah. Miran Arshaan sam bai biyo ƙyawawan halayen mahaifiyarsa ba, munafuki ne shima kuma yanada boyayyan nasa sirrin duk da riƙo irin na uwa da Malikat Haseena tai masa bayan rasuwar mahaifiyarsa, shiyyasa ya yarda ya haɗa kai da Miran Jasim domin kauda Tajwar Eshaan. Amma kaico UBANGIJI shi mai bawa wanda yaso ne, dan gashi dai Tajwar Eshaan ya zama Shahan-shan a daular ruman. Amma hakan baisa sun bar ƙulla-ƙulla na ganin cikar burinsu ba. ALLAH yasa kun gane🥲).

Miran Jasim da dama tsumayen isowar Miran Arshaan ɗin yake ya miƙe daga zaman ƙasaitar da yay a katafaren falonsa da ya jiku da kayan more rayuwa. Juna suka tsirama ido cikin nazari dan bayan ƙullin tsakaninsu kowa nada ɓoyayyen sirri na akan ɗan uwansa. Miran Jasim ne ya fara kauda kansa ya maida hannayensa baya ya goya ya tako a sannu har tsakkiyar falon. Hakan yasa shima Miran Arshaan ɗin ƙarasa shiga suka tsaya gab da juna.

“Arshaan Akh Barka da isowa”.

Kai Miran Arshaan ya jinjina masa, sai kuma shima ya maida hannayensa ya goya a bayansa tare da ɗan takawa ya koma ta gefensa yana fiskantar window. Murmushi Miran Jasim yayi tare da juyowa yana kallonsa. Shima ya ɗan taka ya sake komawa gabansa. “Arshaan Akh kayi shiru, bayan kuma naga magana mai muhimmanci a cikin idanunka kamar yanda ka sanar dani ta waya”.

Huci Miran Arshaan ya furzar, sai kuma ya ɗago suna kallon juna shi da Miran Jasim ɗin. “Jasim Akh akwai damuwa ne. Yanzu nakeji wajen Zawjata. A ziyarar Yaron can ta yau wajen kakarsa akwai shirya ganawa tsakaninsa da yarinyar da shashashar matar can da ban san amfaninta garemu ba tasa muka aura masa”.

“What! Waye yay wannan ƙullin?”.

“Bana tunanin kana buƙatar tambaya dan kasan wace gadararriyar ce zata iya yanke wannan hukuncin. Na gaji da ganin matar can a raye.”

Murmushi Miran Jasim yayi da cije lips. Cikin ɗacin murya ya ce, “Ba Bushirat bace ta cancanci mutuwa. Waccan tsohuwar ce Arshaan Akh. Sai dai kuma su duka bazasu mutu yanzu ba”.

“To sai yaushe?”.

“Sai sunyi kuka akan gawar wancan shashashan yaron kamar yanda sukai kuka akan ta ubansa”.

Karan farko Miran Arshaan ya saki murmushi. Sai kuma ya warware hanunsa da ɗage kafaɗa. “Hakan ma shiri ne mai ƙayatarwa. Yaya batun uban yarinyar da ɗan uwanta? Dan sun sami Barrister Abdullah Aas a yanzu haka”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button