Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 157

Sponsored links

yana maimaita kansa to na aiwatar. Cikin damuwa na sanar masa ni bana son al’amuran nan nasa. Yay murmushi idanunsa a kaina. Kafin ya kira sunana da fadin, (Baka isa canja abinda ALLAH ya rubuta ba daga kaddararka, tabbas al’amarin dake zagaye damu baiwace da ga ALLAH, sai dai wasunmu na kaucewa wajen tafiyar da ita har su hada da shirka ko saka wasu a shirka. Why why Ban taba aikata shirka da wannan baiwar tawa ba, sai dai ina bada maganin da ALLAH ya sanar dani akan duk wani shaidani da cututtuka. Kai jinina ne, a kuma dade da tabbatar da abinda yake tare da ni kaima yana a tare da kai, sai dai bazan tilastaka yin abinda ni nayi ba, zan dai rokeka tsayawa a bayan yarinyar nan da izinin UBANGIJIN har ranar da makiyanta zasuyi kuka. In ba hakaba ba iya ita ba, kasar ruman gaba dayanta na cikin garari inhar waccan mushirikar ta samu cikar burinta a kanku. Domin burinta shine mulkar kasar ruman ne, ta taka wasu tsanikan nasararta kuma a dalilin son zuciyar wasu dake cikin masarautar da karancin toro da dogaro ga ALLAH. ALLAH ne ya daura maka wannan nauyin bani ba, dan haka jeka, jeka maza da iznininsa ka magance matsalar). Wanna wasiyyar ta mahaifina sune sanadin komai, sune suka cigaba da jagorantata har zuwa yau. Fhareedatu ta tashi yarinya mai shiga rai, kyakykyawar gaske da akoda yaushe mukanta mamakin wama ta biyo a kammani, dan duk da tana kama da yan uwanta idan ka nutsu zaka fahimci kamanin nata sunada sirrika masu yawa kuma duk ta fisu kyawu. Kamar yanda mahaifina ya fada nakanyi mafarki akan abubuwa da yawa da suka shafeta, wani lokacinma akan min abu kamar wanda aka budema idanu, duk yanda nake gudun bada magani ko taimako akan masu hatsabiban iskoki wani lokacin saina tsinta kaina nayi, amma dai ina iya bakin kokarina na ganin na kaucema hakan. Dan da gaske abubuwa da yawa basa kwanta min a rai, duk da Alhamdullah ni dai wani aljani bai taba sakani yin yanka na zubda jini ba ko shardantamin wasu abubuwa. Kawai nakan samu kaina da yin abunne.Komai ya fara fitowa ga Fhareedatu a lokacin data fara mafarkai akan abubuwa, duk mafarkin da tayi nima sai nayisa cikin amincewar UBANGIJI. A lokacin na fahimci komai yana tunkarowa kenan, ban fahimci kalaman baba ba na sai muni hakuri mun rasa kafin ta samu sai lokacin da Arfa ta rasa ranta, aka kuma na Fariha itama. A jiyyar da Fhareedah tayi na kusan wata bakwai kamar wadda ta fita a hayyacinta ne na fahimci komai da ga wasiyyar mahaifina, da ga lokacin ne kuma abubuwa suka fara daki-daki har zuwa yau. Hatta bibiyarmu da suka saka anayi na barsune kawai, hatta kubutar damu da akayi da ga shirinsu nasan wanda yayi. Duk kanin kalubalen da Fhareedah ke fuskanta a gidan nan nasani duk. Sai dai abinda masu hakilon basu sani ba tana zagaye ne da kariyar UBANGIJI, ya saka wasu halittu gadinta domin masu talala da ita da ruguza ayyukansu badan ta banbanta da sauran mutane ba ko zama ta daban. Kawai dai UBANGIJI idan yaso karya azzalumi sai yay masa talala da abinda ya raina. To hakance akan Fhareedah da mushirikar bokanya da ma duk mabiyanta dan sun san kansu”.

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button