Hausa Novels and Stories

Tabarma Kashi 3

Sponsored links

Cikin madaidaicin falon matsakaicin gidan,wanda bai cika da wani kayan ado da qawa na rayuwa ba,saidai tsananin tsaftar data bayyana kanta jikin kowanne loko da saqo na gidan zai matuqar burgeka tare da daukar hankalinka,har kayi sha’awar matsakaicin gidan.

Kyakkyawar macace fara sol,irin farin da zai iya daukan hankalinka,tare da alamta maka cewa lallai mutum yana da nasaba da wani yare cikin yarukan nigeria zuwa afrikaans da kowa yasan fatar duk wani dan yarensu farace,koda akwai baqaqe suna wahala qwarai. Duka duka shekarun haihuwarta a ido ba zasu haura ashirin ba.

 

A gurguje take sakawa yaron dake tsaye a gabanta uniform dinsa,tana gyara masa kwalar rigar uniform din,lokaci guda kuma tana jijjiga yarinyar dake goye a bayanta daketa faman tsala kuka kamar wadda ake yankar naman jikinta.

Kana kallonta zakasan a rude take,uwa uba kuma alamu sun nuna sauri takeyi sosai,fadi takeyi cikin yanayin damuwar dake shinfide akan fuskarta

“Yi shuru……yi haquri yanzu zamu wuce kyasha iska a hanya” ta fada fana durqusawa tana qoqarin sanyawa kyakkyawan yaron da sumarsa mai yawa da santsi ke sake kwantowa gaban goshinsa saboda duqawar da yayi zai karba safar da take qoqarin saka masa

“Zansa da kaina ummee”

“Bari na dauko maka lunch box dinka da hijabina saimu wuce,kaima ka kusa makara yau” tayi maganar tana miqewa,dai dai lokacin da aka bankada labulen falon aka shigo.

A nutse ta daga kai ta kalli matar,wadda zasuyi kusan sa’anni da ita,idanma ta girme mata duka duka baifi ta bata shekara daya ba. Ita dinma ita ta kalla suka hada ido,saita dauke kai tana yatsine fuska,ta kuma tattara dukka bacin ran duniya ta azawa fuskarta,ba tare data ko kalli sassan da matar gidan take ba,ta wuce kanta tsaye zuwa kitchen din gidan.

Wani abune yazo ya tsaye mata a wuya,duk da cewa idan da sabo yaci ace ta saba da mummunar hali da dabi’ar ta,amma akance,duk mutumin da yasan daraja da martabar kansa baya iya jurewa cin xarafi daga wajen ko waye,tana da dukka hanyoyin da zata cusguna mata ta hanata jin dadin zaman tarensu,to amma wannan ba shine muradinta ba a halin yanzu,don haka tayi qoqarin share wannan daga ranta,ta wuce kitchen din tana dan bubbuga goyon nata data samu ta lafa da kuka zuwa yanzu.

Tsaiwa tayi turus tana dubanta cikin kitchen din,lunch box din yaron da tazo dauka tuni ta budeshi,ta kuma zazzage duka soyayyen chips da indomie din data dafawa yaron,wanda su kenan sukayi saura cikin gidan nasu,sai yau da take sanya ran samun albashi take tunanin ta biya kasuwa ta taho masa dasu.

Ba yau ne karon farko data fara yi mata irin hakan ba,saidai na yau din yafi na ko yaushe bata mata rai da quntata matuqa,idan a baya tanayin hakan ta qyaleta ta debo wani ta dafa masa,yanzun basu da sauran abinda zata dafa masan,don haka cikin muryarta data cika da bacin rai tac

“Wanne irin abune haka?,bakisan abincin waye bane da kika juye kina ci?” Cikin gadara ta waiwayo,ta watsa mata wani banzan kallo da ya sake tunzurata matuqa

“Ko abincin me gidan ne ina da right din naci qarewa ma kenan,tunda dai yaya na ne ya kawo,guminsa ne,saboda haka banga wanda ya isa ya dinga yimin shamaki ba” wani mummunan bacin rai ya yunquro mata,taji ya tsaye mata a wuya,kamar ma da qyar take zuqar numfashi,har batasan sanda ta isa gareta ba ta tankwabe plate din abincin ya warwatse a qasa ba. Itama abun yazo mata a bazata,don bata taba tanka mata ba,duk da ire iren wadan nan abubuwan da take mata masu yawan gaske.

Da yatsa ta nunata tana kafeta da idanunta da suka canza launi

Wannan abincin dama saurana binciccikan da kike zuba rashin mutunci da rashin tarbiyya a kansu to ba yayan naki bane ya kawosu ba,gumi na ne ke dashi duka kuke ci,kuma daga rana irin ta yau kinci iya rabonki kenan,duk ranar da kika qara saka hannu kika taba min wani abu dana ajiiye cikin kitchen dina,bama kitchen dina ba gidana ma gaba daya sai nayi maganinki naga uban daya tsaya miki” tuni ta miqe tsaye,gabanta yana faduwa saboda ta tsorata da yadda ta ganta,ta jima tana burin wannan ranar dama

“Ni kika zaga?” A fusace ta daga kai daga kwashe lunch box din yaron ta dubeta

“Muddin wannan shine zagi to na zagekin,kiyi duk abinda kika iya”

“Wallahi wallahi sai na sakaki kinyi nadamar wannan abun da kikayimin,zakiga iya matsiyina a wajen dan uwana”

“Na nawa kuma?,annamimiya?,wadda ta sanadinta na rasa duk wani walwala jin dadi da fahimtar junan dake tsakanina da mijina kuma me yayi saura?,ai ba abinda ya rage sai abu daya……”

“Wannan abu dayan shi zan ida” ta fada idanunta carr a tsaye cikin nata. Haka kawai ta samu kanta da faduwar gaban fitar lafazin daga bakin FAUZIYYA,amma saita gyada kai

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button