Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 56

Sponsored links

Cikin zumuɗin son jin yaya haɗuwar Shahan-shan da Zawjata-almilk ta kasance a jiya Malikat Bushirat tai shirin ziyartar sashen Malikat Haseena a yau. A ƴan rakkiyarta har da Jasrah dake son sake duba jikin Iffah. Tuni ƴan leƙen asirin cikin hadimai sun kwasa zuwa sassan iyayen gijinsu kuwa. Dan wannan ya zama kamar al’ada a masarautar kowane ɗan leƙen asiri kan kai wa uwargijiyarsa ko uban gidansa duk wani motsin wani babba a daular. Ta wannan hanyar ne a mafi yawan lokuta abubuwa ke yaɗuwa kunnen duk wani mai faɗa aji na gidan musamman abinda ya kasance na sirri.

 

Malikat Bushirat ta samu tarba ta girmamawa ga surukar tasu a fadarta. Tuni hadimai sun cika gabansu da kayan motsa baki. Kasancewar ganawar ta shafi wani yanki na ɓoyayyen sirrinsu duk wani hadimi aka sallamesa. Katafaren falon ya kasance daga Malikat Haseena sai Malikat Bushirat da Jasrah sai Daneen Ammarah. Tattaunawar ta jasu tsahon lokaci kafin Malikat Haseena ta aika amintacciyar hadimarta Banou kiran Iffah….

 

 

 

★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faɗuwar gaba da sanyin gaɓɓai sakamakon mummunan mafarkin da tai akan su Babiy a barcin zuhur daya figeta bata san mi ake ba saboda bata fita ko’inaba yau iyakarta ɗakinta. Yanzu hakama da aka idar da sallar la’asar tana tsumayen Daneen Ammarah ne kamar yanda ta saba, dan duk yinin yau ma basu haɗu ba tun bayan idar da sallar asuba dai data fita ta gaishesu kamar yanda ta saba ita da Malikat Haseena. Hadimai dai sun kawo abinci tare da saƙon gaisuwa daga Daneen Ammarah ɗin ɗazun da rana akan cewar tana nan tafe. Malikat Haseenah ma kullum da kanta takan zo ta duba ta, kasancewarta tsohuwa mai dattako da iya zama da mutane tuni ta shige zuciyar Iffah itama, dan duk da bata da sakewa da yawan fara’a har dan jan Iffah take da hira. Sallayar datai sallar ta linke har yanzu jikinta a sanyaye ga damuwa fal ranta akan iyayenta, acan ƙasan zuciyarta takeji akwai wani mummunan abu dake sake tunkarota koma ya riga ya iso garetan ta hanyar iyayenta batare data sani ba. Yanayin ɗan zafi da ake ya sata yaye mayafin abayan data naɗe kanta da shi ta ajiye, ɗaurarren dogon baƙin gashinta dake reto a tsakkiya ya bayyana. Abincin da aka shirya mata tun ɗazun da bata ci ba ta nufa, ta bubbuɗe taga komai, batama jin cin komai har yanzun, dan haka ta tsiyayyi madara kawai da shanta tamkar al’adar ƴan ƙasar ne. Tana buƙatar fara canja kayanta zuwa marasa nauyi, dan haka ta ajiye kofin madarar a bedside drawer. Toilet ta fara shiga ta fito sannan ta shirya cikin wata yar yololuwar rigar mara nauyi mai zubin shimi. Iyakar rigar gwiwar ta ne, gata kalar fari da adon jajayen firanni. Ta matuƙar haskata da fidda ƙuruciyarta tamkar ƴar budurwar balarabiya. Turarrukan da Daneen Ammarah ta tule mata ta zaɓa kusan kala uku ta fesama jikinta. Cikin nutsatstsen takunta ta dawo saman gadon tana mai kallon fatar hanunta dake jajir saboda saɓar da tayi. “ALLAH dai ya isana wlhy” ta faɗa cike da halin tsiwarta tana jan bargo ta rufa iya cinyoyinta bayan ta jingina jikinta da fuskar gadon. Littafin da take rubuce-rubucenta na duk abinda ya faru ta ɗauka ta buɗe ko zata ji sassaucin tunane-tunen da zuciyarta ke mata marasa daɗi akan iyayenta, dan sam mafarkin nan yaƙi barin ranta koda na sakan ɗaya… A zahiri rubutun tai shirin fawara, dan yanda ta tsurama littafin ido da riƙe biron da nutsuwa matuƙa zai saka ka hasashen haka. Sai dai sam ko kalma biyu ta kasa rubutawa tamkar ma an mata wankin ƙwaƙwalwa komai ya gudu, hasalima nisan da tai a tunani yasa bibbiyu take ganin rubutun baya da tayi….

Knoking ƙofar da akai ya sata jan numfashi ta fesar, sai kuma taja mayafin dake gefenta ta yane jikinta har saman kanta tare da amsawa da “Yes! Kowaye ya shigo”.

A ɗarare hadima banou ta shigo, tsananin tsoron Iffah shimfiɗe akan fuskarta ya kasa boyuwa. Daga bakin ƙofar ta zube muryarta na ɗan rawa kamar yanda jikinta ke tsuma. “Amincin ALLAH da lafiya su tabbata ga Zawjata-almilk”.

Harara Iffah dake kallonta ta zabga mata. “Ina tare da masu lashe kurwar mutane irinku lafiyar zata tabbata a gareni? mtsoww!! Malama faɗi abinda ya kawoki bana son gulma”.

Ƙasa Banou ta sakeyi da kanta muryarta na rawa, dan harga ALLAH tana shakkar wannan yarinya da ko magana gatsau take yinta babu alamar shakku tattare da ita. “Uhm uhm dama Malikat ce take buƙatar ganinki”.

Hannu kawai Iffah ta ɗaga mata, dan har cikin rai ta tsani matar nan matuka. Sai da ta miƙe zata buɗe ƙofa sannan tai magana a gadarance. “Ki jirani a ƙofa, saura kuma kafin na fito ki lashe mun hadimai azzalumar bamza”.

Da rawar jiki data harshe Banou tace, “Hakan bazata faru ba ranki ya daɗe”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button