Hausa Novels and Stories

Fulani Page 2 Hausa Novel

Sponsored links

Inna Ladi na fadar hakan ta juya ta fice rike da kwayar sabon nonon da ta taso yanzu, nonon da ko manshanu ba a cire masa ba.

Mika Fulani tai tana sauraren busar Sarewar da take yawan jin a cikin bachinta, ba kuma dan ana burar a Sahiriba sai dan sabo da tai da ita a kowa wane bachi, ya’alan na safe ne ko na rana ko dare, indai har ta kwanta sai ta yi mafarkin wannan mutumen da ya bata baya yana ta burar sarewa a saman dotse, busar da ke sakata hawaye da murmushi a lokaci daya kuma a cikin duniyar mafarkinta, sai dai murmushin da hawayen har a zahiri ana ganinsu, yayinda busar sarewar kuma ita kadai take jin abarta a cikin bachinta. Mikewa tai tsaye ta nufi gurin jakar kayanta ta dauki littafinta da buro ta zauna a gurin ta soma rubutunta kamar yadda ta saba.

_Yau ma na yi mafarkinsu, dayan a gefena mai busar ya ba ni baya, dayan kuma a bayana_

Bayan ta rubuta ta rike biron tana ta tunanin yadda mafarkin ya zo mata, a kullum mutanen nan uku mafarkinsu take, sai dai ba zata iya siffanta su ba, domin bata iya shadar fuskokinsu balle kuma wani abun da zai saka ta iya cewa aljanuna ko mutane. A zahiri dai sun fi kama da aljannun domin shi mai busar sarewar kullum baya yake bata, tun tana jin busar a nesa har ta fara mafarkin tana tsinkayarsa ya bata baya, to shi kuma wanda ta bashi baya wanene? Wanda kuma yake gefenta wanene? Su ma duka aljanun ne ko kuma wani abun ne na dabam? Miyasa take yawan mafarkinsu? Miye alakarta da su?

“Fulani…..”

Kiran mahaifiyarta ne ya katse mata dogon tunanin da ta fara, da sauri ta mike tsaye ba dan tana son zuwa kiwon ba, gudun irin abubuwan da suke faruwa wani lokacin, mawuyacin abu ne ta fita ta dawo ba tare da wata saniya ta samu karaya ko kuma ta mutu ba, ko da yake idan ba tai kiwon ba mi za tai? domin a kullum cikin fargabar fita take a cikin jama’a saboda abubuwan da suke samunta ko kuma suke samun jama’ar da take kusanta, kusan ta zama annoba kowa a garin tsoronta yake gudunta yake idan ka cire iyayenta babu mai iya zama da ita ya wanye lafiya…….

Omar Abdallah Jari da na biyu a gurin Sarkin Yola wato Sarki Abdallah Jari da Hajiya Kilishi. Mutum ne mai yawan kyauta da nuna kauna da ga talakawa ga yawan murmushi da haba haba da jama’a.

Tsaye yake jikin window falonsa yana kallon yadda ruwan sama ke sauka harabar gidan yadda ya kurawa gurin ido sai ka rantse da Allah kirga ruwan yake, babu komai a zuciyarsa sai kewar triples dinsa, saboda suya baro gurin aikinsa sokoto ya zo garin iyeyensa kuma garin haihuwarsa Yola, amman yana fargabar tunkarar Masarautarsu saboda mahifiyarsa wato Hajiya Kilishi.

 

 

 

Hannu ya saka ya cire wayarsa da ke aljihu ya nemo number Nana ta aika mata kira, ringing biyu ta daga

. Dariya yai dariyar da ta bayyanar da fararen hakoransa ya sauke wayar. He wonder how mahaifiyarsa take da basira haka har ta tasan da dawowarsa. Baba Adamu ne ya fado masa a rai a take ya bar jikin tagar ya nufi dayan falon da Baba Adamu yake. Baba Adamu na ganinsa yai saurin mikewa tsaye irin na girmamawa, har sai da Omar ya zauna sannan shi ma ya zauna a kasa.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button